← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 103

Sashe 9

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Bakomai kawai ban ji daÉ—in da ba ki faÉ—a mini zaki kwana ba ne."

Baki na buɗe na sake rufewa ya wani sassauta murya jin na bashi haƙuri sai ma abin na shi ya ba ni dariya sai da na murmusa shima ina jin sa ya ɗan yi dariya kafin ya ce.

"Na yi kewar mirmishin ki Sadiya ta. "

"Uhm!"

Na faɗa a ƙasan maƙoshi.

"Sai kin dawo goben a matsayina na Babba zan ba ki haƙuri a duka laifukan  da kike tunanin na yi miki su Sadiya."

Ban yi magana ba amma na yi shuru ina jin sa. Ban yi mamaki ba daman na san ya na neman hanyar da za mu shirya ne.

"Na gaji. Na gaji da wannan horon da muka yi ma juna. Ki dawo mu zauna mu warware komai a tsakanin mu kin ji ko?

Ya faÉ—a cikin sanyin murya sai na gyaÉ—a kai kamar ya na ganina kafin na ce.

" Sai da safe.'"

"Sai da safe Madam."

Daga haka na katse wayata. Na daɗe zaune ina tunani daman ai yanzu duk zai ce na yi haƙuri shi ba da gayya ya faɗin duk mganar da ya faɗa ba. In ma na haƙura amma ba shi zai saka na manta da abin da ya yi mini ba.

*Janafty*.*TKGB30C3*

*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*

Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732

Washe gari tun safe muka tashi da aikin nama muka soye shi a ka raba a ka ɗibar ma dangin mijin Saude kafin mu haɗa kayan tafiya. Tashar mota ya samo mana tun daga ƙofar gidan Saude a garin Jigawa har zuwa ƙofar gidan su a anguwan Ɗorayi da ke Kano, zuwa la'asar duk muna Kano ni daman muna isowa na shige gidan Gwaggo na yi salla na iske har lokacin Alhajinmu bai dawo ba.

"Gaskiya Alhajinmu ya ga wuri. Yashe ta yi masa daÉ—i wannan karon."

Na faÉ—a ina dariya Gwaggo ta ce ai ko wannan karon dai ya daÉ—e, ni kaina ban samu kiran shi ba sai a lokacin har ya ba ni Baba Aminu muka gaisa da shi yana ta saka mana albarka.

Ina shirin tafiya sai ga saƙon naman suna da yawa daga gidan su Saude har da omo da sabulu na Gwaggo. Da zan tafi tare da Gwaggo muka shiga gidan ta yi ma Saude barka a nan na bar ta na wuce gida na shiga gida ba daɗewa domin ruwan zafi kawai na ɗora ban ma san me zan dafa ba su Jidda suka dawo daga makaranta kawai sai na sulala mana indomie na haɗa da ƙwai na dafa mana muka ci, tun da yamma ta yi sannan yau Yallaɓai na gidan Gimbiya ba ni da wata matsala.

Saboda yana neman shiri bayan mangariba sai ga kiran shi, tambayarsa ita ce na dawo? Na ce masa na dawo tun É—azu sai ya ce mini zai shigo gidan in ya dawo. Ban ma san ashe tafiya ya yi ba sai da ya zo gidan wajajen taran dare, ina É—akina saboda yana son shirin da gaske har ciki ya biyo ni, muka gaisa shi ne fa ya ke faÉ—a mini Dutse ya je akwai wani gidan radio da za a gina kuma shi a ka ba ma kwangilar wajen shi ya sa ba ya samun zama ni dai nawa fatan alheri kawai.

Tare da shi muka fito falo ina ba ma su Jidda naman sunan da a ka bani na gidan su Saude. Tsoka bibbiyu na ba su ni kuma sai na saka sauran tsoka ɗayan a bakina akwai kuma saura biyu a hannuna da ƙashi.

" Umma Sadiya. Ni ina nawa naman sunan?

Ba zato kawai na ji maganarsa ban tsaya nuna masa mamakina ba na miƙa masa sauran na hannuna. Sai dai na shanye mamakin nawa da na ga ya saka hannu ya karɓa har kuma ya ɗauki tsokan da ta rage ya saka a baki ya na taunawa.

"Lah Abba kai ma kana cin naman suna?

Baby ta faɗa tana yi masa dariya duƙawa ya yi daga in da muke tsaye a bayan kujerun falon ya lakace mata hanci yana  faɗin" E mana. Ai har na ki naman sunan na ci."
"Na Ya Jidda fa?
Ta faÉ—a ta na dariya.
"Har na ta ma na ci."
"To na Umma fa?
Sai na kalle shi, nima ni ya kallah kafin ya yi dariya ni kuma sai na kauda kaina na zagaya na zauna saman kujeran da Jidda ke zaune ta na ta duba wani littafin Chemistry ba ta shiga maganar Baby da Abban na ta ba.

Na ga dai ya yi mata raɗa a kunne tana kallona tana dariya amma ban san me ya faɗa mata ba. Bai zauna ba ya yi mana sallama ya tafi. Saboda gulma har yana zuwa yana sumbatar goshina. Yaushe rabon duniya da ayyarahe? Amma dai ban kushe sa ba, na yi masa yaƙe Baby ce ta raka shi har haraban gida amma daga ni har Jidda muna daga in da muke ko motsawa ba mu yi ba.

  Washegari da safe bai zo ba amma ya kira ni a waya yana tambayan yadda na tashi ni da yara. Na ce masa muna lafiya sai ya ce zai ta fi Dutse sai zuwa anjuma in ya dawo na ce a dawo lafiya. Ranar a gida na yini ina warware gajiya mun yi waya da Anty Laila maƙotan ta na son hijabai sun gani a wajenta da yake ta siya kuma shima Ya Auwal ya siya mata wasu. Nan da nan na ji ciniki na ce ta tura mini colours da simple ɗin irin wanda suke so sai na tura a ɗin ka musu daga can za a tura musu Abujan ba sai an ma an kawo mini shi nan ba. Datti ma mun yi waya amma ni na kira shi ina masa tsiyan tun da ya fara zaman kansa ya daina neman mutane.

"Kai Ya Sadiya ko kwanaki ba na kira ki ban same ki ba "

"Uhm kai Datti fita idanuwana na rufe. "

Sai ya fara dariya yana faÉ—in" To na ji na amsa laifina a yi min afuwa"
Sannan na yarda muka gaisa yana tambayan ya yara na ce suna lafiya.
"Ko jiya sai da Jidda ta yi zencen ka da cewa Uncle Datti shuru kwana biyu"
"Allah sarki Jiddodi ta na lafiya ko? Ya mganar jarabawarta?
"Yallaɓai ya ce a wannan shekaran za ta yi har Jamb ma."
"Za ta iya ai ta na da ƙwanya mu ta yi gado"

Dariya na yi shima yana ta ya ni, mun sha hira da shi ya ce ma ƙarshen wata zai shigo garin ba sa samun hutu ne mai tsawo ni ko na ce daman aikin kamfani ai sai mai haƙuri. Ina jin zumunci har Ya Aina na kira da Ya Balki muka gaisa Ya Murja ce da na kira ba ta gida yara suka  ɗau wayar Rahila kuma Ya Muntari ya ɗauka ya ce min wayar na hannunsa tun jiya wutar layin su ta lalace wayar ta kwana ba chaji sai ya fita da ita yau ɗin domin ya sa mata chaji bai ma daɗe da kunna wayar ba sai ga kirana. Na dai ce ya gaisheta in ya koma gida ya ce in sha Allahu zai faɗa mata. Amina ce kaɗai da ban kira ba saboda ita ko kafin tafiya ta Jigawa ai mun yi waya. Ma'u kuma daman na yanke alaqa da ita, ba ta kirana ba na kiranta sai dai in mun haɗu a gidajen ƴan'uwa amma dai ban goge lambarta ba kamar yadda nima na ke da yaƙinin ba ta share tawa ba.

Daga nan na yi ta shige shige na a I. G. Ni kaɗai ban taɓa jin ina jin haushin halina ba sai kwanakin nan ba ni da wata ƙawa Aminiya shaƙiƙiyan da yau in na shiga matsala zan je mata da mgana ta saurareni kuma ta ba ni shawara kamar yadda na ga wasu suna dashi, ni ko ni ɗaya tal ban taɓa ƙawa ba bare ba sai su Munnira su kuma aure ne ya haɗa ni da su duk da mun shaƙu amma akwai wani matsalan nawa da ba na iya faɗa musu saboda shi aure ai sirri ne, kuma cikin kowani aure da zamantakewa akwai matsaloli kowa kuma da irin na shi matsalan. Ba komai ba ne za ka zo kana faɗa akwai wani abun da ya ke buƙatar sakaya. Yau da a ce bani da shigen halin rashin sakin jiki da mutane da yanzu ina da ƙawaye na tuna tun muna makaranta ƙawayen da suka yi ta shige mini ina ba sar da su. Har na zo matakin jami'a yan set ɗin mu sun yi ta shige mini amma na ƙi ba ma kowa fuska har Maijidda ma ta layin mu ta so ni har muka haɗu a jami'a da ta ga dai ba na yi da ita sai ta kama kanta.
Chapter 9 · 0% Book details