← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 103

Sashe 71

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya faɗa yana mai kallon fuskata. Nima shi nake kallo, na tuna ni ce nan na sha cika bakin cewa in Yallaɓai ya tashi kara aure ba zan damu ba domin ni ya gama yi mini kishiya, Gimbiya ce ke da wannan ƙuncin ba ni ba, ban tabbatar ma da kaina kishi sunan shi Kishi ba sai yau, domin sai na ji wannan ƙullutun abin da ya taɓa tsaya mini a ƙahon zuciya a daran da na samu labarin Yallaɓai ya auri Gimbiya. Irin shi ne na ji ya tokare mini zuciya. Ya yi sanadiyar rufe bakina da kassara sauran kuzarina.

"Ba ki ji komai ba Sadiya ta?

Ya faɗa yana leƙen fuskata. Kamar an ƙwato numfashina haka na ji na saki ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan na kalli Yallabai. Sai ga ni jiki a sanyaye ina mai mikar masa wayar sa, ya saka hannu ya karɓa.

"Ka yi haƙuri ban san haka maganar take ba."

Na faɗa cikin sanyin murya. Sai na ji kwarmin idanuwana suna cika da kwallah. Sai ya fara dariya yana faɗin" Me ya faru? Ni ba ki yi mini laifin ba ni haƙuri ba na ji daɗi da kika zama mace ta farko da kika fahimci ina boye miki wani abu."

"Gimbiya ma ta sani."

Na faÉ—a ina kallon shi, sai ya kalle ni cikin mamaki.
A hankali na warware mishi yadda muka yi da ita.
Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Allah Sarki Æ´an mata na. Ina son ku wallahi."
Ai ni ko jin sa ban yi ina cam na tafi duniyar tunani.
Aure. Aure fa Yallaɓai ya ce zai ƙara, in a da ina raba shi da kwana biyu ne yanzu fa sai dai kwana huɗu. Kai innalillahi.

Haka nake faɗa a ƙasan zuciyata. Gabaɗaya jikina ya yi sanyi kamar an yi mini duka.

"Da man lokaci na ke jira na same ki mu yi maganar nan. Wallahi tallahi ban da ke ko Nene da yan uwana ba su san da labarin Rabi'atu ba."

"Nima ai ban sani ba, ba ka faÉ—a mini ba sai da na gani da kaina."

Na faɗa kamar zan yi kuka sai ya rumgumo kafaɗata yana faɗin" Allah shi ne shaida na. Niyyata cikin satin nan na ke da niyyar faɗa miki, kin san ba ni da wata abokiyar shawara sama dake. Ni da ke mun kai wani matakin da ba zan iya ɓoye miki komai ba, da man na ce sai na yi magana da ke sannan zan je na yi magana da Nene."

"Uhm"

Kawai na faɗa domin na kasa magana ko na ce  ba ni da ta cewa ne kwata kwata kamar an shafe manganganun dake cikin ƙwaƙwalwata.

"Da gaske na ke yi Sadiya ta "

Ya faɗa yana wasa da yatsun hannuna guda ɗaya da ya kama ya riƙe.

"Ko da gaske ne ni na isa na hana ka ƙara aure ne? Ai kamar yadda ka yi na farko ban iya hanawa ba wannan ma sai dai na sake yin maka fatan alheri."

"Na san baki isa ki hana ba. Amma ai kin isa na yi shawara da ke ko?

"Sabo da mene?

Na faÉ—a ina kallon shi.

"Saboda ke kin zama TURKEN GIDA na. Ban isa na zartar da wani hukunci ba tare da na nemi shawaran ki ba. Duk da ba ki isa ki hana ba amma kin isa ki nuna mini abin da nake ƙoƙarin yi in mai kyau ne ko akasa sa,  Sadiya kina da wata daraja mai girma a zuciyata da na ke girmama manganganunki. Na ke kuma kambama tunanin ki a kaina. Na tabbata ke mai adalci ce mai kau da kai mai haƙuri da hangen nesa. Kamar yadda kika saba ba ni shawara da zuciya ɗaya yau ma ina da yaƙinin da zuciya daya zaki ba ni dukkan shawarwarin da na ke son samu daga gare ki"

Koda a ce daÉ—in baki ne na Maza to ni dai wallahi ya yi tasiri a kaina, har ban san ina ta mirmishi ba kaina ya yi girman da na ji ashe nima na isa a wajem mijina ban sani ba.

"Da gaske Yallaɓai na?

Na faɗa ina yi masa mirmishi duk da a ƙasan zuciyata nauyi na ke ji, amma bai hana daga can sama wata tsoka ta jin daɗi ta motsa mini ba.

"Haba. Kike tantama? Ke ce fa mafarin Yusuf, ke ce da shi a shekaranjiya da jiya har da yau. Bayan iyayena ke ce macen ta farko da zan nuna da ta yi ma rayuwata hidima. Ki sani ke ɗin ta musamman man ce a wajena. Anan ƙarƙashin nan na ke jin tarin hidimarki a gare ni "

Ya faɗa yana taɓa wajen zuciyarsa da hannuuwana da ya riƙe, sai gani kamar shashasha ina ta dariya da mirmishi.

"Na gode da Martabawa Yallaɓai."

"Nima da na gode da hidimantawa My Sady"

A tare muka kalli juna sannan muka yi mirmishi sai na faÉ—a jikinashi ya rumgumeni cikin rumfar hannayensa masu zame mini garkuwa a koda yaushe.

"Wata shawara kake buƙata daga gare ni?

Na faɗa ina kwance a saman ƙirjinsa.
Sai ya dago ni muna kallon juna kafin ya riƙe dukka hannayena guda biyu ya fara faɗin.

"Rabi'atu yar maiduguri ce amma zama ya kawo ta nan Kano. Akwai Baffanta a nan garin ƙanin mahaifinta kenan bayan rasuwar mahaifinta shi ya karbeta ta dawo hannun shi tun tana JSS3. Ga shi yanzu har tana karatu anan BUK ajin ta ɗaya."

"Ina jin ka."

Na faɗa ina kallon Yallaɓai domin ganin yadda ya natsu kamar Nene ce a gaban shi ba ni ba.

"Mun fi wattani biyu da haÉ—uwa. Kuma ni dai yanzu ina matakin na gabatar da kaina a wajen Baban nata ne."

"A ina kuka haÉ—u?

Na samu kaina da yi masa wannan tambayar
Saboda ni dai a sanina ba ruwan Yallaɓai da yan mata amma sai ga shi ya zaunar da ni yana ba ni labarin budurwa.

"A bakin BUK new site. Na je yi ma wani abokin karatun mu murna ya samu koyarwa a wajen shi ne bayan na fito na haɗu da ita tare da ƙawayenta su biyu."

"Sai ka rage musu hanya ko?

Na faɗa ina kallon shi sai ya fara dariya kafin ya ce" E. Ranar alhamis ne, daga cikin makaranta za su je gida Weekend. Sai na rage musu hanya na kai ƙawayenta gida itama na kai ta daga baya."

Sai na samu kaina da yin mirmishi kawai.

"Kuma suka yadda suka shiga motarka ba su san ka ba?

"Ni na yi ta bin su ina yi musu magiya."

Ya faɗa mini gaskiya da na ji da man ban tambaya ba. Da man bayan ni akwai wata macen da Yallaɓai zai iya yi ma magiya! Kin manta da Gimbiya? Wata zuciyar ta tunasar da ni.

"To kin ji yadda muka haÉ—u da Rabi'atu"

Sai na kalle shi, na ɗauka bayan ni Yallaɓai ba zai ji daɗin faɗin sunan wata mace ba, sai ga shi a gabana yana kiran sunan wata macen cikin shauƙi da muradi.

"A hostel take zaune kenan?

"E. Can take zaune sai bayan sati uku take zuwa gida Wekeend"

"Can kake zuwa taÉ—i kenan?

"E to wani lokacin. Amma har gidansu ina zuwa."

"Can Maidugurui?

Sai ya zaro mini ido kafin ta ya ce" Gidan Babanta dake Kano dai, Maiduguri wataƙila sai mun je ɗaurin aure."

Sai na jinjina kai na ma kasa mgana. Yallaɓai ya riga ya gama tsara komai shi da yarinyar.

"Kana son ta ne haka sosai?

Sai ya fara sosa gira. Sai kawai na yi mirmishi kafin na ce" Ko ba ka faÉ—a ba labarin zuciyarka fuskarka ta bayyana mimi.
To ita nata sonka kamar yadda kake son ta?

"Ofcourse. "

Sai muka kalli juna sai ya rage zumudin ya dan saussauta murya kafin ya ce" Na ce mata bana som auram ya wuce wata uku ta ce ta amince."

To da mam za ta ki ne, me Yallabai ya rasa?  In ba ya faɗa ba ba mai ganin sa ya ce ya kai shekaru arba'in da tara, yana nan a matashin sa, kamar ɗan shekara talatin da ɗoriya. Balle ga ƙudi ga rufin asiri ga iya gayu ga kalamai ta same shi me za ta tsaya jira ban da ta amince?

"Me kika ce?

"Me zan ce?

Na faÉ—a ina kallon shi.

"Kice koma me za ki ce"

"Ba abin da zence sai fatan alheri. Allah ya tabbatar Allah ya haÉ—e kawunan mu ya kauda da fitina."

"Amin Amin My Sady. Amma wattanin ukun ba matsala?

"Babu tun da ka shirya."

"Gida ne, kuma in ba su ƙarisa ba zan ce a gyara mata shashe ɗaya ta fara tarewa. In ya so bayan bikin in an gama gyara na ku ke da Daughter sai ku tare a lokaci ɗaya."

Sai na kalle shi kafin na ce" Kana ganin Matarka za ta amince?

"Me ya sa ba za ta amince ba? Ai ba cewa na yi ba za ku tare gabaÉ—aya ba. Kuma tun da kika amince itama za ta amince in sha Allahu."

Sai na samu kaina da cewa Allah ya sa. Ban ce ina son ganin hoton ta ba amma sai da ya nuna mini a cikin wayarsa..
Ba Yallaɓai da yake matsayin namiji ba har ni mace kyan yarinyar ya dake ni. Tabbas yar maiduguri ce fara ce tas ga gashi har gadon baya ga diri. Masha Allah hancin nan har baka, ga ta doguwa sai dai yarinya ce wannan ko za ta girmi Jidda da ƙadan ne.

"Ta yi kyau. Allah ya sanya alheri."

"Amin Amin. Itama na nuna mata hoton ki."

Ban yi magana ba sai dai ina ta kallon shi.

"Ta ce ganin ki ya fi jin ki."

Ya faÉ—a yana dariyan nishaÉ—i.

"A ina take jin labarina?

"A bakina mana. Ai ba za mu hadu mu rabu ba ta ji sunan Sadiyata a bakina ba."

Na yi zuru ina kallon Yallaɓai yana labarin budurwansa cikin nishaɗi.

"Ta ce duk yadda aka yi ina ji dake. Na ce sosai ma ko ita na faÉ—a mata in har tana so ta kama babbar fada to ta kama kafa dake domin har ni juyanj kike yi "
Chapter 71 · 0% Book details