Sashe 44
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fara aikin babban kamfanin Yallaɓai da wattani biyu muka fara azumin watan ramadana. Kafin azumin Gimbiya ta yaye Anwar a ka kai shi can Rano. Yallaɓai na ji ya na faɗa a nan na ji tun da ba ta faɗa mini ba. Mun yi azumi ashirin da tara mun yi salla a satin salla Jidda suka zana Jamb kuma cikin ikon Allah ta samu 220. Ta cancanta domin ba ta da wasa. Ba daɗewa kuma suka fara WAEC su Jidda an zama yan mata za ta yi graduation zai zama tana da shekara sha takwas cikin na sha tara. Baby kuma za ta shiga Jss2 tana da shekara sha biyu kenan. Na roki Yallaɓai da cewa ya bari na haɗa ma Jidda Waliman gama makaranta har yanzu dai bai ce komai ba. Ya ce sai ya yi tunani. Na lura tun da Yallabai ya koma babban ma'aikata ba ya son kashe kuɗi. Kuma sai ya kashe domin walima zan shirya ma Jidda in ta gama jarabawa kuma da kudinsa za a yi komai in sha Allahu.
*Janafty**TKGB3K011*
Ganin hankula sun kwanta ya sa ranar wata laraba Yallaɓai na gidana muna falon shi bayan mun gama ƙaryawa. Yumna na hannun shi yana yi mata wasa tana ta bangala masa dariyan su na yara.
"Yallaɓai."
"Uhm"
Ya amsa mini hankalin shi na wajen Yumna ɗaga ta sama yake yi yana cillata tana dariya. Yallaɓai ba ya ba ni mamaki in dai akan yara ne, haka yake zai iya ɓata lokacin sa mai tsawo shi da yaran shi ba shi da wannan damuwan in dai yana gidan to Yumna na hannun shi su yi ta kara kaina a kanta shi da Baby.
"Ya maganar koya mini mota? Kyan dai alƙwari cikawa. Yanzu na haihu ba ni da ciki"
Na faÉ—a ina kallon shi ina daga kujera mai zaman mutum É—aya shi kuma yana zaune a saman mai zaman mutum uku ne shi da Yumna.
Kallona ya yi kafin ya ce" Ko ba ki da ciki ai kina da goyo ko?
"Goyo kuma? Yumna ce za ta hana ni koyon mota Yallaɓai?
Na faÉ—a ina cikin mamakin sa, har ina É—an haÉ—e rai domin sai na ga kamar ba ya so kwata kwata ya koya mini motar nan to bai isa ba in ba zai koya mini ba ya ba ni dama na yi ma Musbahu ko Adnan magana su koya mini.
"Ki bari ta ƙara wayau zuwa ki yaye ta mana. Amma ai yanzu ba ki da natsuwar koyon tuki ko Yumna?
Ya faÉ—a yana kallonta sannan ya nuno mata ni yana faÉ—in"ki yi ma Umman ki bore wai za ta koyi tuki ba ki yi wayau ba! Ki ce baki yarda ba."
Kamar tana ji sai ko ta fara wuntsila kafafunta tana wani abu irin na su na jarirai da suke cikin wattanin haihuwa ba su shekara ba.
"Yauwa. Yumna ma ta ce ba ta amince ba sai ta girma."
"Tabɗijam! Ai lokacin ma na ƙware a tuki har Zaria ma ina tuƙa kaina in sha Allahu."
Na faÉ—a cikin gatse har ina mele baki. Kallona ya yi ganin na haÉ—e rai ne ya sa ya fara ma yar da maganar wasa da dariya.
"Har garuruwa ma za ki riƙa zuwa kenan a motar kan ki?
"Ƙwarai da gaske. In sha Allahu."
"To Allah Ya tabbatar. "
Ya faɗa yana yi mini dariya sai na shaka ina hura hanci na sake kallon shi ina faɗin" Za ka cika alƙwari ne ko kuwa ka ba ni izinin na nemo wanda zai koya mini a mutumce?
"Au ni kenan ba a mutumce zan koya miki ba kenan?
"Ni dai ban ce ba"
"Kin ce mana."
Ya faÉ—a yana mai tsare ni da ido.
"To na ga sai kokarin yi mini wulaƙanci kake yi da na yi maka zencen koyon mota."
Sai ya yi murmishi kafin ya ta so daga in da yake zaune ya zo kusa da ni ya zauna Yunma kuma ya É—ora mini ita a saman cinyata shi kuma sai ya saka hannunsa na dama ya sagalo kafaÉ—ata.
"Uhm to mene kuma na fushi? Ni na isa na ce ba zan yi miki abin da kike so ba?
Ina tura baki na ce" To gashi sai againsing É—in maganar kake yi duk lokacin da na ta da maganar."
"Ni har na isa? Ke ba ki san wasa ba ne. Ko shike nan ni ba zan yi wasa da matata ba?
Ya faÉ—a ya na jan kumatuna. Gyara ma Yumna zama na yi a kan cinyata lokaci É—aya ina fadin" To yaushe za mu fara?
"Mu bari weekend ko?
"Allah Ya kaimu da rai da lafiya."
Na amsa ina masa mirmishi.
Shima martanin mirmishi ya mayar mini, sannan ya ɗan ramƙwafa ya sumbaci ƙuncina lokaci ɗaya ya miƙe yana faɗin" Tukwaici me zan samu?
Ina dariya na ce" Me kake so?
"Abin daÉ—i mana."
Ya faɗa yana kashe mini ido ɗaya na san manufar shi ya sa na miƙe ina saɓa Yumna a saman kafaɗata lokaci ɗaya ina faɗin"To ka bari anjuma zan yi maka kyakyawan Tanadi"
"Uhm ni yanzu na ke so."
"Yanzu kuma?
Na faɗa cikin mamaki sabo da ko yau da asuba bai bar ni na huta ba. Amma wai yanzu ya na ƙoƙarin komawa ruwa. Matsowa ya yi kusa da ni ya rumgumo ƙuguna ya na faɗin" Muje ki ba ni, ina son na fita ne yau ina da baƙin da zan gani da ƙarfe sha ɗaya na safe."
"To ka je mana. In ka dawo ai abin daÉ—in ba zai gudu ba"
Ƙirjina ya taɓa har yana ɗan matsaawa har sai da na kalle shi, lumshe ido ya yi sannan ya buɗe yana yi mini wani kallon ƙasa ƙasa.
"Wai ba ka gajiya ne Yallaɓai?
Har ya na wani miƙa yana ta da power hannun shi kafin ya ce" Gajiya? Taɓ ni ai yanzu na ke jin kaina ma."
Taɓe baki na yi bai ƙyale ni ba sai turani gaba da ya hau yi da hannayensa a saman kafaɗuna. Bai kuma ƙyaleni ba sai da ya sake ɓaro mana wani ɓarnan ruwa sai bayan mun gama ne ya yi wanka da zai fita har yana faɗa mini saura na anjuma in ya dawo.
"Wani anjuman? Malam tuƙwaicin har guda nawa ne?
Da hannushi ya ƙirga mini guda uku, hararan shi na yi kafin na ce" Kai dai Yallaɓai sam yanzu ba ka yi mini abu don Allah sai ka dawo ka fanshe ko?
Maganata ta saka shi dariya har yana ƙyaƙyatawa.
"Na ji ba komai. Duk cikin cika sunnar ma'aiki ne(SAW)"
Ni da Yunma muna haraba mun rakosa ya karɓeta ya yi mata wasa ya sumbaceta sannan ya miko mini ita bayan ya haɗamu duka ya rumgume.
"Ki kular mini da kan ki Abar ƙaunata."
Ya faÉ—a yana kai mini sumba a gefen bakina.
Nima na mayar masa da martani kafin na ce.
"A dawo lafiya Allah Ya ba da sa'a."
"Amin My Sady."
Muna tsaye ya shiga mota ya ta da. Daman ya buɗe get ya fita sannan ya dawo ya rufe get ɗin duk muna tsaye ina ɗaga masa hannu shima yana ɗaga mini sai da na ji ƙara tashin motarsa sannan na koma cikin gida ni da Yumna.
Haka ko aka yi weekend na shiga Yallaɓai ya ce na shirya. Ranar farko ba da Yunma muka je ba wajen Baby na bar ta. jidda ba ta nan ta ta fi Tahfezz suna ta ƙoƙarin haɗa haddarsu ne gabaɗaya ba ta samun zama sosai. Ranar farko haka na yi ta rawan jiki da na hannu ban yi wani abun arziƙi ba da ya ke wani fili ne can gabanmu Yallaɓai ke koya mini anan, haka rana ta biyu tare da Yumna tun da Baby ta je Hadda itama Yallabai ke rike da ita ni kuma yana nuna mini yadda ake fara kunna mota da sauran su sai na yi kamar na gane in ya sakar mini sai na yi shirme kuma motar Auto ce shi ya sa za ta yi mini wahala amma ya ce wani sati zai saka Salisu ya kawo ta hannun shi tun da ita Munual ce za ta fi mini saukin koya.
A satin dai haka muka gama ban gane komai ba Yallaɓai na ta yi mini dariya amma daga baya da ya ga na damu sai ya bar dariyan ya koma ya na lallashina da ban baki. Ni har cewa na yi an ya ina da rabon tuka motar kaina kuwa! Tun da gashi nan ma motar ta gagare ni iyawa. Shi kuma yana lallashina da cewa zan iya in sha Allahu. To satin na biyu motar hannun Salisu ya karba ita dai kan an ga sauyi tun da ranar lahadi har ya sakar mini sitiyari amma fa da na fara tafiya sai na ruɗe na kasa yin kwana na saki kan mota Allah ya sa Yallaɓai na gefe riƙe da Yumna ya yi saurin rike kan motar da na halakamu, duk na ruɗe sai da kuma koma gida ya yi mini faɗan na daina ruɗewa na riƙa natsuwa ne in ba haka ba zan daɗe ban koyi abin da ke da sauƙi ba, kuma ya fahimci ina da tsoro to na fara cire wannan tsoron in ba haka ba, to ba zan iya ba.
Haka dai haka dai duk sati muna ta lallaɓawa kuma cikin ikon Allah na fara iya mota. Yallaɓai na sakar mini har na dawo damu gida ma. Ina ta murna da farimciki na iya mota na faɗa ma su Jidda suna ta mini ihun murna suma kar da Baby ta ji labari yan gidanmu kuma na ce mamaki zan ba su sai na yi mota na tuka kaina zuwa gidajen su su sha kallo. Sama da wata biyu Yallaɓai na koya mini mota kuma Alhamdulillah hannuna ya faɗa soaai fiye ma da tunanin shi tun da har cikin gari muna shiga na tuƙa mu, kuma na mayar da mu gida. Sannan har motarsa ma ina iya tukata yanzu lafiya lau.