Sashe 65
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka amsa da Amin gabaɗaya. Shi ya buɗe mini gaban mota na ƙi shiga na faɗa baya kusa da Baby. Mun tafi muka bar Kawu anan amma ya ce za su biyo kafin su wuce. Muna tafe a hanya yana ta kallona ta madubin gaban mota ni ko na yi cuɗun ciɗun da fuska bai ga fuskar ma wata mgana ba.
Haka muka isa gida ni ko jiran shi ban yi ba na yi wuce wata cikin gida. Ya biyo ni har ɗaki yana so ya yi mini magana na bar masa yarsa nan saman gado na faɗa tiolet na banko masa ƙofa ai ban fito ba sai da na ji ƙaran jan get alamin ya fita sannan na fito ina jan tsaki.
Sai da na yi wanka sannan na duba gidan. Kitchen dai ya sha kyau Baby na saka ta gyara shi ta goge da falon su. Falon Yallaɓai ko ta kan shi ban bi ba girki ma doya na ce Baby ta fre mana ta sulala mu ci da mai da yaji sai bayan azhar na duba wayata. Hauwa da Munnira sun kikkirani da Rahila sai Suwaiba.
Munnira na fara kira ba ta ɗauka ba sai na kira Hauwa. Ita ke faɗa mini Mutaƙka ya yi fata fata jiya akan abin da ya faru, ni tsabar haushi ban san lokacin da na ce.
"Ku fita hanyata ku fara aminta da Gimbiya shine faÉ—an na su."
"Wani irin magaana ne wannan? Ai ba su isa ba. Shima ai na faÉ—a masa ba zai yuyu ba sai ya ce wai shi bai ne na rabu dake ba amma na daina wulakanta Gimbiya saboda ke Ya Tafida ya ce ba ya jin daÉ—in haka."
"Kar Allah ya sa ya ji daÉ—in mana.'
Na faɗa cikin ɓacin rai, ban faɗa mata na je gida har na kwana ba amma na faɗa mun hau ramar da ba ta da ganye mun fado a jiya da daddare ni da Yallaɓai.
"Kai Gimbiya ba ta ji daÉ—i ba. Ta haÉ—a karya da gaskiya.'
"Daga shi har ita in sun fasa sun raina Ubangijin su.'
Sai da na faÉ—a sannan na rufe baki ina waige-waige ni kaÉ—ai sai da na yi dariya Hauwa ma sai da ta dara."
"Haushi take ji kuna tare da ni, ba ma ita ba har su Anty Bahijja ma. Kuma sai dai su mutu wallahi.'
Hauwa ta ce kwarai mun daÉ—e muna mgana kiran wayar Munnira ne ya katse mu. Ta ce mini Ashe ta koma tun safe,Marwa fa? Na ce mijinta ya zo É—aukanta ta je gida ta dawo.
Munnira zage-zage ta dinga yi tana faÉ—a mimi hauka hauka ta yi ma Nasir jiya ya zo yana ce mata ita ke hassada fitina tsakanin matan Yaya Tafida."
"Ai ko jiya ya ga tijara. Na fashe kamar tayagas faaa faaa. Haka nake yi ta in da na ke shiga ba ta nan nake fita ba. Ai daga karshe sai ya dawo yana bani haƙuri."
Ina dariya na ce" Duk haka suke suna da son kan su. Amma ba su da laifi abin da Yallaɓai ya faɗa musu. Za a ce ke ce ke da fitina ya ja miki kunne."
"To ai ba shi kaÉ—ai ba hadda su Anty Bahijja, a group É—in gidan su je ki gani sai abin da suka manta ba su fada mana ba, na fara ma yar da martani Mimisco ta kira ni ta ce kar na sake magama shi ya sa na yi shuru."
"Au kuma?
"Wallahi kunna data ki sha kallo."
Ba musu na yanke wayar na kunna data. Sai da na bari saƙonnin duk sun gama shigowa a group din gidan su Yallabai Iyalan Marigayi Muhammad Inuwa02. Mata ne kaɗao sai mi surukai a ciki mazan suna can na farkon.
An yi ta cin kasuwa akan mu har Yayar Gimbiya da ba ta zo ma sunan ba, tana ta mganar cewa ba za su yarda da duka ba ko su Anty Bahijja su É—au mataki ko su su É—auka da kan su.
Ita ko yar kanzagi Anty Bahijja ta ce ai Tafida tuni ya ɗauka mataki dukkanmu an ja mana kunne. Anty Maimuna ta fito ta ce ba lafin kowa ba ne sai ni Munnira ta ce ko gobe yarinya ta sake mata rashin kunya sai ta mata dukan tsiya. Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya Nasir zai ji, group ya koma faɗi in faɗa har sun jj labarin abin da ya faru. A cewar Jamila ta ce Gimbiya da bakinta tafaɗa mata ni da su Munnira taron dangin muka yi mata ita da yan uwanta Suwaiba ta yi taggin ta ce ƙarya ne tana wajen ta yi Vn wajen mimtina sha tana bayanin abin da ya faru ni ina fara ji ma haushi ya sa na kashe gabaɗaya.
An yi manganganu har Ant Zabba ta tanka ta ce in dai har gida muka je muka dake su ba mu kyauta ba.. amma ya kamata a yi bincike domim a samu sulhu. Mimisco ta tawatar ganin abin na nemen ya zama rigima ta ce kar wanda ya ƙara mgana. Ba ni da damar ma yar da martani shi ya sa na yi shuru.
Kafin ma na kashe datan sai ga kiran Mimisco na ɗauka muka gaisa sannan ta tambayeni abin da ya faru duk na zayyane mata, ta ce gaskiya suma ba su kyauta amma Munmira ma ba ta kyauta da tun farko ba ta tanka su ba. Ta yi mini faɗa sosai ta ce bai kamata ina barin ƙananun abubuwa suna shan gabana ba. Na yi gaba fa sai dai a biyo bayana. Na ji daɗin magana da ita shi ya sa duk cikin yayyen Yallaɓai Mimisco na dabam ce a wajena. Ta ce ko an buɗe gidan kar na tanka ma kowa na yi shuru kawai itama amsa ce. Nan take na yi mata alƙawarin ba zan yi magana ba ta yi mini godiya muka yi sallama.
Mun gama wayar kenan ina shirin ajiyeta bayan na kashe data Jidda ta kira ni kwana biyu ba mu gaisa.
Bayan gaisuwa da tambayan makaranta ta kira sunana.
"Umma."
"Na'am Jidda."
"Me ya faru tsakanin ki da Abba ne?
Cikin mamaki na ce" Me kika gani?
"To ya kira ni yanzu ba daɗewa yana faɗa mini ya yi miki laifi kina fushi da shi na kira ki na baki haƙuri"
"In ji baban na ki?
"E Umma. Don Allah ki yi masa haƙuri ba ki ji muryan Abba ba duk ya damu."
Sai na yi mirmishi kafin na ce" Bayan nan bai faÉ—a miki komai ba? Bai faÉ—a miki laifin da ya yi ba?
Tana dariya ta ce."Umma ba sai ya faÉ—a mini ni dai kawai ya ce kina fushi da shi na kira ki na ce ki yafe masa ki kula shi."
"To."
"Don Allah Umma."
"Na ce to ko?
Na faÉ—a a É—an hasale.
"To ai Umma na san halin ki ne yanzu sai ki fara gaba da shi, yana mgana kina yin banza da shi. Allah Abba abin tausayi ne fa Umma in dai a kan ki ne."
"Ƙaniyarki Jidda."
Na fada ina danne dariyata itama dariyan ta ke yi.
"Ke har kin san abin tausayi a kaina? Zan ci mutimcin ki fa"
"Wallahi Umma in ba ki yi masa mgana da ya ganki duk sai ya ruÉ—e"
"Sai anjuma Jidda"
Na faɗa mirmishi, jin tana yi mini shaƙiyanci.
"Umma a duba mini my Abbana don Allah."
Kawai sai na yi tsaki na kashe wayar, har ta saka ni mirmishi wai Yallabai ne da kiran Jidda yana cewa ta ba ni haƙuri, ba ma wannan ba yaran mu fa yanzu duk motsin mu suna ankare damu ji dai Jidda da na ke ganinta shuru shuru ashe tana ankare da komai. Wayar da muka yi da ita sai na ji zuciyata ya ɗan sauka
Ina cikin É—aki Marwa ta zo, ba ta wani daÉ—e ba amma ssi da na zuba mata doya ta tafin ma Kawu da shi tun da yana so amma ya ce ba za su tsaya ba akwatinta ta É—auka na raka ta har haraba na ba ma Afra 1k na ce ita 500 Abadalla ma haka tana ta mini godiya. Kawu daman a can waje ya yi parking É—in motar shi.
Yallaɓai na neman shiri da wuri ya dawo ana yin sallar mangariba ya siyo mini fura da kayan marmari ban sake masa gwiwa ba amma dai na karɓa kadahan kadahan. Lokacin na yi wanka abinci kuma daman farar shinkafa na dafa da daddaren ina da sauran miya, saboda na san muna faɗa sai na ji gayu na tsuke cikin riga da wando ina tafe mazaunena suna kaɗawa. Ai da ƙyar ya fita sallar isha'i yana dawowa ina ciki Yumna na wajen Baby ya ritsani yakulle kofa.
"Sadiya so kike yi na haukace a kan ki ko?
Ina tssye lokaci É—aya ina ninke darduman da na idar da salla a kanta na ce" Sai dai in matarka ce za ta haukata ka. Amma ni Sadiya ai ban kai wannan matsayin ba.'
Ban san ya ƙariso gabana ba sai da na ji ya ruƙumƙume ni daga tsayen yana mai faɗin" Ki yi haƙuri ki yafe mini na yi kuskuren da na zo na yi miki magana cikin fushi. Am sorry please."
Na yi banza da shi, amma dai ban yi ƙoƙarin kwace jikina ba. Ya juyo da ni muna kallon juna ya saka hannu ya zare mini hijabin jikina yana bina da wani kallo duk ban yi masa mgana ba.
"Kike cewa ba ki isa ba Sadiya ta? To wai wata kuma isar kike so na nuna miki da za ki san ni a wajena kin isa kin iss. Ke É—in isa ce kafin ma isar ta iso."