Sashe 70
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ranar da muka yi magana yana gidan Gimbiya ne sai washegari da zai dawo gidana ya saba dawowa da wuri, amma yau har goman dare bai shigo ba na gaji da jiran shi kuma na kira shi bai ɗauka ba. Kamar zan kira Gimbiya sai na fasa tun da ni ban saba kiran ta haka ba. Baby ce daman ke jiran shi kan maganar JSSCE ɗin ta na makaranta ta ƙi yin barci daga ƙarshe da ta gaji da jira dole ta kwanta.
Ba Yallabai ya shigo ba sai sha É—aya saura. A yanayin da ya shigo mini ba na lafiya ba ne. Toilet ya faÉ—a yana faÉ—a mini cikinsa ya lalace. Wayarsa da babban rigan sa ni ya bari da su tunda ni ce na tarbe shi.
Na shiga bedroom É—in mu da niyyar na ijiye masa wayar da key É—in mota sai rigan shi. Ina shirin ijiye masa wayar a saman gado kira ya shigo. Gabana ya faÉ—i ras!
Ganin sunan mai kiran RABI'ATU BUK."
Har ta katse na kasa daina kallon wayar. Kaf a tunanina ban tunano wata yar uwan Yallaɓai mai wannan sunan ba. Ban gama mamaki ba gur! Saƙonta ya shigo wayar daga sama na ja na fara ganin abin da ta rubuto.
"Yallaɓai na ka isa gida lafiya? Mun gode...!
Daga nan sai saƙon ya yanke, jiki na rawa na watsar da rigar hannuna ina ƙoƙarin gwada buɗe wayar amma na kasa.
Wata zuciyar ta ce Sadiya ki natsu ki yi aiki da hankali. Sai kawai na ijiye ma sa wayarsa nan saman gadon na zauna a gefe na É—aura kafa É—aya kan É—aya ina girgizawa.
Mintina biyar sai ga shi ya buÉ—e kofar bedroom É—in ya fito yana nishi sama sama.
"Cikina kawai ina hanya ya karta. Ina zuwa sai gudawa kina da ko pulajin ne Sadiya?
Ya faɗa yana dafe cikinsa. Lokaci ɗaya yana ƙarisowa gabana yana kuma ƙoƙarin cire rigar jikinsa.
"An kira wayarka. "
Ya kalleni a É—an tsume yana cire rigan daga shi sai farar vest.
"Ta kuma turo saƙo."
Sai kawai ya tsaya yana ksllona. Nima ina kallon fuskar shi yanayin shi ya nuna tsoro amma sai ya yi dakiya irin ta maza.
"Rabi'atu ce ko?
Ya faÉ—a yana kallona.
"E ita ce"
Na faɗa ina kallon shi, shima yana mai kallona sai kawai na ga ya yi murmishi. Mirmishin da na ji ya soke ni a ƙasan zuciyata.
*Janafty**TKGB3017*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX
Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732
Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰
"Da man na san za ta kira."
Ya sake faɗa lokaci ɗaya da ƙwatanƙwacin irin mirmishin da ya yi a farko lokacin da na ce an kira wayarsa.
Gabana ya sake faɗi ras! Ba tunanin komai na kawo ba sai tunanin Yallaɓai ko dai ya fara bin mata ne? To ni dai ban san wannan yarinyar ba sai yau amma shi a yanayin da ya nuna kamar ya jima da sanin ta. Sannan fuskarsa ta bayyana asirin zuciyarsa na yadda take da muhimmaci a wajen shi koda bai furta da fatar baki ba.
"Yallaɓai."
Na faÉ—a jikina na rawa tare da zuciyata ban san ma na sauke kafafuwana daga harÉ—e sun da na yi ba sai da na ji suna karkawa, tare da dukan junansu saboda tsoron tunanin da ya shige ni yanzu nan.
"Na'am."
Ya faÉ—a yana mai kallona fuskarsa ba alamun wani firgici ko nadama.
"Me ya faru?
Ya faÉ—a yana mai sake kure ni da ido, sai na ga kamar yana neman raina mini wayau bayan ya san abin da ya faru amma kuma yana sake kallona yana tambayata me ya faru?
"Wa ce ce Rabi' atu?
Na fada da sigar tambaya amma a rarrabe saboda fargaban amsan da zan ji ya faÉ—a mini. Ni fa cikina har curewa ya yi waje É—aya nima ina jin kamar in na yi motsi zan iya barkewa da zawo saboda zullumi.
"Wata ce ba ki san ta ba."
Ya faÉ—a yana sauke rigar hannunsa a saman gado. Sai kuma ya saka hannu ya É—auki wayarsa yana dubawa.
Mirmishi yake yi alamun yana karanta saƙon nata ne.
Ban san ina da wannan ƙarfin ba sai da na ganni tsaye kan ƙafafuwana lokaci ɗaya kuma na saka hannuna da ƙarfi na fizge wayar daga hannun shi.
"Wace ce Rabi'atu Yusuf ina tambayan ka kana faÉ—a mini wai ban santa ba. Wace ce wannan yarinyar ehe?
Na faɗa ina mai ɓoye wayar a bayana sannan cikin ɗaga murya nake maganar. Ni fa na gama tunanin kaf na haɗe shi waje ɗaya Yallaɓai ya fara neman mata a waje shi ya sa yanzu ba shi da lokacin mu.
Innalillahi Wa'inna alaihirraju'un. Nake nanatawa a cikin zuciyata lokacin da na ga kawai ya kalle ni amma bai yi magana ba.
"Yusuf wace ce Rabi'atu?
Kar dai a ce abin da zuciyata take zargi akan ka gaskiya ne?
Na faÉ—a ina jin zufa na taruwa a saman hancina tsabar tashin hankalin da nake ciki.
"Me zuciyarki ke tunani na a kaina Sadiya?
Ya faÉ—a hankalin shi a kwance har yana karya hannayensa a saman kirjinsa alamun bai damu da yanayin da na shiga ba.
"Yusuf neman mata ka fara yi? Mu har ka gama moran mu ka fara hango matan bariki?
"Subhanallah wannan mganar bai da ce ba Sadiya. Allah ya tsare ni da aikata ɓarna. Ban yi da ƙananun shekaru ba sai da girma ya kama ni Sadiya?
Ya faÉ—a a yanayin muryansa da É—an bacin rai kaÉ—an. Domin har yana sauke hannuwan shi ya nufe ni da su yana faÉ—in.
"Taho mu zauna na yi miki bayani."
Da sauri na ja baya domin ni kawai idanuwana suna hango mini Yallaɓai wasa yake son yi da tunanina shi ya sa.
"Na saurare ka? Me za ka faÉ—a mini? Tun farko me ya sa da na tambayeka wace ce ita ba ka faÉ—a mini ba?
"To mun bar É—akin nan ne kika ga ban faÉ—a miki ba? Da man ko ba ki gani ba ina da shirin sanar dake a kwanakin nam."
Sai kawai na saki baki ina kallon shi, a gefen gado ya zauna hankalin shi kwance.
"Na ce ki taho dai ki zauna mu yi magana."
Ya faÉ—a yana nuna mini gefen sa, sai na É—auke kaina kafin na jijjiga jikina ina faÉ—in" In ba ka yi lalacewa kana matashin ka ba, yanzu da ka haÉ—u da yar iska yar bari.."
"Ya isa haka Sadiya."
Ya ɗaga mini murya sannan ya ƙara da ɗaga mini hannu abin da ya hana ni ƙarisa maganar da na ɗauko.
"Me ya sa kika kasa shaida na ne Sadiya? Ashe ba za ki iya rantsuwan a kan bayan ku da kuke gonakin da Ubangiji ya hallata mini ba, ba zan iya shinshinar gonar da ba mallakina ba ne? A she ni ba za ki iya mini wannan shaidar ba?
"Ɗan Adam mai sauyawa. Tun ballanta jinsin Namiji. Me ye kake ɓoye-ɓoyewa in ba wata yar bariki ka samu a waje tana ɗauke maka hankali ba?
Na katse shi nima ina taso masa sai kawai ya yi shuru amma ya kalleni yadda na firgice da zargina shi ya sa sai ya gyaÉ—a kai kafin ya ce" Ko dai mu jinsin maza muna sauyawa amma ba sauyawa ta wannan bangaren ba Sadiya. Ba maganar yar bariki kuma ki daina faÉ—a, ba ki san wace ce Rabi'atu ba, sabo da haka ki daina danganta da sunayen banza."
"Ƙarya na yi. Wace ce ita in ba yar bariki me bin mazan wasu a titi ba?
"Ba ita ce ke bi ni ba. Ni ne ke bin ta Sadiya."
Ya faÉ—a yana kallona. Kamar an iska ya wuce ta gefen kunnuwana haka na ji kamar sautin wani abu ya wuce.
Shuru na yi ina kallon shi, shima ni yake kallo.
."Me ha kan ke nufi?
Na faÉ—a ina mai raba bakina saboda rawan da ya fara yi mini.
"Sadiya Rabi'atu ba karuwa ba ce sannan ba Æ´ar bariki ba. Yarinya ce da ta fito daga gidan tarbiya da dattako."
Ni fa duk ba nan na ke so ya je ba. Matsayinta a rayuwarsa na ke son sani.
"Ni na ganta na ce ina son ta."
Sai na yi ma Yallaɓai zuro kamar na warke makanta.
"Kuma AURANTA zan yi in sha Allahu "
Shike nan ƙurungus kan kusa. Ni gabaɗaya na sha'afa idanuwana sun rufe na manta cewa bayan biyu. Ubangiji ya ce su cike huɗu in har za su yi adalci, na sha'afa da cewa bayan mu akwai guraben mata biyu, tunanina da zuciyata kawai suna hasko mini Yallaɓai ya fara neman matan bariki saboda yana da kuɗi. Su kuma matan bariki da man in har kana da kuɗi shike nam za su tallata maka ƙofar lalacewa.
Na manta yadda ya aure ni ya kuma auri Gimbiya. To watan wata rana in ya yi ra'ayi zai iya auro wata ko wasu ma biyu bayan mu. Na manta ko na ce ban É—auka yanzu ba ne. Kamar yadda auran shi da Gimbiya ya shammace ni haka labarin wannan auren ma ya sake shammata na.
Na kasa motsi daga in da nake tsaye. Zuru kawai na yi ina bin Yallaɓai da kallo shi kuma ganin haka sai ya taso ya zo ya kamani ya zauna da ni a gefen gado sannan ya kuma ya zauna a gefen har yana dafa kafaɗata hannunsa na rito a wajen kirjina.
"Bayanin da nake so ki zauna na yi miki ne tun farko kika kasa zama ballanta ki fahimce ni."