← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 103

Sashe 63

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki na buÉ—e ina kallon Alhajinmu. Duk da na san halin shi amma ban tsammaci zai iya cewa wai ban kyauta ba? Me na yi na rashin kyautawar?

"Na san a cikin zuciyarki kina ta tamtaman me kika yi na rashin kyautawa ko? Duk buɗe kunnuwanki da kyau Dubu. Kin yi rashin kyautawa da yawa a cikin duka abin da ya faru. Kuma hukuncin da Yusuf ya so yankewa yana kan daidai ne shima. Tun da ba a gaban shi komai ya faru ba shima faɗa masa aka yi, kuma da bakin ki kika ce daga can gidan abokiyar zaman taki an faɗa masa ƙarya da gaskiya. To ke me ya sa da ya zo gare ki, ba ki zaunar da shi kin faɗa masa gaskiyan abin da ya faru ba?

"Alhajinmu bai ba ni da mar haka ba faÉ—a kawai yake yi ta in da yake shiga ba ta nan yake fita ba."

"Shi ne kuma yana faÉ—a kina fada. Har kika yi masa rashin É—aa da gatsen ko yanzu ya ce ki bar masa gida za ki ta fi ko? To menene abin kuka don ya yi miki abin da kika bukata Dubu?

Ai sai na kasa mgana na dukar da kaina kasa. In Alhajinmu ya saka a É—aki tun kana jin kana da gaskiya sai ka sare ka fahimci kai ne ba ka da gaskiya saboda irin kalaman da yake amfani da su wajen jawo hankalin mutum

"Ni da ke nan da Yusufa zai ƙara aure na kira ki, a wannan falon kika zauma kamar haka na yi miki nasiha? A cikin duka nasihin da na yi miki wata kalma na yi ta jadadda miki da in kika rike ta zaki rabauta?

"Haƙuri. Ka ce na je na yi ta hakuri wata rana ni ce zan zama mai riba."

"To ashe ba ki manta ba? To me ya sa yanzu kika kasa haƙurin kika kuma kasa rabauta da sakamakon masu hakuri?

Sai kawai na sake fashewa da kuka ina fadin" Alhajinmu na yi ta haƙru wallahi ba ka san hakurin da na ke yi ba ne. Ko wani abu ne suka yi mini da na tuna da nasiharka na ke ma yar da komai ba komai ba. Yau ma ɗin ya ƙure ni ne shi ya sa na tanka masa."
Na gama faÉ—a ina ta jan hanci saboda kuka.

"Du ka na ji kin yi haƙurin a baya amma abin da kika aikata yau duk ya kore wancan haƙurin na ki na baya "

Na ma kasa mgana na buɗe baki zan yi sai na ma yar na rufe. Ni fa na manta ne in dai Alhajinmu ne ba zai taɓa bani goyon baya ba da gaskiyan Gwaggo Alhajinmu na ganin ƙimar Yallaɓai a duk cikin surukansa ya sha faɗa ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba.

"Kina maganar ke ma da kika haihu ba ta zo ba kaza da kaza ina ruwan ki da wannan? Ke dai ba ki yi don Allah ba ai bai kamata,ki duba ita abin da ta yi miki ba. Ke kin yi mata domin Allah da zaman tare. Ruwanta ne ta ma yar miki da martanin Alheri ko sharri. Ke dai Ubangiji ya yi amfani da zuciyarki kuma ladan ki na wajen Allah. Ba hujja ba ce mijinki ya ba ki umarnin ki je asibiti ki dubata ki yi zaman ki, ki ƙi zuwa kin ga kenan kin saba umarninsa kuma mala'iku sun yi fushi dake matuƙar ba ki nemi gafaran shi ba. Sannan kuma abin da ya faru yau sanadin ki ne, ko da ruwan zam zam ba za ki iya wamke kanki ba tun da kin je wajen sannan waɗanda ke tare da ke ne suka yi hatsiyani ni da ke mun san ke ba ki saka su ba amma ba za mu ƙi gaskiyan cewa a sanadinki suka yi komai."

"Wallahi ni Alhajinmu ban ce kowa ya yi faÉ—a saboda ni ba."

Na fada ina ƙara rantse masa da Allah.

"Na ce miki ni da ke mun san ba ki saka su ba. Amma shi da sauran mutane in suka ji labarin za su yarda ba bakin ki a ciki! Ki yi tunani ki gani. A wannan gabar Yusufa ba shi da laifi abin da ya ji da shi zai yi amfani."

Ina sharan ƙwallah na ce" Amma me ya sa ba zai yi bincike ba sai ya rufe ni da faɗa har yana ce mini ina da mugun nufi a raina?

Dariya na ga Alhajinmu ya yi kafin ya ce" Dubu ke kika jawo duk zargin da ya yi miki. Me ya sa kika bashi kofar ya fahimci kamar kina jin haushi da haihuwar da aka yi mass? Ki tuna  shi ma fa ɗan adam ne yana da zuciya kamar yadda kike da ita. Sheɗan ne ya kawata masa a zuciyarsa amma ina da tabbacin ba haka yake nufi da gaske ba. Ai in da kima da mugun nufi akan matarsa da tun a farkon auran shi zai fahinci haka."
Ni sai na ga kamar kawai ina zaune Alhajinmu na ta faman boye laifukan Yallaɓai yana bayyana nawa.

"Har fa ce mini ya yi wai ina kishi da tana haihuwan Maza ni kuma Allah bai ba ni ba "

Na faÉ—a hawaye na kece mini saboda takaicin kalamansa.

"Haka zai yi tunani haka ma kowa zai yi tunani. Haihuwa kuma na Ubangiji ne daman Allah ya faɗa mana wasu zai ba su maza da mata, wasu mata kaɗai wasu mazan kaɗai wasu ma har su koma ga Allah ba zai ba su haihuwan ba ki godema Allah kina cikin zabaɓɓun Ubangiji. Maganar ita tana yin farar haihuwa ki bar ta da tunaninta, tun da ai shi mijin na ku bai ce ba ya son matan ba duka yana so kuma duka ƴaƴan shi ne. Sai ki roƙi Ubangiji ya baki mai albarka daga Mazan ko daga matan."

Kawai sai na cigaba da sharan ƙwalla domin ni dai Alhajinmu ya gama ƙure duka mganganuna.

"Ki yi haƙuri ki daina kuka ba wai ina goyon bayan shi ba ne a'a ina faɗa miki gaskiya ne a matsayina na adalin Uba. Ba wai don kina ƴ'ata na goyo bayan ki ba, a'a ni ke da shi duka ƴaƴana ne zan yi miki adalci kamar yadda zan yi masa. Ki daina kuka ya isa haka nan ba wani abu ba ne. Kawai sheɗan ne ya shiga tsakani ganin kun kasa samun fahimtar juna."

"Alhajinmu ta ya ya zai fahimce ni?

"Ta hanyar amfani  da kalamai na kwantar da hankali kar ki ɗaga sautin ki sama da na shi, na tabbata da kin yi haka da kun fahimci juna.'

"Uhm"

Na sha numfashi saboda na fahimci Alhajinmu ba zai gane karatun kurma ba.

Murmishi ya yi ganin na yi shuru yana kaÉ—a kai ya ce" Kukan ya isa kin ji share hawayen ki."
Ban yi musu ba share hawayena.
"Yau kike so ki koma gidanki ko sai gobe da safe?
Na kalli Alhajinmu baki buÉ—e kafin na ce" To kore ni fa ya yi me ya sa zan koma?

"Ashe ba yanzu na gama yi miki nasiha na ganar da ke kuskuran ki ba? To za ki koma gidan auran ki in sha Allahu. Shima ai na san yana can cikin damuwa in bai zo a daran nan zai da safe ina da tabbacin haka"

Kallon Alhajimmu na ke yi na kasa mgana yadda kawai yake da confident a kan Yallaɓai ke ba ni mamaki. Don ba warware masa komai ba! Ai wallahi da ya san wani abu da tuni zai daina wani cika baki a kan shi.

"Har gobe ina ganin sa da ƙima. Tun bayan shekaru ashirin da doriya na ba shi amanarki dai dai da rana ɗaya bai taɓa kawo mini ƙaran ki ba. Ko da yaushe ya zo gaisheni godiya yake yi mini yana yaba miki. Duk da na san kina saɓa masa shina haka amma bai taba fada mini saɓanin alherin ki ba. Ya zauna dake cikin daɗi da rashin sa. Kema ai ba ki taba kawo mini ƙaran sa ba sai yau. To na yau ɗin ma duk kishi ne shi ya sa ban ɗauke sa wani abu mai girma ba. Ki koma gidanki ki daidaita da mijinki domin yana yi miki kara ba domin komai sai domin yana son ki. Ki je ki ba shi haƙuri ki kara haƙuri  Mai hakuri in ya yi ta shan haƙuri ba ya kiɓa lokaci ɗaya amma watan wata rana zai zama giwa in har ya koshi da hakuri"

"Ki yi hakurin kin ji ko?
Ki koma ki cigaba da Biyayya aure. Domin Aljannarki tana a karƙashin diga digin mijin ki ne Dubu. In kin yi masa biyayya ki rabauta. In kin saɓa masa ki taɓe. Ni ba ruwana na riga na sauke haƙƙin Ubangiji na in kin bauɗe na faɗa miki gaskiya."

Na yi shuru ban yi magana ba kaina na ƙasa amma na daina kuka.

"Kin ji ko?

Ya sake faɗa yana kallona sai na gyaɗakaina kafin na ce" In sha Allahu Alhajinmu na gode Allah ya ƙara girma."
Ya amsa da Amin kafin ya cigaba da faɗin" Da dake da Rahila ne na ke yawan kafa misali da ku. Na kan ce tun da na aurar da ku ba ku taɓa tada mini hankali da korafin mzajen ku ba. Sannan suma ba su taɓa kawo mini maganar sharrin ku ba sai alheri. Amma sai ga shi a wancan satin nan in da kike zaune Muntari ya zauna yana karanta mini wani abu daga cikin na ƙuntata da Rahila ta ke yi masa ya kasa haƙuri ya kasa tanƙwasata sai da ya karya kaurin nan ya zo gabana yana faɗa mini na kira ta na yi mata faɗa. To kema ko sati ba a yi ga ki nan zaune kina kawo mini suka akan mijin ki, ke da Rahila kuna so ku ba ma misalina kunya ne?

Da sauri na ce" Ba za mu ba ka kunya ba in sha Allahu Alhajinmu."
Chapter 63 · 0% Book details