← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 103

Sashe 72

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kaina sai da na yi dariya kafin na ce" Kar ka jawo mini ta shigo da shirinta sabo da ni."
"Haba. Ai Rabi'atu ba ruwanta."

"Uhm"

Na faɗa a ƙasan makoshi to wai ba ruwanta Yallaɓai da neman suna.

"Tana ce mini Yallaɓai na ce ta bari kada ki ji ta. Ko a ma'aikatana ba mai kirana da Yallaɓai sai dai Oga ko Injiniya saboda ba na jin daɗin sunan a bakin kowa sai a bakin ki."

"Ai sai na bar mata sunan. Ita ce amarya mu ai mun tsufa."

Na faɗa ina kallon shi hAr na fara tausayin Gimbiya. Domin rawan ƙafan da Yallaɓai zai yi a kan yarinyaa nan, sai ya ce bai yi komai a lokacin auran ta ba.

"Ta ce tana som sunan sai dai ku riƙa kirana ke da ita."

"A'a ni fa na bar mata sunan. Ai na É—ana ina laifi mun sha miya ita kuma yanzu take."

Yana wata dariya nishaÉ—i kafin ya ce" To ni kuma sai na koma wani suna a wajen ka?

"Ah sunan ka mana."

"Yusuf gatsal?

Ya faÉ—a yana waro mini ido sai na gyaÉ—a masa kai ina yar dariya.

"Tab. Ban yadda ba, sannan ban amince da wannan maganar ba. Sai ita ta sauya amma ni ba zan sauka daga kam mikamina ba "

Ni dai sai bin Yallaɓai nake yi da kallo ina jin abin a zuciyata. Yallaɓai na zaunar da ni yana ba ni labarin wata macen cikin jin daɗi da annushuwa.
Da bakin shi yake faÉ—a mini yau na sun fita ne, ya je makaranta ya É—auke ta sun je shooping daga nan suka biya restaurant suka ci abinci anan ne ya ci wani ferfesun kifi ya lalatamai ciki kwana ya yi yana gudawa. Sai da asuba na bashi sauran flajin É—in da nake da shi ya samu ya sha guduwan ya tsaya amma har da ciwon ciki shi ya sa da safen bayan ya yi wanka ya fita ya ce zai fara tsaya ta asibiti a ba shi magani. Sannan ya biya makaranta su Baby kafin ya wuce office tun da ya ce mata zai shigo makarantan na su yau.

Har ya fita ya bar ni, ina cikin mamakin manganganunsa jiya, shi kenan kuma tun da ya faɗa mini sai ya samu kofa in dai yana gidana sai ya kawo sanadin da zai yi labarin Rabi'atu. Aikin sa kenan tana gaishe ni na ce ina amsawa, ban san yadda suka kare da ƴan uwan shi ba amma ni dai kawai ya ce mini ya yi magana da Nene, na san da man ba za ta hana shi ba shi ya sa ban matsa sai na ji amsarta ba. Ni dai ban yi taɗin da kowa ba ko su Munnira saboda na kasa iya sarrafa harshe wajen ba da labarin wai Yallaɓai zai ƙara auro zai auro yar yarinya ɗanya shakaf, mu kuma da man tafiya ta tafi jiya ba yau ba. Ko naƙi ko na so ba zan koma kamar Sadiya a jiya ba. Sai dai na koma Sadiya a yau har shekara arba'in da wani abu a duniya. Duk gyare-gyare na ban isa na koma kamar budurwa ko yarinya ba. Dole dai wajen ya saki tun da jiya ba yau ba ne. Itama Gimbiyar ni da ita duk samkal ne,  tun da tsere yan mu a shekaru ba nisa sosai itama ai ta kama gidan arba'in. Tun da yana da kuɗi zai buƙaci canji yanayi.

Duk ƙoƙarina na kar ƙarim auran Yallaɓai ya dame ni na kasa. Abin ya tsaya mini a zuciya amma ina ƙoƙarin yakicewa saboda na zauna lafiya. Yallaɓai da bakinsa ya faɗa mini Kawu zai zo za su je su gabatar da kansu wajen baban Rabi'atu. Kuma ya zo sun je ɗin ya dawo yana faɗa mini ya yi musu karamcin amma ya ce su je zai neme su da kan shi. Yallaɓai rawan ƙafa kawai yake yi bai ƙi a ce gobe ma an ɗaura auran nan ba gyaran gida kam tuni ya tsaya bangaren da Rabi'atu za ta fara tarewa ma'aikata suka raja'a duk da namun ma fenti ne ya rage sai tayels da za a sanya amma ita bangarenta har tayels ɗin an saka kaɗan yarage a ƙarisa. Da bakinsa yake sanar da ni in ma an gama da wuri ba zai bari a saka lokacin bikin ya kai wattani uku ba.

  Duk wannan bidirin da yake yi ban sam bai sanar da Gimbiya maganar da wuri ba. Na ɗauka yadda ya faɗa mini itama ya same ta sun yi magana ashe bai sanar da ita da wuri ba, ni kuma gani na yi ba hurumina ba ne shi ya sa ban yi azaɓarɓaɓin bakin kiranta in faɗa mata tun da ba ni ba ce mijinta.
Kawai sai wayarta na samu kwana biyu tsakani da zuwan su Yallaɓai gaban Baban Rabi'atu.

"Maman Jidda kin manafunce ni."

Haka ta fara ce mini da na É—auki wayarta da sallama.

"Ikon Allah. Munafuncin mene kuma?

Wataƙila kuka take yi domin tana ta jan hanci.

"Ba ki faɗa mini Daddy aure zai ƙara ba. Sai da kowa ya gama jin magana sannan ya faɗa mini."

"Ai ba hurumina ba ne na sanar da ke. Shi ya sa ma kika ji ban yi miki maganar ba."

Na amsa mata, gaskiya na faÉ—a mata ba bangarena ba ne.

"Amma ai mun yi magana da ke na ce ki bincika a bangarenki nima haka. Abin da muka sani mu faÉ—a ma juna me ya sa kika boye mini? Ahalin da bakin shi ya faÉ—a mini ke ya fara yi ma maganar kafin ma ya sanar da Nene?

Sai na saki baki kawai kamar tana ganina saboda na ga kamar tana neman ta É—ora mini jakar tsaba ne.

"Nima bai sanar da ni ba sai da na ga kiranta sannan na tambaye shi wace ce ya faɗa mini. Ki yi haƙuri in rashin faɗa mikin da ban yi ba ya yi miki ciwo. Na ga ba hurumina ba ne sanar dake shi ya sa"

"Wallahi Daddy bai isa ya auro wannan yarinyar ba.  Anty Bahijja ta faɗa mini yarinya ce ƙarama kamar sa'ar Jidda shi ko kunya bai ji ba? Da me muka rage shi?

"Ta É—an girme ma Jidda gaskiya."

Cikin mamaki a muryanta ta ce" Kin santa ne?
"A'a ya dai nuna mini hoton ta na ganta. Kuma ya faÉ—a mini shekarunta."

Sai kawri Gimbiya ta yi wani jan numfashi kafin ta ce" Da man yana ta cika baki da cewa
Ko a lokacin aurena ba ki bashi matsala ba wannan ma yana fsÉ—i da fahari ba za ki bashi matsala ba. "
"To matsalan me? Ai ko na yi kishi da hauka ba shi zai saka ya fasa ba. Sai ma ni na zubar da ƙimata. Kema ina mai baki shawara ki yi haƙuri duk da akwai zafi amma in ka daure sai komai ya zo ya wuce."

"Tab. Wallahi ni ba zan yi munafunci saboda namiji ya so ni ba. Matsala kuma a wajena yanzu ya fara gani."

Kafim na na yi magana ta katse kiranta sai na bi wayar da kallo kafin na furta" Ikon Allah!
In na fahinceta ni ce mai yin munafuncin saboda Yallaɓai ya so ni, sai da na yi mirmishi Gimbiya kenan, ni fa ba zan yi tashin hankali da faɗa saboda Yallaɓai zai ƙara aure ba, yadda ban yi a baya ba yanzu ma ba mai sskani na saka kaina a cikin damuwa. Na san ba zai fasa ba kuma a yadda Yallaɓai ke ji da yarinyar nan wallahi Gimbiya ta ce za ta bashi matsala to shi zai iya nesa da ita saboda ya samu masalahan na shi muradin. Tana tunanin ina yin haka ne saboda ya yabe ni, ba ta sanni ba ne ni fa ban yarda na zubarma da kaina ƙima saboda namiji ba, a je dai a dawo suna ne zai yi tambari na bar ma kaina da ƴaƴana abin kunya daga ƙarshe ya yi auran shi to wa gari ya waya? Shi ya sa na koma ga Allah ina faɗa masa damuwa da fatan ya cire mini damuwa da tunanin ƙarim auren da Yallaɓai zai yi. Kuma Alhamdulillah na fara ganin canji.

Yadda ko ƴan uwana ban yi zencen da kowa ba. Haka ƴaƴana kamar yadda ya sanar da su na auran Gimbiya wannan ma ya sanar da su da bakin shi. Jidda jarabawa ma suke yi jibi za su gama za ta dawo gida Baby kuma sun fara Jsce ta gama ajin ukun ƙaramar sakandiri. Duk ta buɗe tantanin budurci ya bayyanar mata. Wancan watan ta fara jinin al'ada gashi ta fi Jidda manyan gabbaina tun ba ta yi wani shekaru nanna sun cika mata ƙirji. Hankalina na mai da kan kula da tarbiyan yayana. Yallaɓai yanzu ba ma gaban shi hankalin shi da duka tunanin shi na kan yadda zai mallaki Rabi'atu ne shi ya sa nake yi masa uzuri.

Ni ko da muka yi magana da Gimbiya ban yi ma ko Yallaɓai zencen ba, nima bai nuna mini a yanayin da suke ciki ba. Shi ya sa nima ban tusa kaina a cikin abin da ba ruwana. Jidda ta gama jarabawa ta dawo gida sai gidan ya yi daɗi na rage kaɗaici, har Yumna yanzu ta fi karsasshin wasa da dawowar Jidda har uban gayyar ma ya yi murna da dawowarta yana faɗa mata gidan ba daɗi da ba ta nan. Ban san me ya faru ba kawai na ga Yallaɓai ya kwaso mini su Khalipa da Anwar, na tamnaye shi lafiya? Ya ce ba komai. Ina maman su? Ya ce mini ta je Rano ta dawo. Ni kuma har ga Allah ban kawo ma kaina tunanin matssla suka samu da zuciya ɗaya na karɓi yaram gidan sai ya zama active saboda ɗan hayaniyarsu  in sun tafi makaranta Jidda da Baby suna gida, in sun dawo gidan ya sake rikicewa da wasannin su tun ballanta Yunma da Yallaɓai ya gama ɓata ta da mugun wasa.
Chapter 72 · 0% Book details