← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 103

Sashe 62

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na faÉ—a cikin karyewan sauti kafin lokaci É—aya na fashe da kuka.
Gwaggo ta ce" Subhanallah ke da waye haka?
Alhajinmu kuma duk ya ruÉ—e faÉ—i yake yi.
"Maimuna kama ta ku shiga ciki. Ba lafiya"
Kamar haÉ—in baki sai ga nepa sun kawo wuta tsakar gidan ya yi haske É—au.

"Marwanatu."

Alhaji da Gwaggo suka haÉ—a baki wajem ambaton sunan ta.

"Na'am."

Ta amsa itama a sanyaye. Ai sai Alhajimmu ya kalli Gwaggo itama ta kalle shi Allah kaÉ—ai ya san mai suke sakawa a zuciyarsu amma in zan iya karantar fuskokin su, sun bayyana damuwa tare da mamakin ganin mu a tare a wannan daren.

"Dubu lafiya? Me ke faruwa ne? Me Marwanatu ke yi tare da ke?

"Alhaji ƙafafuwana sun fara rawa. Allah ya sa dai lafiya.'

Gwaggo ta faÉ—a cikin damuwa.

"Ina fa lafiya. Ba lafiya Maimuna "

Alhajinmu ya faÉ—a shima a muryansa har ta bayyana damuwa.
Muna tsaye ni da Marwa mun kasa mgana, gwara ita ba kuka take yi ba ni kuka na ke yi har yana ba da sauti.

"Shin ba ku faɗa mana abin da ke faruwa ko sai kun sarƙe mana Numfashi da zullumi?

Gwaggo ta faÉ—a tana É—an karisowa in da muke tsaye.

"Ke Sadiya bar kuka. Taho mu je abin da ke faruwa.'

Ta faɗa tana riko ni, ina jin ta taba ni sai na faɗa jikinta na ƙara fashewa da kuka ina faɗin" Gwaggo Yallaɓai ne ya ce wai na bar masa gidan sa"

"Innalillahi wa'inna ilaihirraju"un.

Gwaggo ta yi salati.

"La'ilahaillalahu."

Alhajinmu ya karɓa.

"Muhamadan rasulillahi."

Gwaggo ta ƙarishe cikin wani yanayi

"Da kika yi masa me zai kore ki da girman ki da kuma daren nan?

Gwaggo ta tambaya daga jin muryan ta za ka san hankalinta ya tashi.

"Ban yi masa komai Gwaggo a kan matar shi ne ya ke son ya wulaƙanta ni."
.

Na fada ina shessheƙa. Gwaggo ta na bubbuga bayana alamun lallashi ta ce"Kai jama'a. Me ya sa Yusuf zai haka? Da girmansa?
To ita Marwanatu ba  na gan ku tare a wannan daren?

"Suna ta zo. Gimbiya ce ta haihu yau suna suka taho daga Rano É—azu da rana"

Ina jin Gwaggo ta sauke numfashi kafin ta ce" To da sauƙi ai na ɗauka itama wata matsalar ce."

"Umma ce ta ce na taho mu tafi. Mun baro Baby da Yumna na ta kuka."

Marwa ta faÉ—a kafin Gwaggo ta yi magana Alhajinmu ya É—an murmusa yana so ya yi magana sai kuma ya yi shuru.

"Alhaji ya ka murmusa? Ka na ji surukin naka da É—azun nan ka gama yabon sa ya baka kunya ya koro maka y'a kusan shekaru ashirin da aure cikin dare."

"Ho Mata kenan ku dai ba a rabaku da son kai. Ni daman na san ai ta tsuniyar gizo ai ba ta wuce ta ƙoƙi ko?

"Ban ga ne ba Alhaji. Kuka fa Sadiya ke yi?

"Duk na ji. Kamata ku shiga ciki bari na je masallaci na dawo sai mu zauna mu yi magana. Allah ya rufa mana asiri.".

Ta amsa da amin ya fice ni kuma Gwaggo ta rike ni zuwa falon Alhaji Marwa ta bi bayan mu. Zama muka yi a saman kujera mai zaman mutum biyu ni da Gwaggo.

"Wai shi Yusuf din ya ce ki bar masa gidan shi!

"Wallahi shi ya ce Gwaggo "

Na faÉ—a ina jan hanci irin na masu kuka.

"Me kika yi masa da zafi haka? Gaskiya ya ba ni mamaki ai ko mai kika yi masa bai kamata ya yi miki haka ba "

Ina goge hanci ina zayyana ma Gwaggo abin da ya faru ina hawaye ina faɗin" Abin takaici Gwaggo wai ni Yallabai ke kallona ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa saboda tana haihuwan yaya maza ni kuma mata shine ina bakin kishi da ita na kasa hakuri na saka an dakar masa mata shi ne ya zo yana ta faɗa mini mganganu son ran shi daga ƙarshe ya ce na bar masa gidan shi"

Gwaggo ta yi salati ta dire kafin ta ce"oH ni Maimuna. Ashe yarinyar makira ce? Ina ganinta shuru shuru kamar ta Allah. Su suka shirya masa komai, shi kuma laifin sa ɗaya rashin bincike sannan na ga ɓakin sa da ya iya buɗe baki ya ce ki bar masa gida Haba. Ai ba ki cancanci wannan tozarcin ba.'

Uhm"

Kawai na iya cewa saboda zuciyata suya take yi. In ina tuna abin da ya faru.

"Umma ba cewa fa ya yi ki tafi ba. Ke kika ce mai za ki tafi ya ce shi ba zai hana ki ba "

Marwa na ƙura ma ido cikin takaicinta da bakin ciki. Na ma kasa mgana saboda na rasa abin da zan ce mata. Ina tunanin ba ni ce ƙanwar uwarta ba Yusuf Muhammad Inuwa ne.

"Af to me ya rage? Ai duk ɗaya. Mata ai mu haka Allah ya hallice mu, wata ƙila ta fadi haka ne ta gwada zurfin matsayinta shi kuma sai bai ba ta kunya ba, ya nuna mata iya na shi tattalin a kanta ya ce ta tafi ba zai hana ta ba. To ai shike nan bari Alhaji ya dawo sai ya ji shi ne da an tashi hira sai ya ce mijin Dubu  dabam ne ina ganin ƙimarsa. To ai yau ga ƙarshen ƙima nan ya kore masa ƴ'a gabanin mangariba da isha'a da girmanta da komai, bai yi miki haka kina da kuruciya ba sai da shekaru suka fara gangarawa."

Gwaggo sai faɗa take yi ni sai na ga ma ta fini ɗaukan zafi. Har a ƙasan raina ban ji daɗin da ma zo gida na buɗe cikina ba amma kuma ai shi ya ja. Da bai yi abin magana ba da ba a yi magana ba. Alwala muka yi ni da Marwa muka yi salla muna cikin sallar Alhajinmu ya dawo shi ya sa muna idarwa Gwaggo ta zo ta kira ni, da man a ɗakin Mama muka yi sallar.

falon Alhajinmu na koma yana zaune ga kwamukan abinci Gwaggo ta jera masa amma bai taɓa komai ba. Duk da ya nuna kamar bai damu ba amma na san ya damu ya kasa yin wani abu ba tare da ya ji damuwata ba. Allah sarki Alhajinmu ina son shi saboda in dai matsala ta tunkaro iylanshi shi baya samun natsuwa sai ya ga ya yi maganin matsalan nan. Dattijo ne mai juriya da jajircewa. Sai a lokacin na ji nadama da tunanin me ya sa na taho gida na ɗaga musu hankali? Da man ban zo ba, ssi wata zuciya ta ce gwara da kika zo a karon farko yau dai Yusuf zai fahimci ba da gidan shi kaɗai kika dogara ba.

"Dubu."

Alhaji ya kira ni kamar yadda ya saba. Ina mai zama gaban shi na tankwashe kafa na amsa masa.

"Na'am ina yini Alhajinmu."

"Lafiya lau. Sai kika baro mini mata can tana kuka?

Kaina na kasa na kasa mgana.

"Bai kamata laifin wani ya shafi wani ba Dubu. Rukayyatu nawa take da za ta fara karban hukuncin da ba na ta ba? Ba mama take sha ba har yanzu?

"E Alhajinmu."

"Kin ji ko? Me ya sa kika yi haka Dubu? Koda na sanki da fushi ai ban san ki da rashin tausayi ba ko?

"Ka yi hakuri Alhaji na yi kuskure."

"Kin yi kuskure babba. Domin kin ɗauki alhakin ran da bai ji ba, sannan bai gani ba, kar ki ƙara irin haka komai zai faru kar ki yi hukunci a in da bai dace ba. Ina ruwanta? Ta sam ne babanta ya yi miki? To ko domin wata rana ki yi aikin hankali kin ji ko?

"Na ji. In sha Allahu ba za a sake ba."

Na faÉ—a ina wasa da gefen hijabina.

"Yauwa. In kin baro ita Mai sunan Gwaggon ta ku ita babba ce. Amma Rukayyatu kin ɗauki haƙƙin ta."

Ni dai na yi shuru, saboda sai a yanzu da Alhaji ya sake jadadda mini sannan na sake fahintar ban kyauta ba. Ina jin nonuwana suna cika na san tana can tana rigima.

"Allah ya kyauta na gaba."

Na amsa da Amin shuru na wani lokaci kafin Alhajinmu ya sske kiran sunana.

"Halima."

Tun da na ji haka na san mganar mai girma ce.

"Na'am"

"Me ya haÉ—a ki da Yusufa har ya ce ki taho gida a daran nan?

Nan da nan na gyara zama cikin natsuwa na warware ma Alhajinmu komai tun daga farko na haihuwan da ta yi ban je barka da wuri da abin da ya faru yau. Har mganganun da muka yaba ma juna na fada masa, ni fa duk a tunanina Alhajinmu zai goya mini baya in ji É—ibar albarkar da Yallabai ya yi mini saboda matarsa.

"An faɗa masa ƙarya da gaskiya daga can Alhajinmu kawai yana zuwa gida ba bincike bai ji ta bakina ba kawai ya fara mini masifa da faɗa kamar zai dage ni."

Na ƙarishe faɗa ina goge ƙwalla da gefen hijabina. Domin ina mai da yadda aka yi hawaye suka kece mini.

Alhajinmu ya yi shuru ni na ma É—auka ko wani abu ne sai da na dago kaina na ga kallona yake yi na wani lokaci sannan ya gyaÉ—a kai ya yi wani mirmishin su na manya kafin ya ce.

"Dubu ba dai kina so ki faÉ—a mini rashin kunya kika yi ma mijin naki ba?

"A'a. Kawai dai raina ne ya baci nima na ma yar masa da martani Alhajimmu."

Sai ya yi dariya wannan karon mai sauti kafin ya ce" Hohoho hausawa suka ce ko shekara É—ari ka yi baka haÉ—u da mutum ba. In ka fara ganin shi tambayi halin shi, domin hali zanen dutse ko zai iya sauya komai to ba zai iya sauya wannan halin na shi ba."
Na yi kasaƙe saboda ina so na fahinci in da maganar Alhajinmu ta dosa.

"Dubu na san ki sarai bakin ki ba ya iya shuru. Kina da saurin hasala da faÉ—a. Kina so na ce kinyi daidai da abin da kika yi ne? To ba zan ce kin yi daidai ba sai ma na kira sunan ki ki amsa na sanar da ke da kaushin murya da cewa ba ki kyauta ba."
Chapter 62 · 0% Book details