← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 103

Sashe 92

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni ban ce ba amma dai na ce ba ka yin tunani in za ka yi wani abu."

Kawai sai ya yi wani mirmishi na san in ya tashi magana ba zai faɗi mai daɗi ba ita kuma ta harzuƙa za a iya yin abu mara kyau.

"To ke kiyi haƙuri don Allah. Zuwa gobe in hankula sun kwanta cikin tsanaki sai ki nuna masa in da bai yi daidai ba sai ya gyara."

"Ba zan gyara ba."

Ya katseni a fusace na yi jage ina kallon shi sai kawai ya miƙe kamar zaki ya fara nuna Gimbiya da yatsa kafin ya ce" Ke wai me ya sa kin raina ni ne! Komai abin kishi ne a wajen ki? Rabi'atu ba ta da lafiya na je gidansu na dubata na shigo kin yi tunanin ki ce mini ya mai jiki.? Matata ce fa ke kuma y'ar uwan ki ce fa?

"Aa ni wallahi ba yar uwata ba ce. Ta tsaya iya dai matsayin matarka dai."

Ta faÉ—a har tana É—aga masa hannu sai ya yi wani slow kafin ya cigaba da faÉ—in"Ok yanzu na ma gano ki. Duk wannan ihun da kike yi cikin ne baki so ta samu ba ko?
Ta buɗe baki za ta yi mgana ya hanata ya ɗaga mata hannu yana cigaba da faɗin" Ba sai kin yi magana ba na gano ki baƙinciki ne da hassada dankare a zuciyarki. To bari ki ji na faɗa miki haihuwa yanzu Rabi'atu ta fara sai dai ki mutu wallahi"

"Haba Yallaɓai."

Na faÉ—a saboda na ga kalaman na shi sun yi tsauri amma sai ya juyo ya balla mini harara kafin ya ce" Ki yi mini shuru kema ai zan iso kan ki."
"Topha"
Na faÉ—a a zuciyata me kuma na yi?
Gimbiya ta ba ni tausayi ta jawo ma kanta cin mutumci Yallaɓai haka yake ta jifanta da manganganu wai ita kaɗai ce matarsa! Ni me ya sa ban taɓa masa ƙorafi ba sai ita daga dawowarsa ta san abubuwan da suka faru da shi yau? Ta san wani hali ya yini a ciki ba tarba ba kalamai ma su daɗi kawai ta zaunar da shi tana challanging ɗin sa a kan mganar banza! To wallahi in ya ga dama sai ya kwana a duk in da ya ga dama kuma ba wacce ta isa ta hana shi.

"Allah ya ba ka sa'a ka koma gidan su Rabi'atu a ba ku ɗaki sai ka riƙa kwana "

Gimbiya ta faɗa tana tsane hawayen baƙin ciki. Ba ita ba ni kaina wallahi na ji zafin mganganunsa haba wai kamar Yallaɓai ya fara haukacewa.
Ni ina ta tsoro ma kar su Khalipa su ta so.

"Ina ruwan ki? In ma a hotel zan É—auke ta mu je mu kwana wannan duk ba damuwarki ba ce. Matata ce."

Da na so ba zan ƙara mgana ba amma ganin lamarin ya fara lalacewa shi ya sa na sake mgana.

"Don Allah Yallaɓai ka yi haƙiru ke ma Gimbiya ki yi hakuri ku bar mganar nan. Dare ne kar ku ta shi su Khalipa."

Ita dai Gimbiyar ta yi shuru tana ta jan majinar kuka shi ko uban gayyar komawa ya yi ya zauna yana huci shi kaÉ—ai da man ina tsaye ne ban zauna ba sai na ce" Sai da safe"
"Dawo nan kema"
Ya kira ni a ɗan zafafe, ni fa ban san me na yi masa ba amma na fahimci ba mganar Gimbiya ba da man yau a fusace ya shigo ita kuma kishi ya rufe mata ido ba ta gane ba ta je ta taɓo shi.

"Na'am kana kirana ne?

Wajen zama ya nuna mini a kujeran da ke gefen shi ta zaman mutum É—aya sai na zauna ina jiran na ji ni kuma me za a sauke mini?

Gimbiya ya kallah kafin ya ce" Da kika kira Sadiya ita É—in uwa ce ita! ?
Daga ni har Gimbiya sai da muka kalli juna sannan muka dawo muna kallon shi saboda mamaki.

"Zugwai-zigwai kin É—aga waya kin kirata na ce ita din Nene ce?

Dukkan mu mun kasa mgana daga ni har ita saboda ba mu da abin cewa.

"Sadiya ke aurena ko ni nake auran ta? Ni ne shugaba a gidan nan a cikin ku ba wacce ta isa na faÉ—a muku."

"Ikon Allah"

Na iya faɗa a saman leɓena kamar an turo fa Yallaɓai.

"Kar ki ƙara mini wannan sakarci muna mgana ki je ki kira mini wata wallahi in kika ƙara ranki sai ya ɓaci na ma faɗa miki."

Ya faɗa yana nuna Gimbiya da yatsa, ni ta kalla sai na gyaɗa mata kai alamun ta ba shi haƙuri.

"Ka yi haƙuri."

Ko sauraranta bai yi ba ya juyo kaina ai ni na yi suman zaune tun da yau Yallaɓai ya ke kirana da wata ai na san kuma sai abin da ya manta.

"Ke kuma ki daina ganin ina jin mganarki ki É—auka ko wani abu na rayuwata sai kin shiga. Ba ruwan ki da tsakani da kowacce a cikin matana. Ki tsaya in da na saka ki, ni ne mijinki ba ke ce mijina da za a ce komai ya faru ki tasani kina yi mini faÉ—a kamar wani É—an ki ba. Ba na so na faÉ—a miki bana so"

"Ka yi haƙuri "

Na faÉ—a cikin sanyin murya.

"Ban yi ba."

Shima ya ma yar mini a fusace.

"Allah ya huci zuciyarka."

"Amin."

Ya faɗa a ƙufule kafin ya tashi ya shige bedroom har yana bango mana ƙofa.
Gimbiya ta kalleni kafin ta riƙe baki tana faɗin" Kin gani ko Maman Jidda? Wallahi ba ƙalau yake ba"

Miƙewa na yi tsaye kafin na ce" Lafiyar sa ƙalau. Da a ce kin ji shawara da duk ba ki jawo ma kan ki tozarci ba, nima da ba ki jawo mini wannan jan kunnen da ya yi mini ba. Don Allah Gimbiya ki daina sakani cikin rigimarki. Ba zan iya da Yallaɓai ba nima kina dai ji ya ce ni ba Nene ba ce ina yi masa shisshigi, in dai kin san ba za ki dinga haƙuri da wasu abubuwan ba nima to ki yi ma Allah ki daina saka ni a ciki."

"Ki yi hakuri."
.
Ta faɗa a sanyaye to itama ai ta gani yadda ya zauna yana ta yaɓa mana mganganu.

"Na ce miki ki riƙa kauda kan ki. Ba fa komai ne sai ka yi mgana ba. Ki bar shi ya yi ta kai wa daran mana in kin ga za ki iya jiran shi ki jira shi in ba za ki iya ba ki yi kwanciyarki. Ke in ya ga dama duk ranar girkinta ya je can ya kwana me ye na ki? Gidan shi abin da ya dama shi za mu sha, kuma Allah ai yana sama yana kallon shi cikin mu duk wacce ya danne ma haƙƙi sai Allah ya tambaye shi.
Duk tsiyar shi ba zai kwana can ba zai dawo kuma yau da gobe ba ta bar komai ba in kika yi haƙuri itama ai wata rana za ta zama ɗaya da mu. Ai mace ce haihuwa za ta fara. Kamar yadda ya ganta ya auro wata rana haka zai ga wata ya auro itama a fara gwagwarmaya da ita ba, ai Namiji ne shi a rayuwar namiji mai ya yi ne da kuma ɗauka da ajiyewa ke dai ki zura ido kawai ki daina ma tanka shi, ki nuna ma kamar ba ki san abin da yake yi ba shi da kan shi zai shiga taitayinsa."

"In sha Allahu ba zan ƙara mgana ba."

Ta faɗa tana miƙewa itama.

"Ya dai kamata gaskiya."

Ba mu ji ko ƙaran buɗe kofa ba sai ganin shi muka yi kawai a kan mu a falon, ban san ko ya ji manganganun mu ba ko kallon mu bai yi ba ashe ya manta wayarsa a saman kujeran da ya tashi ita ya ɗauka a fusace ya koma ciki ina ganin haka na kama hanyar fita ina yi ma Gimbiya sai da safe, mganganun sa ba su wani dame ni ba Gimbiya ce washegari ta ce ba ta iya barci ba a raina na ce ba za ki yi ba kam nima haka na kwana kuka a ranar da Yallaɓai ya ce ina baƙin ciki da su Khalipa. A cikin zuciyata na ce Gimbiya Welcome to the Game.

Wannan tsiyar da Gimbiya ta jawo ta aka yi ita ta ja mana Yallaɓai sati ya yi daga ni har ita yana yi mana cin mgani
ko abincin mu ba ya ci da gani har ita, sai ma bangaren shi da ya turo ma'aikata suka fara ida sa gyarawa ko gaya mana bai yi ba, ni in ranar kwana na ba yan gaisawa ba ma mgana sai dai ya yi ta aikinsa a kan system ko kuma ya yi wasannin shi da ƴa'ƴan shi, nima ko ganin haka na kama kaina ban ga abin da na yi masa na bashi haƙuri tun a falon Gimbiya ban san kuma me ya ke so ba ko so ya ke yi na kwanta masa saboda yana fushi da ni, ni ko na ce a cigaba da tafiya gabar nan ce ya san ni na fi shi kwarewa. Da na fahimci ba ya cin abincina sai na daina ma yi masa ta yi, Gimbiya ta ce itama haka ba ya mata mgana in ta yi masa mgana da kyar yake amsawa. Ita duk ta damu kamta ni fa na faɗa mata an riga an zo matakin da ɗan zaki ya riga ya girma ni Yallaɓai ai ya daina hana ni sukuni da takaicinsa tuni na ke tattara shi na watsar na kama sabgogin gabana. Balle da na dawo da sana'ar hijabai na gadan-gadan ina na gama ta lokacin shi, da man hatsiyar tariyar da bukukuwa ne suka saka na yi sanyi ganin ina so ma na taba jarin kuma ga mutane na so shi ya sa kawai na saka aka ɗinko mini da yawa aka aiko mini da shi.
Chapter 92 · 0% Book details