← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 103

Sashe 43

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun fita gidana tara da wani abu ba a fara taron ba sai sha É—aya na safe. Har sarkin Rano ya zo da Tafidan Rano kanin mahaifin Gimbiya. Ta waya muke ganin komai live Adnan ke yi da wayarsa ya na turawa a group É—in gidan su. Irin su Musbahu suna ta hotuna suna É—orawa. Sun gayyaci yan jaridu da masu Video da hotuna. Muna gida amma kamar mu yi tsuntsuwa mu gan mu a wajen Baby sai tsallen murna take yi, su Ma'u da Rahila ne suka zo mini sai su Munnir. Hauwa ta ma dafa shinkafar jalop mai nama muka ci muka sha da lemu. Suma duka mazajensu na can wajen taron

Kafin a fara Yallaɓai ya turo min saƙo. Saƙon da na maimaita shi sama da sau goma saboda daɗin kalaman na shi.  saƙon da ya samu wajem zama na musamman a ƙasan zuciyata.

"Sadiya ta ki sani kome yau na zama Nene ce sila tun da ita ce ta haife ni. Amma ina so ki sani bayan ita ke ce mace ta farko da kika bani ƙwarin gwiwa. Na gode Sadiya ta. Adnan ya nuna min abin da kika yi mini. Ina rubuta miki wannan saƙon cike da godiya a bakina. Zuciyata cike da ƙaunarki. Hawayen farincikin kasancewarki matata sun tarun mini a ƙwarmin idanuwana."

Nima sai na ji taruwan ƙwalla kafin na fita daga shauƙin da na shiga wani saƙon na shi ya sake shigo mini.

"A yau a wannan rana mai muhimmaci nake so na faɗa miki ni ke ce abu mafi muhimmanci da na mallaka a rayuwata. Na gode Abar ƙaunata. Yusuf na ƙaunarki. Ki tuna haka Halimatussadiya."

Sai kawai na samu kaina da ƙwalla, har sai da na saka hannu na share Allah ya sa ni kaɗai ne a ciki daga ni sai Yumna. Ita na ja na rungume ni ina jin wani irin shauƙi na motsawa daga ƙasan zuciyata.

An fara taro cikin nasara bayan an nuno hoton Yallaɓai ya yanka igiyar nan da almaka shi, tare da addu'oi.  Sannan a ka shiga ciki da a ka ƙawata shi da kujeru da kanofi.
Manyan baki sun yi jawabai sosai na godiya da jinjina da burgewa. Kawu ya ba da labarin Yallaɓai. Tariq ya ƙara da irin gwagwarmayan da ya sha kafin ya kawo yau. Sannan ya yi amfani da haka wajen zaburar da matasa domin su nemi na kansu. Ya faɗi har tarin alherin da Yallaɓai ya cimma  a shekaru ashirin da wani abu . Mafi rinjayen ciki samar da matasa aiki daga karƙashinsa sannan da gina wannan ma'aikatan bayan ya fara da kama hayan ƙaramin shago sai gashi yau ya mallaki ƙaton waje da sunan mallakin shi. Ya Usman ya yi jawabi a matsayin babba Yaya.

"Yusuf ƙanina ne amma zan iya cewa ya fini jajircewa.  Ni gidan soja kawai na sani amma shi ya san gwagwamarya. Ya san zane ya san gine gine, ya san ya ɗau kankare akan sa. Sanadin shi matasa da dama sun samu aikin yi. Ciki har da ƙanin mu dake aiki a ƙarkashin sa. Abin da zan ce shi ne Yusuf is a good Exmples ga matansa mu. Ku tashi ku nema. Ku jajirce in kuka gwada kuka faɗi ku sake miƙewa ku cigaba da tafiya. Watan wata rana za mu iya samun kamar Yusuf ko ma waɗanda suka zarta shi da samun ɗaukaka sanadin jajircewarsa. Congratulations My Bro. Allah Ubangiji ya sa nan da shekaru goma duka arewa kowacce state kana da reshe Amin."

Sai tafi raf! Mu kan mu mun zagaye waya muna kallo kamar mu yi hawaye. Mimisco ce ta ɗora jawabin a status har mijinta ma ya je shima ya yi jawabi, daga ƙarshe ne Yallaɓai ya yi jawabinsa. Da farko ya yi sallama sannan ya yi salati ga Annabi(SAW) sannan ya gangaro wajen gode ma iyayen shi. Tare da addu'an Allah ya jiƙan Marigayi Muhammad Inuwa.

Mace ta farko bayan Nene ni ce wacce Yallaɓai ya gode mawa. Wallahi ina kallo ina hawaye ban sani ba su Munnira na ta minI sowa amma ni ina hawayen farinciki.

"Zan miƙa sakon godiyata zuwa ga Matata Uwargidana. Sadiya Sulaiman Yashe(Mrs Yusuf Muhamma Inuwa) bayan iyayena da ƴan uwana. Ita ce macen da ta yi gwagwamaryan rayuwa da ni cikin samu da rashi. Sadiya ta kasance wata mace mai hikima da baiwa. Wannan sunan kamfanin idea ɗin ta ne, duk da burina ne amma da shawaranta yau na kai ga gaci. Sunan da ke jikin wannan kamfanin ma nata ne. Ita ta samar da shi. HM TAFIDA ba mallakina ba ne ni kaɗai. Namu ne ni da ita da ƴaƴanmu. Ni zan kasance Md a idanuwanku amma asalin mai juya kujeran tana gida. Miss Sadiya Yusuf Muhammad ina miki jinjina ina kuma ta ya ki murna. Da girmamawa ina mai sanar dake MUN YI NASARA"

Ya faÉ—a sannan ya É—aga hannu sai ihu da tafi. Daga nan Vedio ya yanke tuni na É—auka na saka a status É—ina na ma kasa magana sai emojin kuka na saka. Munnira faÉ—i take yi" Wallahi gaskiya ya fada. Da bai ambace ki ba da ya yi butulci."
Ni dai ina ta sharan ƙwallar farinciki. Sauran jawabin na shi godiya ne ga amininsa guda biyu Tariq da kawu sai ƴan uwan shi gabaɗaya sannan ya jinjina ma Musabahu domin da jajircewan shi suka samu nasara. Daga ƙarshe ya yi godiya ga matasan da ke aiki a ƙarkashinsa domin ya ce ba domin su ba, da bai yi nasara a yau ba a ƙarshen ƙarshen dai ya kira sunanayen su Jidda da su Khalipa da Gimbiya ya gode musu a cewarsa suma suna cikin labarin nasarar shi a wannan ranar. Kafin taron ya tashi sai da matasan da yake aiki da su bangaren gine gine suka bashi award na takarda da gilashi sannan aka tashi taron za a ci abinci a raba gift shike nan taro ya tashi.

Ni Yallaɓai ya gama mini komai. Na maimaita kallon jawabin sa ban san iyaka ba. Ya Hamza sai da ya kira ni ina ɗauka ya ce" To Miss Sadiya yau ta sha godiya wajen Mr. Yusuf. Ya dai ce ke ce Md shi acting Md ne."
Sai kawai na hau dariya shima ya na taya ni.
Nan ya fara mini nasiha ya na fadin" Kin yi abu mai kyau ko Alhajinmu in ya ji zai ya ba miki kin tsaya ma mijinki. Da daÉ—i ba daÉ—i yau kun yi nasara. Congratulatons"

Saƙonni sai da suka yi mini yawa nima murna ake taya ni. Tabbas ni ma na samu nasara. Datti daga wajen taro gidana ya taho ya na ta sake ba ni labari. Shima ya taho da jakarsa na gift faɗi yake yi" Ya Sadiya Yallaɓai ya gama tashin kaina da jawabin sa. Danƙari."
Kowa sai ya ce abin ya burgeshi ba kamar wasu mazan butulu masu manta alheri ba. Ni kam Yallaɓai bai manta da ni ba ranar ba a  gidana yake ba amma da daddare bayan sun sallami baki sai da ya zo gidana lokacin duk an watse daga ni sai yara. Marwa ma tun dazu Kawu ya zo ya ɗauketa.

Baby ta yi barci Jidda ce ta ce sai ta jira Abban ta. Ai ko muna jin buɗe get ni da ita muka fita. Ni saboda zumuɗi da sauri a falo na baro Yunma. Sai ga ni, ni da Jidda muna rige rigen faɗa ma Yallaɓai. Ture Jidda ya yi yana faɗin" Jidda ya za ki ture mini mata kuma"
Tana dariyan farinciki ta ce" Congratulations Abba. You make us proud Today."
Sai ya sake ni ya rugumeta sannan ya É—ago ya dafa kafaÉ—unta yana faÉ—in.

"Thank you Fav Daughter."

Ni ko sai da na sumbaci gefe kumatunsa sannan na ce" Da ikon Allah ka fara hawa matakin nasara kenan."
"Amin My Sady."
Ya faÉ—a ya na mini mirmishi, ya shiga gidan amma ruwa kawai ya sha ya tafi bayan na ce gobe ni zan ba shi na wa gift É—in.

"Mai daÉ—i ko Sadiya ta?

"Sosai ma. Ya fi mazan ƙwaila."

"Ina godiya Hajiya ta."

Muka raka shi har haraba muna É—aga masa hannu.

Na cika alƙwari domin washe gari da ya dawo gidana ban nuna masa gajiyawa ta ba sosai na saki jiki muka yi ma ruwa tas. Ƙarshen shi ne kawai ba mu gani ba. Tabbas kwans biyun da ya yi a gidana na saka su a cikin tarihin rayuwar auran mu.
Ni ban sani ba ashe kalaman da Yallaɓai ya yi a kaina Gimbiya kishi ya kusa kashe ta a cewarta ita bai ambaceta ba sai daga ƙarshe. Nima Sameena ta kira ni tana mini tsegumi ta ce a group ɗin su na gida Gimbiyar ta yi maganar da aka turo jawabin ta ce ai ita saboda haushi ba ta ma gama saurara ba. Na yi dariya na ce to me ta ke tsammani? Ya ya yabe ta sama da ni? To ta jira tukunna da sauran lokaci.
Nima na samu gift É—in tun da ya yi saura kaf yan gidanmu sai da na ba su, na ba ma Hauwa da Munnira da Mubeena har Ya Auwal na ba ma Datti na shi ya kai mishi. Amina kuma ta kira ni a waya ta ce sai na ijiye mata mug É—in da Memo na ce an gama. Na É—aga akwatina na saka mata. Sauran kuma na ba ma su Jidda nima na ijiye ko domin tarihi.

Hankula sun kwanta. Tun da an yi taro lafiya an gama lafiya. Ni kan sai da na hi sati ina saka jawabin Yallaɓai a status ɗina, da hotuna kar ku ga laifina yaɓo na aka yi, dole na yi ta sakawa ina jin dadi. Na kuma san na tura ma Gimbiya haushi. Ya Auwal har sai da ya gaji ya ce sun gaji da gani har sun haddace. Na ce su cigaba da gani suna haddacewa sai an yi wata zan dai na sakawa. Kuma haka aka yi ko bai kai wata ba an kusa. Tuni aiki ya kamkama a sabon kamfani sai hamdala kuma kamar an buɗe a sa'a kwangololi suna ta zuwa saman tuberin Yallaɓai. Abin sai godiya kawai.
Chapter 43 · 0% Book details