Sashe 21
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"In kuma Namiji ne to sunan Alhajin ÆŠorayi za mu saka masa ko?
Ya ƙarishe mini yana dariya. Nima dariyan na yi kafin na ce" Ka yi gaskiya. Tabbas haka ne a raina."
A lokacin jawo ni jikinsa ya yi yana faÉ—in" Kar ki damu fata na ki sauka lafiya duk sunan da kike so shi za mu sanya kin ji ko?
Sai na ji daÉ—i har ina ba shi sumba.
Vibration ɗin waya ta ne ya dawo da ni daga tunanin da na faɗa. Ta na gefen in da na ke kwance ne na saka hannu na ɗauko ta sai na ga Yallaɓai ke kirana. Ban kawo komai a raina a tunanina sallama zai yi mini kamar yadda ya ke yi in bai samu zuwa ba.
"Zan taho da Daughter yanzu ina so mu yi mgana gabaÉ—aya."
Abin da ya ce minI kenan bayan mun gaisa. Sai na ce masa sai sun taho. Har muka gama wayar tunanina bai hasaso mini kan abin da ya faru ba ne sai daga baya na fara tunanin wataƙila kan haka ne amma kuma a ina ya ji? Ko wa ya faɗa masa? Watsar da tunanin na yi saboda ba ni da mai ba ni amsar su.
Sai da suka zo gidan sannan na fito daga ɗakin na saka hijabi amma duk wanda ya gani ya san ina fama da azaban laulayi duk na yi fari na lashe na kuma rame. kullum ina fama da bushewar baki da maƙogwaro. Ina ganin Gimbiya sai na tuna da faɗan da ya shiga tsakanin mu da ita shi ya sa na yi kamar ban gan ta ba kamar yadda itama na ga ta yi, sai wani cin magani take yi tana wani hura hanci.
Shima gogan ransa a ɓace na gan shi da ga gani sun yi ta ne kafin su ƙariso. Jidda ya haɗa da yaran gabaɗaya da cewa su koma falon su za mu yi mganam ita ta tattara su suka bar mana falon. Shi yana saman kujera mai zaman mutun uku ni kuma ina zaune a mai zaman mutum biyu a gefen sa ita kuma sai ta zauna kan mai zaman mutum ɗaya muna fuskatan juna ni da ita. Ai ni tun da ta yi mini wannan wulakancin na yi alƙwarin duk in da za mu haɗu in ba ta ce sannu ba ba zan tanka ta ba. Da mutumcina ba zan zauna wacce ba ta isa ta zubar mini da ƙima ba.
"Ba ku gaisa ba?
Ya faÉ—a bayan ya kore shurun namu gabaÉ—aya.
"Tsakanin ni da ita wa ya zo ya samu wani?
Na tambaye shi ina mai kallon shi da idananuwa da suka ƙanƙance.
"Ita ce "
Ya faÉ—a yana kaÉ—a kai, ni ban yi magana ba sai shi ne ya kalleta kafin ya ce" Ki gaishe ta mana."
Ta yi shuru taƙi mgana ni dai kaina na ƙasa ina wasa da gefeb hijabina da ya sani bai ɗauko mini ita ba. Ta zo har falo na tana yi mini Taƙama.
"Ba da ke nake mgana ba."
Na ji ya da ka mata tsawa.
"Ina yini."
Ta faÉ—a kamar dole. Ko da ya ke ai dolen ce ya saka ta.
"Ke kuma ki amsa tun da ta gaishe ki."
Ya faɗa muryansa a sama daga gani yau an taɓo zuciyar ƴan maza.
"Lafiya lau."
Nima na faɗa a tsume saboda ni ba gan amfanin wannan zaman ba tun da wacce ta yi laifin ba ta ji a karan kanta ta yi nadamar abin da ta yi ba.
"Hakan da kuka nuna shi ne ya ƙara tabbatar mini akwai wani abu da ya faru a tsakanin ku wanda kuka rufe ni ba ku gaya mini ba. Ban sani ba ba domin Kawu Abba ya kirani ya faɗa mini ba, sannan Maman Farko ma ta kira ni ta ce na tara ku kun samu yar hatsaniya ranar a gidan Bahijja amma cikin ku a ka rasa me faɗa mini wani abu ya faru? Me ya sa haka?
Dukkan mu muka yi shuru. Ni sai da ya faɗa sannan na gano in da ya fara samun labari. Wato Marwa ce ta sanar ma da mijinta shi kuma ya kira Yallaɓai ya faɗa masa. Sai Maman farko da ta yi masa mgana ashe ita ma mara kunyar ba ta faɗa masa ba.
"Daku fa na ke mgana?
"Me ya sa ba ku faÉ—a mini ba?
Ya faɗa yana ɗan sausaauta fushinsa saboda ya yi ƙasa da muryan sa.
"Kasan daman ni ba halina ba ne na tare ka da mganar an yi kaza an yi kaza. Ballatana matarka daman ta ce ni ce ke kai ta gaba a wajen ka."
"Wannan ba Hujja ba ne. Ke ce babba bai kamata ki same ni ki faÉ—a mini wani abu ya faru ba?
Ba na so mganar ta yi tsayi ya sa na ce" Ka yi haƙuri na yi kuskure."
"Gaskiya ban ji daÉ—i ba. A ce sama da kwanaki ban san wani abu ya faru da matana ba sai wasu ne za su kirani suna faÉ—a mini ? Kun yi mini adalci kenan?
"Ka yi haƙuri."
Na sake faÉ—a ita hajiyar tana zaune tana karkaÉ—a kafa ba ta yi mgana ba.
"Ya wuce. Amma kar a ƙara irin haka ba na so. Duk abin da zai faru da ya wuce ku biyu wasu suka sani to nima ya kamata na sani ɗin"
"In sha Allahu."
Na faÉ—a ina muskutawa domin na gaji da zama duk na takura.
"Me ya faru ne a tsakanin ku da a ka ce kun yi sa'in sa a gaban mutane? Yaushe kuka fara sa'in sa a tsakanin ku ni ban sani ba?
Tambayar gabaÉ—ayan mu ya yi mana. Amma ni ban ce komai ba ita kuma sai ta fara faÉ—in" Ai na É—auka ka san duk abin da ya faru."
"Na sani zan zo in tara ku ina tambayar ku?
Ya faɗa a ɗan fusace ganin ya harzuƙa ya sa ta fara mgana a ƙoƙarinta na ta juya mganar tun da ta fara faɗin wai na ce na yi mata mgana ta yi banza da ita. Ita ba ta ji ba ne amma shi kenan na fara faɗa ina faɗin ta ji da gangan ne.
"Sadiya"
Ya katseta da kiran sunana sai na É—ago kaina ina amsawa.
"Na'am"
"Ki yi mini bayanin abin da ya faru daga farko."
Na buÉ—e baki zan yi mgana ta tare ni da cewa" Ni ba ka yarda da ni ba sai ita kenan?
"E. Ai ita na fara sanin kafin ke. Saboda haka ita zan fara ba ma Amincina kafin na baki "
Sai ta yi shuru bayan ta koma ta haÉ—e rai tana faÉ—in.
"To ai shike nan."
Ni dai ban bi ta kanta ba na yi masa bayanin duk abin da ya faru tun daga farko. Ban ɓoye masa komai ba har mganganun da na gaya mata da wanda su Munnira suka faɗa mata duka na faɗa masa na ƙarishe da cewa" Na yi ƙoƙarin na danne zuciyata amma na kasa. Saboda na ga ta na ta nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. In su ta ce farar haihuwa ne su kuma su Jidda ɓakar haihuwa take son ta kira su? Ta fada mganar nan ba sau ɗaya ba kuma sau biyu ba. Shi ya sa na tanka mata har ta kai mu ga sa'in sa"
Sai ta taso mini tana faɗin" Ni yaushe na ce su baƙar haihuwan? Ni fa ba haka nake nufi ba. Munnira ce ta ce wai ina bakin ciki da kin samu ciki ni ko na ce me zai dame ni,? Ni da na yi farar haihuwa.."
"Shutup."
Ya katse ta bayan ya da ka mata tsawa. Sai ta yi shuru ta na wani nuƙufarci.
"Har kina sake maimaitawa?
"To ai na ga ba."
"Ki rufe mini baki na ce ko?
Ya sake mata tsawa har ya na miƙewa kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin" Ni shikenan ba za a bar ni na yi mgana ba. To da yake ita kake so ai ka bar ta ta yi mgana ni kuma da a ka tsana ina mgana kana mini tsawa."
"An hana ki É—in. Kuma ba a son ki É—in, an tsane ki, ki yi abin da za ki yi wawuya kawai "
Kamar famfio sai ta ƙara ma kukanta volume.
"Ki yi mini shuru na ce ko?
Ya sake faÉ—a a fusace dole ta kama bakinta ta koma tana haÉ—iyan zuciya.
Shima sai ya koma ya zauna yana sauke numfashi kafin ya kalleni yana faɗin" kin yi mini laifi Sadiya. Me ya sa da kika yi ta mata mgana tana miki wulaƙanci ba ki faɗa mini ba! Da tun lokacin zan faɗa mata ko ni da nake aurrn ki ba ki taɓa mini mgana na yi miki haka ba ballatana ita ? Sannan mganar tun da kika samu ciki ba kya laifi a wajena sai ki faɗa mata tun kafin ki samu ciki ke ɗin daman ba kya laifina a wajena ko za ta ɗau mataki ne? Wallahi da kin faɗa mini da na ci mata mutumci da ba ta isa ta tare ki da wata mgana ba."
"Ka yi hakuri."
"Kar ƙi kara ganinta ki ce za ki yi mata mgana. Umarni ne daga ni na ce duk in da kuka haɗu ita ce za ta fara gaishe ki "
"TabÉ—ijam"
"Ko ba za ki bi Umarnina ba ne?
Ya katse ta a fusace kamar zai kai mata duka.
"Na ji."