Sashe 75
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Har nan falona in da kike zaune nan megidanki ya zauna ya sanar da ni zai ƙara aure, ya kuma dawo ya roƙeni na shirya aje nema masa aure da ni sai kuma aka yi rashin sa'a ranar zan je Yashe shi ya sa ban samu zuwa ba amma na yi masa alƙawarin zuwa masa ɗaurin aure."
"Maidugurin Alhajinmu.?
Na faÉ—a ina zare ido saboda mamaki.
Sai kawai Alhajinmu ya yi dariyar su na manya kafin ya ce" In sha Allahu in dai muna raye zan je. Ai ya girmama ni matuƙa nima zan ma yar masa da girmamawan sa."
Uhm kawai na ce na ma kasa magana saboda mamakin Alhajinmu wai zai je har Maiduguri ɗaurin auran Yallaɓai, ni bai ma taɓa nuna mini ya zo ba ashe ya zagayo sai da na koma gida da Yallaɓai ya zo yi mana sallama a daran nake masa mganar aahe ya wanke kafafunsa ya je ya faɗa ma Alhajinmu maganar aurensa.
"Ya ba zan faɗa masa ba! Me kike nufi? Alhaji ai uba ne dole na je na same shi na faɗa masa komai dangane da aurena. Bai ma samu zuwa maganar auren ba amma ya yi mini alƙawarin zuwa ɗaurin aure har can maiduguri "
Kallon Yallaɓai kawai na ke yi, a fatar baki na ce Allah ya kaimu da rai da lafiya. Tun da Alhaji ya yi niyya wa ya isa ya hana shi, ni ma kafin na fito sai da ya sake yi mini nasiha sosai akan haƙuri na zauna kuma da kowa tsakani ga Allah, ina jin daɗin manganganun Alhajinmu shi dai har na zama mai ɗaga ma mijina hankali. Na zama mace mai samar masa da zaman lafiya a cikin gidan shi, haƙurin da na yi a farko yanzu na ninka shi, nan gaba kaɗan zan ga riban haƙurina ko ya ce zan ƙara gani domin ribar haƙuri na gan shi tun da har gobe mijina ya yaba mini da hallaya masu kyau.
Tun da aka sanya lokaci Yallaɓai bai zauna ba shiri kawai yake yi kamar zai yi auran farko. Ko da yake budurwa zai ɗauka dole ya yi rawan jiki, ranar sati na zuwa Yallaɓai ya ce na shirya yara za su je su gaida Gimbiya. Shi ya sa ya ƙi ma yar da su Khalipa gida, ni na ma manta da zencen amma shi yana sane bai manta ba faɗa mini yake yi ai ta riga ta gama shirin tarɓansu tun da ya faɗa mata za su zo, Jidda na saka ta shirya yaran suma na ce su shirya sun ci gayun su ni dai ba ni da komai Hijabi da mayafi na ba ma Jidda na ce ta kai ma Antyn na su. Yallaɓai kamar bakin shi zai yage saboda farinciki shima ya ci gayu yana rawan jiki har sai da na yi masa magana.
"Yallaɓai wai ba can za ka bar yaran ka wuce office ba?
"E ina tunanin haka akwai baƙin da zan gani."
Sai na yi shuru domin na ga yana rawan kafa ne har ya wuce misali, har yana yi mini godiyan saƙon da na ba da akaikace na ce bakomai yiwa kai ne.
Shi ya ɗauke su a motar shi, tun wajem sha ɗaya na safe, ina jira na ga Yallaɓai ya dawo mini da yara amma shru har la'asar shi kuma na kira wayarsa bai ɗauka ba sai na kira Jidda ina mata faɗan zaman me suke yi ne har yanzu ba su dawo ba.
"Umma Abba ya ce mu jira shi zai dawo ya É—auke mu."
"Kenan shi kuke jira?
Na faÉ—a ina mai kama baki, kafin ta yi magana sai na ji an yi mini sallama cikin sanyin murya ina jin murya na gane na Rabi'atu ne
Gaishe ni ta yi na amsa nima cikin sakewa kafin na ce" Yau an kawo miki gidan gabaÉ—aya hayaniya ya dame ki ko?
Tana mirmishi ta ce" A'a ni da man su kwana Anty"
Sai nima na yi dariya kafin na ce"Haba dai. Ba yanzu ba ki jira saura ƙiris wata rana ma sai kin kore su saboda gajiya."
"Ni ba zan kore su ba. "
Ta faɗa tana yar dariya, godiya ta yi mini na saƙo na ce mata haba yi wa kai ne. Na ce su kira Yallaɓai in ba zai samu komawa ya ɗauke su ba Jidda ta yi jagoranci su samu a daidaita su dawo gida yamma ta yi.
"Ya ce zai dawo ya É—auke su. Na san yana hanya."
Ai ni sai na kasa magana tun da ga abin da ya ce. Ni dai ban ga yara ba sai bayan sallar isha'i, Yallaɓai bai isa can ba sai bayan mangariba can suka ci abinci sannan ya tarkato yara suka taho. Baby ke faɗa mini a mota suka jima Abban su na cikin falo da Antyn na su. Ni fa tsoron rawan jikin Yallaɓai na ke yi a kan yarinyar nan har ta haukata shi, sun dawo da kayan zaki kaya guda kamar za a buɗe shago su bickit ne da su katan ɗin boo na yara. Yallaɓai yana faɗa mini ya ce ta bar shi amma ta fara fushin yana nuna mata su Jidda ba ya'yanta ba ne, ni dai ban yi magana ba saboda ba ni da ta cewa
Godiya ma shi ya yi mini na ci sai na kirata na yi mata godiya kamar wani laifi ne in ban yi mata ba haka nan na ce Jidda ta kira ta a wayarta tun da sun karɓi lambar wayar juna. Shi ne na samu na yi mata godiya tana ta jin kunya da man iyayin Yallaɓai ne amma ni na san har tsaraban ma duk shi ya siya ba wai ita ba, in ita ta siya ma da kuɗin shi ne.
Washegari Lahadi Gimbiya ta aiko aka tafi da su Khalipa. Da man ko ba ta aiko ba ina shirin na roƙi Yallaɓai ya ma yar da su to sai ga shi bayan fitan shi, ta aiko Salisu ya zo ya tafi da su. Da ya dawo a daran da man yana gida ne, ya ga bai gan su ba ya tambaya na ce sun koma gida.
Sai ya fara faÉ—an wai ba na jin maganarsa me ya sa zan ma yar da su ba tare da izinin shi ba.
"Ah ni fa ba ni na ma yar da su ba kana fita mamansu ta aiko Salisu ya tafi da su."
Sai ya yi shuru bai yi magana ba amma ya yi ƙyafci alamun ran shi ya ɓaci ni ko a raina na ce can ku ƙarata ba ruwana. Sai da muka zauna ne Baby ke ba ni labarin da suka je gidan su Antyn ta su haka ake ta zuwa ganin su, a raina na ce dole a zo a gan ku Jidda ba ta magana ita da man Baby ce da man yar surutu amma faɗa mini take yi Antynsu na da kirki gidan ta za ta koma na ce Allah ya ba da sa'a.
Jidda ce mini kawai ta yi She is young Umma, ko ba ta faɗa ba na san ƙaramar yarinya ce Yallaɓai zai aura. Kuma yadda yake rawan kafa wannan in aka yi auran sai Allah kawai kar Yallaɓai ya lalace a gindin yarinya ƙarama. Ni ban san a in da Gimbiya ta ji labarin su Khalipa sun je wajen Antyn ta su ba amma na fi tunanin a bakin Khalipa ta ji tun da yana da magana shima. Kawai bugo mini waya ta yi da man tun zuwan su gidana na ce ba na tare da su ba mu ƙara magana ba.
Ni wai Gimbiya ta buga ma warning akan me ya sa zan yanke hukunci kan ya'yanta? Me ya sa na tura su gidan wata banza ba tare da sanin ta ba.
Ni ko cikin mamaki na ce' Umarnin megidan ne amma ba ni na tura su ba "
Sai ta fara masifa tana faÉ—ar manganganu wai da sanina aka yi komai da ban ba da goyon baya da ba a tura mata yara gaida wata banza ba tare da sanin ta ba.
"To ki yi haƙuri."
Haka kawai na ce mata ganin kamar ni ce take jin haushi yanzu ba mijinta da zai ƙara aure ba.
"Ahto ni dai a kiyayeni. Ya'yan dai nawa ne ba wani ya haifa mini ba, in kina son neman sunan ki aika na ki Æ´a'Æ´an amma ban da nawa."
"To in sha Allahu hakan ba za ta ƙara faruwa ba'
Kawai sai ta yi mini tsaki mai girma har ina jin sa a cikin kunnuwana sannan ta kashe wayarta ta bar ni sake da baki. Ni zan fita? Ina ruwana a wannan maganar da abun zai dawo kaina? Raina ya ɓaci amma sai na danne zuciyata na ɗau girma na yi haƙuri shi ya sa ko zencen ban yi ma Yallaɓai ba. Nima bai yi mini ba. Mun shiga tsakiyar watan December, Yallaɓai na ta shirin shi na gida ina ga ma an gama gyara bangaren da Rabi'ar za ta zauna sai maganar lefe ya fara yi mini. Da cewa ya yi magana da Mimisco ta ba shi shawaran kawai ya ba ma ita Rabi'an kuɗi ta siya komai da kanta. Nima da ya faɗa mini na ce hakan ya yi, tun da Mimisco ita ce kaɗai ke supporting ɗin sa sai su Suwaiba amma su Anty Bahijja sun ja tunga shi ko ya ce uwarsa ba ta hana shi ba ba wacce ta isa ba.