← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 103

Sashe 36

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na yi dariya kafin na ce ma Sameena." Duk maganganun su Anty Bahijja a kaina ne itama ta ɗauka. Ni gaskiya na riƙe kuma shi ke riƙe da ni har gobe. Maganar hidimar suna kuma wallahi  kayan abinci da kayan sawa kawai Yallaɓai ya yi mini. Sai sauran abin da ba a raasa ba. Maganar gaskiya nima na yi hidima da kuɗina sannan ku ma da muke tare kun yi mini amma ba kuɗin Yallaɓai ba ne balle hankalinsu ya tashi kar na karar da kuɗin ɗan'uwan su."

Sameena ta ce wallahi ita ta sani ita ko magana ta ji a kaina ba ta yarda. Lamarin Gimbiya ya daina ba ni mamaki tun da kishin take so a yi to za a yi. Sannan suna kuma za a yi sai dai ta mutu.

Ni Allah ya ji ƙaina da ban yi haƙuri a lokaci haihuwar Gimbiya ba, da tuni an buga mini tambari amma yau da na yi haƙuri ga shi komai ya wuce abin da Yallaɓai ya yi mata ko rabin shi bai yi mini a haihuwan Rukayya ba amma Na tsaya mata a ƙahon zuciya saboda kishi da baƙin ciki.

*Janafty**TKGB3I09*

RANAR SUNA.
Talata.
17,November. 2020.

A safiyar talata muka tashi da hidiman sunan Rukayyatu(Yumna). Da yake duka nan suka kwana tun asuba suka tashi da aikace aikace kafin ka ce kwabo an gama komai. Alele ne ma ƙarshen gamawa amma waina tun asuba suka fara suya tun da tun a daran jiya suka haɗa ƙullun wainar miya kuma da safen nan wuta kawai suka ta da mata tun jiya sun gama haɗa komai. Kafin azahar komai ya kammallah gida ya fes sannan duk mun yi wanka amma ba mu saka anko ba sai bayan ƙarfe biyu amma ni da yara da ba su je makaranta mun saka sabbin kaya muna walwali. Yunma ma tun safe a ka yi mata wanka a ka saka mata kyakyawan kayan jarirai masu kyau da safa da takalminta na yara mai kyau da hula cikin kayan da Yallaɓai ya ba ni kuɗi na siya mata ne.

Da safen nan ya zo ya gan mu har Amina ta matsa masa sai da ya tsaya muka yi hoto. Shima ya sha farar shadda har da babban riga har sai da na ce masa
" Yallabai hala kai ma walima za ka haÉ—a mana?

"A'a kawai na yi shigar fararen kaya ne domin nuna murnata a wannan ranar"

Abin da ya faɗa mini kenan na yi shuru kawai ina kallon shi ya yi kyau sosai. Sajen sa na shafo in da tsillin furfura suka fara fito masa, Yallaɓai fa yanzu shekarunsa wajen arba'in da takwas ne yana ƙoƙarin shiga gidan hamsin Allahu akbar jiya ba yau ba, ni ina ta kallon shi a matsayin ɗan saurayin da na aura ɗan shekaru ashirin da bakwai da takwas a duniya.

"Kallon fa Madam?

Shi kan shi ya gaji da kallon sa da nake yi sai da ya yi mini magana sai na yi mirmishi. Na isa gare shi na rumgume shi, shima sai ya kama ƙuguna ta baya yana faɗin" Wata Sadiya ta yi kewar Yusuf ɗin ta ko?
Ya faɗa yana sumbatar wuyana. Sai na noƙe ina ɗan mirmishi mun daɗe a haka muna shaƙan turaran juna sannan muka saki juna lokaci ɗaya muna masu kallon juna. Mun raja'a a kallon juna sai da shigowar Amina da kukan Yunma ya fargar da mu sannan muka saki juna na karɓeta na zauna gefen gado shima biyo ni ya yi shi ya zage min zip ɗin gaban riga ta na fito da nono ina ba ma Yunma. Yana zaune gefena muna hira yana faɗa mini Tariq da Kawu sun tura mai kuɗi wai ya ƙara na hidimar suna.

"Allah ya saka musu da alheri. To sai ka ƙara mini wani abu don Allah Yallaɓai."

Na faɗa har langwaɓe kaina sai ya wani kalle ni kafin ya ce" Da ga jin na ce an ba ni kuɗi sai ki ce na ba ki? Ke yanzu me ya rage ba ki yi ba ko ba ki siya ba?
"Yallaɓai ban ɗauko mai DJ da mai hoto ba fa"
Na ƙarishe faɗa cikin shagwaɓa har ina tura masa baki.

Yallaɓai sakin baki ya yi hakan bai ishe shi ba sai da ya riƙe haɓa yana faɗin" Kika ce me?
"Na ce DJ da mai hoto. Domin kasan Haihuwan Yumna na dabam ne za a sha shagali."
"To ni ba da ni ba."
"Acikin gida ne fa Yallaɓai ba matsala tun da duka taron na mata ne."
"Ba amince ba."
"Yallaɓai."
"Sadiya na ce ban amince ba ko?

Ya faÉ—a yana mai kallona a fuskarsa da maganarsa na fahimci ba wasa yake yi ba.

"To shike nan."

Na so na yi fushi ne amma sai na ga bai damu ba kawai ya miƙe yana saɓa babbar rigan shi. Duƙawa ya yi ya sumbaci goshin Yunma kafin ya dago nima ya sumbaci kumatuna lokaci ɗaya yana faɗin" Na tafi. Take care a yi suna lafiya."
Da dai na ga zai tafin sai na ce to ya taimaka mini da kuÉ—in zan kira ko mai hoton ne.

"Wani irin mai hoto kuma Sadiya? In hoto kike so ba ga wayoyi nan ba? Sai kin gaji da hotuna yau."

"Ni fa ba irin shi ba. Na camera nake so"

"Lalle."

Yallaɓai ya faɗa sannan ya cigaba da faɗin" Ni ba ni da kuɗi kin cika tsarabe tsarabe Sadiya. Suna ba dai a ci a sha ba ne? Kuma na tanadi abinci miye wani hoto? Hoton ma da a ka ce haramun ne?

Ni dai ai sai na kasa mgana ina ji ina gani Yallaɓai ya fice ya bar ni zaune bai ba ni ko sisi ba, to ya za a yi ya ba ni shi da ya ce hoto ma haramun ne. Dj dai tun da ya hana amma mai hoto kam zai zo daman mun yi magana da Samira class mate ɗina ita ce na taɓa zuwa sunan yaronta na ga an kira shi sai ta ce mini ƙanin mijinta ne. Na ɗauka zan samu wani abu a wajen Yallaɓai ne sai na ƙara tun da ban samu ba sai na ɗauka cikin kuɗina na tura mata rabi, anjuma da yamma zai zo, na samu kuɗi sosai ko Anty Zabba 20k ta tura mini ta ce ba yawa ni ko na ce mai yawan kenan, ina ta mata godiya. Har mai makeup na samu ita kuma ƙawar Anty Khaleesat ce tare suka yi makaranta ta yi mata mgana itama anjuma za ta zo ta yi mini kafin baƙi su fara suwa.

Kaf yan uwan Mama na gandun albasa sun taho mini suna. Kuma na ji daɗi sai na sauke su a ɗakin su Jidda. Falon Yallaɓai kuma na ce a bar ma dangin Yallaɓai saboda ba na son ƙananun mganganun falon su Jidda kuma yan gidanmu da sauran mutane ciki kuma ga bedroom ɗina na zauna ni da ƙawayena da mutanen arziƙi. An kawo sinasir da tsiren sannan tun jiya a ka haɗa da kunin aya suka ɗuɗɗura a gorinan suka saka sticker a fridge ma suka kwana ina ganin haka sai na kira su Ya Aina na ce su raba komai kashi uku, ɗaya namu ne da ƴan'uwan mu ɗaya kuma na yan uwan Yallaɓai ɗaya kuma ni da ƙawayena da yara tun da Baby ta ce mini yan ajin su za su zo Jidda dai na san hali ba gayya za ta yi ba.

Bayan na saka an diɓar ma su Gwaggo na ba da a ka kai musu sannan na saka Hauwa ta ɗibar ma Gwammaja suma suka aika da shi can wajen su Nene. Na saka suka ɗibar ma Yallaɓai na ce zam kira shi in yana office ne zan kira Musbahu da Adnan matan kuma na ce su ɗibar ma yaran su da mazajen su a yi komai cikin tsari. Na bangaren mu ragamar na hannun Amina na bangaren su Yallaɓai kuma Munnira ce ni dai na gama jan kunnenta kar ta yi faɗa da kowa a yi suna a tashi lafiya. Ta ce mini ba za ta yi ba amma ni na san sai ta yi mgana ni da na san halin Munnira.

Karfe biyu na rana mai kwalliya ta iso kusan ma lokaci ɗaya suka iso tare da Khaleesat wai mota ta lalace musu a hanya. Itama ta kawo mini turamin atamfa da riga tare da kayan sanyi na karɓa ina ta godiya. Swiss lece na saka cikin wanda na siya na ɗinka sannan a ka tsantsara min kyakyawan kwalliya wanda tun kafin a gama kowa ya shigo sai ya yi santin kyan da na yi kyau ma sai da a ka gama ta yi mini wani irin ɗauri mai kyau da na duba madubi na ɗauka jidda ce tsabar yadda na dawo kamar budurwa. Na yi amfani da takalmi baki mai tudu kaɗan da mayafi baƙi da jaka, Na saka ɗan kunnaye na masu kyau da tsada, ba ni da zinare ko na zobe sai da na yi hawayen takaici na tuna wanda a ka siya mini da Sadaki na, Yallaɓai ya saka na siyar da shi muka cinye kuɗin, da cewa in ya samu zai siya mini wani har yau lokacin bai yi ba ina jin ma ya manta da abin da ya faru. Ni kaina na san na yi wani irin kyau duk kuma in da na gifta Ƙamshi ke tashi, oil ne mai bala'in, wajen wata mai siyar da turaruka a faceebook na san ta Maryam kitty. Tun da na fara siyan turarenta ban taɓa saka shi ba a yi santin kamshin ba Yallaɓai ya daɗe da sanar da ni yana son ƙamshina. Har na ce in na samu kuɗi zan ce ta haɗa masa na maza daga baya da ya ɓata mini rai na fasa.
Chapter 36 · 0% Book details