Sashe 25
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ƙyale shi. Tsokanar ki yake yi kuma jin daɗi yake yi fa. Ki daina biye masa kin ji ko?
Ina sharan ƙwalla na ce" Da man nima ai ba na biye masa "
Ita ta yi ta lallashina ta ba ni haƙuri, mun yi awa ɗaya da wani abu sannan muka yi shirin tafiya ita da megidanta da yara suka rakomu har bakin mota suna ɗaga mana hannu
"Allah ya huci zuciyar gimbiyar Tafida."
Ya faɗa bayan mun fara tafiya. Ganin na yi masa fuska ina hura hanci ba annuri a fuskata kwata kwata. Kaina na mai da barayin window ina kallon giftawan motoci na yi kamar ban ji sa ba sai ya ƙyale ni ya koma suna mgana da Jidda kan mganar buɗe gari sai na karkata kunnina ina jin su.
"Cutar ta fara sauƙi. Tun da an nemi kariya ina tunanin ba zai wuce wata biyu ba za a buɗe gari ku koma makaranta."
"Allah ya sa Abba. Amma har na gaji da zaman gida. Da yanzu ina level 1 fa Abba."
Ta faɗa cikin ƴar shagwaɓa. Sai Yallaɓai ya yi dariya kafin ya ce" Allah ya tsara Nene ta. Kar ki damu za ki shiga makaranta a shekara mai zuwa in sha Allahu."
Ina jin su amma tun da ina jin haushin shi ban nuna ma na ji ba. Ban yi wani murna ba da na kalli cikina sai ƙarsashina ya ragu ina zan je da wannan cikin? In ma na haihu ba hutu ba ne har sai na yi yaye. Wataƙila Yallaɓai ya yi ta addu'a ne shi ya sa ba ni da rabon komawa makaranta.
Muna cikin motar kafin mu kai gida na ji Baby na tambayan shi ina su Khalipa sai a lokacin Gimbiyar ta faÉ—o mini a rai. Kwana biyu ba mu haÉ—u ba sai na ji ya na cewa ba sa gari sun tafi Rano da yara jiya. Har Jidda ke faÉ—in yaushe za a saka Khalipa a makaranta? Ya ce da zaran an buÉ—e makarantu.
Har muka kai gida ina tunanin wani abu. Tuni Gimbiya ta janye ƴaƴanta daga zuwa gidana. Wato na gama cin wahala da su musamman ma Khalipa shi ne yanzu za ta nuna min ita ƴaƴanta ne. Shi kan shi Yallaɓai ya daina tarkato mun su. Wata ƙila ta nuna ba ta so ne sai ya bar ta da ƴaƴanta haka nake tunani. Su Jidda ma ta daina neman su nima ba na cewa su je gidanta. Gwara Baby ma da Jidda. Ita ba ta son zuwa ma kwata kwata. Yallabai ma ba ya matsa musu abin da na fahimta kowa ya zauna in da yake kawai. Kuma Gimbiya yadda take kishi da ni ina da tabbacin ni da ta aure mini miji bana yi da ita. Ta so ni ta riƙa juya ni ta ba ni umarni ta zama ita ke tafiyar da rayuwar Yallaɓai gabaɗaya sai kuma ba ta samu wannan damar ba. Baƙin cikinta Yallaɓai ya nuna ina da daraja. Sai ta ke ganin ya fi sona a kanta nima kuma ina ganin ya na son ta. Daga baya sai na fahimci maza in suna da mace fiye da ɗaya to zargin an fi wata a kaina ba zai bar zukatan mu. Duk yadda ya so ya yi adalci sai wata ta ce ya cuceta. Haka rayuwar namiji mai mace fiye da ɗaya yake.
Ni dai na riƙe maganar da Alhajin mu ya yi mini na zama da ita da zuciya ɗaya. Ruwan ta ne ta zauna da ni da wani manufa ni dai na riƙe Allah kuma shi ne ke yi mini jagoranci a duka lamurana.
Har muka koma gida ina cin mgani ina ta hura hanci. Ban ɗauka zan haƙura da wuri ba sai gashi a daran ya lallasheni na haƙura amma da sharaɗin ba zai ƙara mini dariya ba in ya ƙara duk matakin da na ɗauka ya amince. Sai ya fara cewa zan hana shi dariya ne? Na ce ba zan hana shi ba amma in dai a kaina ne na haramta masa. Da ya ga na tubure sai ya amince tun daga lokacin na samu lafiyan shi in ma zai yi dariyan to a bayan idanuwana yake yi. Tun kuma daga lokacin nake kallon kaina a madubi ina ganin duk na yi baƙi na lalace na yi muni. Sai na daina ganin laifin Yallaɓai in ya yi mini dariya. Tabbas halitta ta jirkice. Komai na fuskata ya yi girma ni kaina ina na ga hancina a madubi na shafa na ji ya buɗe fafa sai na yi ma kaina dariya. Ina ciki mai sauya halitta amma fa shi wannan cikin komai na shi wani sabon salon ya zo da shi.
****
*September*
A ƙarshen watan september lokacin cikina ya shiga wata na takwas kenan. Muka yi wayi gari a safiyar talata da rasuwar yaron Ya Abubakar na farko mai sunan Ya Hamza. Ciwon ciki daga dare zuwa safe, sun ɗauko shi da asuba zuwa asibiti suna hanya ma ya rasu. Yaro ne ɗan shekaru goma sa'an Baby ne ta ma ɗan girme shi da kaɗan.
Ya Aina ta kira ni ta faɗa mini ƙarfe shidda na safe ta ce na zo gida a nan za a yi masa wanka da sallah. Yallaɓai ba ya gidana ya na can gidan Gimbiya sai na kira shi a waya amma bai ɗauka ba a na farko sai da na sake kiran shi Gimbiya ta ɗauka ba gaisuwa ba komai ta ce mini wai yana wanka. Duk da na ji wani motsi a cikin zuciya ta ban nuna mata ba sai na ce in ya fito ta faɗa masa yaron Ya Abubakar ya rasu za mu tafi Ɗorayi ni da yara sai ta ce to za ta faɗa masa sai a lokacin ta ce Allah ya jiƙan sa na ce Amin.
Bayan na kashe wayar sai da na duba lokaci shidda na safe ta gota da mintina ashirin. Na san kuma dalili ɗaya ke saka Yallaɓai wankan safe. Wani abu ya ƙara sukan raina daman da gayya ta ɗaga wayar domin ta faɗa minI ta yi sunna da Yallaɓai. Ganin ni da a ka yi ma rashi tuna kishiya ba nawa ba ne sai na watsar da maganar Gimbiya na fita na je ba yi ma su Jidda mgana na ce su shirya mu je ɗorayi. Hamzan Ya Abubakar ya rasu Baby sai ta fara kuka Allah sarki abokin wasanta ne in dai suka haɗu Jidda ma ta yi shuru jikinta duk ya yi sanyi.
Ba mu tsaya wanka ba muka saka hijabai na kulle gida muka samu adaidaita zuwa can Ɗorayi. Gida cike da mutane har Ma'u a can na ganta. Sai dai ina zuwa Rahila na zuwa har Zaitunan da ƴan'uwanta suna gidan Allah Sarki ta na ta kuka gwanin ban tausayi. Gwaggo ce ta yi ma yaron wanka su Ya Abubakar da Alhajinmu da su Ya Muntari duk suna waje a ƙofar gida. Bayan Gwaggo ta gama yi masa wanka a ce iyayen shi suje su gan shi su yi masa addu'a. Shi dai Ya Abubakar ya yi dakiya amman Zaituna sai da a ka riƙe tana ta kuka kamar za ta shiɗe. A ƙofar gida a ka yi masa salla sannan a ka tafi kai shi gidan sa na gaskiya. Allah ya ba mu sa'a. Su Jidda duk sun yi tsuru tsuru jikin su ya yi sanyi. Rayuwa kenan Allah ka kyautata ta mu bayan ta su Amin.
Sai da a ka dawo daga kai shi can wajen sha biyu Zaituna da ƴan'uwanta suka koma can gidan ta saboda masu zuwa mata gaisuwa mu kuma sai muka zauna a nan saboda makota. Amma Ya Balki ta bi su can gidan, su Amina duk sun kira sun yi gaisuwa Ya Hamza da Ya Auwal sun kira kuma matan su sun kira. Sun ce za su shigo gaisuwa weekend saboda yanayin aikin su. Sai can rana Yallaɓai ya kira ni ya ce mini gashi ya zo ya ba ni mamaki tun safe sai yanzu? Sai da ya shigo cikin gida muka keɓe muna mgana ne ya ce mini Gimbiya ba ta faɗa masa ba har sai da ya tashi barci. Kasa mgana na yi kawai na tsaya ina kallonta.
"Lalle."
Kawai na iya furtawa saboda mamaki ya hana ni ma mgana.
"Sai da na yi mata faÉ—a. Wai ta manta ne ba ta faÉ—a mini ba lokacin da ta tuna kuma na kwanta. Na ce da tashe ni ai mutuwa ta wuce komai."
Ni dai kawai na kalle shi amma ban yi magana ba. To me zan ce? Ai da yaron yayanta be ya rasu ba barci ba ko me yake yi za ta tashe shi ta faɗa masa amma tun da bai shafe ta ba ba za ta damu da ta faɗa masa a kan lokaci ba.
"Ki yi haƙuri. Allah ya jiƙan sa."
"Amin"
Na amsa masa kafin na ce" Ka zo kuma Zaitunan ta koma gidan ta É—azu."
"Ayya to mu je ki rakani na yi mata gaisuwa daga can sai na wuce office."
Sai na ce masa to daman muna korido ne a tsaye muna mgana cikin gida na koma na ɗauko Hijabi ina faɗa ma Gwaggo zan raka Baban su Jidda gidan su Zaituna. Rahila na zaune ta miƙe ta ce za ta je. Ma'u na kalla tana zaune ta yi tagumi tun da safe na lura da ita ba ta da kuzari ta yi firgai firgai kuma ni dai a yadda na san Ma'u ba haka ta ke ba. In ma idanuwana sun gano min dai-dai ta rame ta yi baki sannan ba gayun nan ba surutu. Kuma ba za a ce mutuwar da a ka yi ba ce ta mai da ita haka ba ai Baaba na raye ban ga abin da zai saka Ma'u ta susuce haka ba. Ko a lokacin suna zaune kugu da kugu ita da Ya Murja. Wataƙila koma me ke damunta ita za ta fi kowa sani tun da suna tare.