← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 103

Sashe 20

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ta yi magana dole fa a mayar mata da martani domin rashin kunya ce za ta yi ma mutane."

Munnira ta faɗa a fusace. Anty Zabba sai ta yi aikin hankali ta kama hannuna tana faɗin" Ta ho mu je Sadiya kin ga ba ke kaɗai ba ne. Ɓaçin rai kaɗan zai iya shafar abin da ke cikin ki. Munnira ai ta gama mgana taho mu je."
Har na bi ta, saboda raina ya ɓaci har wani duhu duhu na ke gani amma tabbas Munnira ta faɗa masu zafi shi ya sa ta kasa magana amma Gimbiya ba ta so mganar ta tsaya nan ba sai ta fara masifa har tana fizge hannunta a cikin na Naja da ke riƙe ta, tana faɗin kar ta tanka mgana ta mutu har Maman Farko sai da ta roƙe ta da kar ta ce komai a bar mganan hakanan

"Ahayye. Nanaye baƙin cikin me zan yi niSaudatu! Ai duk haihuwan da za a sake yi ma Daddy sai dai ta biyo bayan haihuwar da na yi masa. Biyu ne amma kamar da goma ne. Irin kuma haihuwar da ba a taɓa masa ba sai da ya auro ni sannan na haifa masa.'"

"Ke Saudatu me ya sa ke b a ki jin mgana ne?

Maman Farko ta faɗa a fusace tana cigaba da faɗin" A na cewa a bar mganar kina ƙara magana?

"Kyaleta Mama ba riba za ta ci ba domin kowa a nan wajen ya san ba ta da gaskiya."

In ji Suwaiba saboda kowa ran shi ya ɓaci da mganganun Gimbiya. Har na ci burki da zan juya na bata amsa Munnira ta ƙara fansana

"Wallahi ƙarya kike yi. Ai am gama yi ma Tafida farar haihuwa tun haihuwan Jidda. Kin san soyayyar a haifa ma ɗa kana tashen samartaka! Kin san girman soyayya auran saurayi da budurwa? Wallahi ko goma za ki ta haifa maza sai dai ki biyo baya amma ba dai ki zo a gaba ba. Kuma in Sadiya ta haihu ki rubuta ki ijiye sai kin gane cewa ke dai kin yi irin na ki haihuwan amma ba dai ki yi irin na Sadiya ba."

Na so na yi shuru amma sai na kasa saboda na biyu kenan ta na faɗin ta yi haihuwan da ba a taɓa yi ma Tafida ba saboda ta haifi maza ni kuma ban iya haihuwan namiji ba shi ne ban iya farar haihuwa ba.
kawai sai na juya na fizge hannuna daga na Anty Zabba na isa gaban Gimbiya ina kallonta kafin na ce.

" Sau biyu kenan ina jin kina nuna bambamci tsakanin su Khalipa da su Jidda. Ban yi miki magana a farko ba amma yau na kasa haƙuri sai na tanka. Gimbiya ni fa Yusuf kaɗai na aura kuma soyayyace ta sa na yarda da shi har ma iyayena suka aminta da shi muka zama a ƙarƙashin inuwar aure. Yau ko mata dubu zan haifa da ɗigon jinin Yusuf wallahi ni Allah ya gama mini komai Gimbiya. Ya tsamoni cikin duba ya yi mini ni'imar da ba kowa ya yi ma wa ba. Haihuwan namiji ko mace ni ban ɗauke shi a wani abu ba. Ɗaya na ɗauke shi. Mata suna da matuƙar tasiri a rayuwar mu da addininmu. Kin manta cewa mace ce ta fara karɓan addinin musulunci a mata? Kin manta da tarihin matar Firauna? Hasiya da irin gwagwarmayan da ta yi domin addinin Allah. Ko kina da labarin Allah ya gina mata gida a Aljannah? To kamar yadda Maza suke da tarihi a cikin addininmu haka ma Mata ke da wannan tarihin. Saboda haka ni in mata Allah zai ba ni ina so in ta haihuwarsu ina roƙon Allah ya shirya mini su. Ya kuma sa su yi ma addininsu hidima. Ke kuma da kike son Mazan saboda tunanin su ne ke da gidan Allah ya yi ta baki ko dubu za ki haifa wallahi tallahi ba zai tsole mini gefen ganina ba Gimbiya. Gargaɗin da zan yi miki shi ne ki daina ƙoƙarin mayar da ƴa'ƴana a baya. Suma ƴa'ƴa ne dai-dai da irin haihuwan da kike tunanin kin yi a kan su Khalipa."

Ina gama faÉ—in haka na wuce. Maman farko ta jinjina kai tana na faÉ—in" Shi kenan Sadiya kin gama mgana."
Kowa sai ya yi shuru ya yi sanyi ita ko Gimbiya sai ta fashe da kuka jin yadda har Hajiya iya da ba ta san farkon faÉ—an ba ta na salla sai da ta ce Gimbiya ce ba ta da gaskiya.

"Ko ba ta girme ki ba ai tana gaba da ke a aure."

"Balle ma wallahi Sadiya ta girme ta. Sai dai ta yi sa'ar ƙanwar ta Amina."

In ji Munnira,  Suwaiba ta karɓe da cewa" Tsaya tsaya ma ko da ma a ce ba ta girme ta a shekaru ba a gidan aure ita ce babba. Kuma bai kamata ta girmama ta ba? Ai kowa ya ji wannan abin da ya faru a san ba ki ta ki gaskiya ba Gimbiyan"

Ni dai ban tsaya ba na ce zan tafi gida. Yau ma tun safe rabon da mu yi waya da Yallaɓai. Anty Maimuna ta ba ni mamaki har da ita a masu ba ni haƙuri Anty Bahijja kuma ta rufe Gimbiya ta faɗa tana kukan munafunci. Tare da Marwa da Munnira muka fita Hauwa ta ce Muttaƙa zai zo ya ɗauke ta. Anty Zabba kuma gidan su ta ce za ta je ta kwana. Amaryan ta ma tun da suka sauka daman gidansu ta sauka bikin ma daga can ta zo.
Muna cikin adaidaita Munnira sai jaraba take yi tana ce mini wai ina yi ma Gimbiya sanyi sanyi shi ya sa ta raina ni.

"Wallahi ta ba ni mamaki ko kunya ba ta ji ba."

Marwa ta faÉ—a cikin mamaki. Munnira ta ce"To daman tana da kunyar ne! Wallah ba ta da kunya ta daÉ—e tana neman da man da za ta ci kasuwa a kan Sadiya."
"Sai me? Don Allah ku bar mganar ni wallahi raina ma ƙara ɓaci yake yi "

Na faɗa ni a ƙokarina su bar mganar amma Munnira ba ta bar ta ba sai masifa take yi tana cewa na faɗa ma Yallaɓai domin ya dauƙi mataki.
"Ni ba ruwana ba ki ji ta ce kar na kai ta gaba ba."
"Ki kaita É—in domin ta san kin isa."

Shuru na yi ban yi magana ba. Saboda ni ba halina ba ne wannan surutun, abubuwa da dama sai dai ya ji su can a bakin ƴan gidan su. Ni bar ni da mgana in na ga za a cuce ni ko magana kan lamarin da ya shafe ni amma ba ruwana da mganar kishiya. Ko kafin ma ya yi aure ko hatsiyar mu da yayyen shi ban taɓa faɗa masa sai dai in ya ji labari ya zo ya tambaye ni amma ba dai ni na kwashi jiki na je ina ce masa an yi kaza an yi kaza ba. Shi ya sa yau ɗin ma na yi shuru amma har a ƙasan raina ba zan faɗa masa ko da kuma ba zai ji labari ba amma dai ina da yaƙinin tabbas zai iya sani.

Mu mai adaidaita ya fara saukewa sannan ya wuce da Munnira. Allah ya so ni ga Marwa ina komawa gida na kwanta sai zazzaɓi ita ce na samu ta dama min kuni na sha ya zauna a cikina. Ni saboda bacin rai ko Baby ban nema ba da zamu taho. Sai kawai na ce gobe sai su dawo tare da Jidda.  Haka Yallaɓai ya zo ya same ni a kwance ya yi ta faɗan sai da ya ce ba ya son na je Anty Zuwaaira ta matsa sai an je da ni gashi nan na dawo ba ni da lafiya sai da na ce masa ba fa komai ba ne aman da na yi a can sai ɗan zazzaɓi kuma ya san ina yin zazzaɓi haka daddare sannan ya ɗan sarara da faɗan da ya fara

Paracetamol ya ba ni na sha na yi sallah na kwanta sai na ji daɗin jiki na zuwa safe kuma sai na ji ya sake ni. Marwa ta gyara minI gida ta yi mana abin kari itama da safen ta wuce Ɗorayi za ta gai da su Gwaggo. Daga can ta wuce gidan su ta kwana da safe ta wuce Rano. Iya kwanakin da Kawu ya ba ta kenan. Ni kaɗai a gida domin Yallaɓai da hantsi shima ya fita, sai can bayan la'asar dai ga shi an kawo su Jidda. Ita na samu ta yi girki ni kuma na ce ta dama mini kuni domin wanda Marwa ta dama min tas na shanye shi kuma shi kaɗai na ke samu ya na zama a cikina sai ganye haka irin su Kabeji, latas da allayahu. In a ka sanya su a cikin abinci ina samu na ci sosai. Amma wani kifi wani nama ko warin shi ba na so balle su ƙwai da sauran nau'ikan abincin da ba na so ma na ji warin su in ana dafawa. Ni warin ma maggi mai star ne kwata kwata ba na so shi ya sa na daina ma giftawa ta Kitchen ɗin na bar ma Jidda ne ban san yadda yake ciki ba, domin na daɗe ban shiga cikin sa ba.

Har a ka kwarari kwana huɗu da dawowata gida ban ji Yallaɓai ya yi mini wata mgana ba. Sai ranar jumma'a ranar ma ba a gidana yake ba yana gidan Gimbiya ne.
Yau Mubeenan Musbahu ta zo ta yinin mini ita ta yi girki da gyaran gida. Tun da ya ga ba ni da lafiya yana yawan turo ta gidana kuma ina jin daɗin haka. Sai dare Musbahu ya zo ya ɗauke ta shi ya sa na koma ɗaki na kwanta saboda na ji na fara jin sanyi sanyi. Ina cikin bargo ina shafa kasan marata cikina ya shiga wata na huɗu kuma har ya fara turowa. Ina jin ƙaunar abin da ke cikina sosai wata ƙila don irin wahalan laulayin da na ke sha ne na tuna kafin bikin Suhailat maganar da muka yi da Yallaɓai.

"Yallaɓai in na mace na haifa sunan Mama za mu saka mata."
Chapter 20 · 0% Book details