Sashe 61
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A shiga da su ciki kuma? Daga baya kenan wai an yi sadaka da bazaawara. Ai sun gama ganin ka, kana ci ma uwarsu zarafi a kan wata banza a banza.'
Na faɗa ina haki saboda ɓacin rai.
"Kar ƙi kara ce mata Banza."
"Na ce banza a banza Yusuf don Allah ka dauki mataki in ka isa."
Na faɗa ina isa gaban shi na tsaya ina riƙe kuguna.
"Da gaske banza ce tun da ba ta iya ramin kanta sai dai na wani. Kuma wallahi tallahi ba ta isa na amsa laifin da ban aikata ba. Rashin kunya ba irin wacce ƙanwarta ba ta yi mini ba shi ba a faɗa maka ba sai gulma da munafunci?
Na faÉ—a ina zare masa ido.
"Ki matsa daga gabana kafin raina ya ɓaci na yi miki abin da ba ki yi tunani ba Sadiya."
Ya É—an fara saukowa tun da ya daina É—aga murya ko saboda yara ne oho. Marwa ta ja su sun koma ciki amma har lokacin ana jiyo kukan su.
"Me zaka yi! Na ce Yusuf me za ka yi?
Na faɗa ina ƙara ɗaga murya ni fa tun da ya jawo wannan faɗan to gwara a yi shi kawai kowa ya san matsayin shi.
"Ƙina so ki ga abin da zan yi ne ?
"E. Ina so na gani. "
Sai ya wani nuna kanshi kafin ya ce" Ni kike tsarewa cikin gadara kina faÉ—in na É—au mataki akan sadiya?
"E sai me? Tsoron me zan ji? Ƙarshen mataki kenan ka ce ka sake ni ko Yusuf? To ai ba ƙarewar rayuwata ba ce ta zo in na rabu dakai ba sai me.'
Kawai sai ya tsaya yana kallona nima ko ina kallon shi ido cikin ido.
"Yau yanzu ka ce na fice maka a gida zan fita. Tun da daman ka ce ba gidan Ubana ba ne."
"To ki tafin ma who stop you? Na hana ki tafiya? The door is open Sadiya. A sauka lafiya."
Ya faɗa yana nuna mini ƙofar falo. Na razana da kalamansa amma ina zuciyata ta ƙekashi ban nuna masa na razana ba, kawai sai na yi mirmishi kafin na ce" Da a ce yau Sulaiman Yashe bai da gida da na sha wulaƙanci."
 Ba ni da kuɗi a jikina daga ni sai hijabin salla na amma ina ganin in na koma ciki zai ga kamar na gaza ne. Sai kawai na wuce har na isa kofa falon sai na juya ina kallonsa dafe da kai a kausshe na ce.
"Ni Sadiya ni yau Yusuf ka kora a gidan ka ko?
"Kin ce za ki tafi kina tunanin zan tsayar da ke ne? Ki sauka lafiya na ce Halimaaa.!
Ya ja sunan shima a kausaahe yana kallona ina kallon shi. Idanuwanshi sun kala nima nawa ya kala ya yi jajir sai kawai na buÉ—e kofar falon na fice ina jin Marwa ta biyo ni tana Umma Umma.
Sai a lokacin na tuna da ita a fusace na waiga ina faÉ—in" Ki dauki mayafinki mu bar masa gidan shi Marwa."
"Umma..amm"
"Wallahi zan mare ki za ki taho mu tafi ne ko na yi tafiyata."
"Zan zo."
Ta fada tana zakuÉ—a goyon ta dake bayanta har ta fara hawaye.
Baby ta fito ita da Yumna ina jin Yallabai ya rike su yana mgana da su kasa kasa.
Marwa ta dauko mayafi ta fito na ji ta tsaya tana mgana da Yallaɓai a fusace na ce" Wai ke ubanki ne da za ki tsaya kina masa mgana?
Ki jira har sai ya kai ga haÉ—a ki da jami'an tsaro sannan sai ki bar masa gidan sa."
Na ga ya buɗe kofar falon ya fito Yumna na hannun shi tana ganina ta fara Uma tana miƙan hannuna na juya zan fita Marwa dake bayana ta ce" Umma ko Yumna ba za ki tsaya ki karba ba!
"Ba da ita na zo ba. Saboda haka ba da ita zan koma ba."
Baby ta rigo tana Umma Umma cikin kuka na tsayar da ita da hannu ina faɗin" Kar ma ki ƙariso ki koma nan ne gidan Ubanki nima gidan nawa Uban zan koma ya tattaraku ya kai ma Matar so ta haɗa da farar haihuwa duk ta riƙe "
"Sadiya."
Ya kira ni a tsawa ce, ko kallon shi ban yi ba na fice daga falon ina jin kukan Baby da yadda Yumna ta yanka ihu. Ni kaina duk dauriyata sai da na ji hawaye sun kece mini. Wani abu ya tsaya mini kahon zuciya, wai ni ce yau Yallabai ya kora daga gidan shi. Lalle duniya juyi juyi na gaba ya koma baya.
*Janafty**TKBB3N15*
Lokacin da na fito daga gida na san ba ni da kuÉ—i a tare da ni amma hankalina bai tashi ba
sai da muka kai titi. Sannan na fahimci daga ni sai kayan jikina da hijabi na fito. Takalmin kafata na silafas ɗin cikin gida ne, tsabar a yanayin da na fito ba mai daɗi ba ne. Marwa na kalla da ke biye da ni, ga Afra sai ƙananun kuka take yi tana faman jijjigata.
"Marwa kin fito da ƙudi?
Na tambaya ina jan majina. Saboda tun fitowarmu har bakin titi hawayena bai tsagaita ba.
"E na ɗauko ƙaramar jaka ta"
Ta faÉ—a tana nuna mini jakar sai na sake jan hanci irin na masu kukan nan, mun É—an jima kafin mu samu Adaidaita muka shiga na ce ÆŠorayi zai kai mu.
Muna tafe shuru sai kukan Afra ni dai ina ta goge hawaye lokaci bayan lokaci ina jin nono na yana zuba kenan har yanzu Yumna ba ta daina kuka ba. Sai na ji tausayinta kamar in koma in É—aukota amma kuma gwara da na barta shima ya ji in da daÉ—i.
"Umma."
Marwa ta kira sunana tana kallona, nima da rinanun idanuwana na kalleta.
"Me ya faru?
Ganin ta ƙura mini ido amma ta kasa mgana.
"Umma me ya sa kika taho?
Da kin tsaya kun fahimci juna da Kawu "
Wata uwar harara na jefa mata sai ta yi saurin kama bakinta ta yi shuru.
"Kika sake yi mini maganar shi zan kwasa miki mari Marwa."
Na faÉ—a ina huci ni kaÉ—ai har ya yi mini wannan tozarcin kuma take tunanin na zauna mu fahimci juna? Mutumin da ya ce na bar masa gida ai ya gama magana.
"Ke ko a ranki ba ki ji haushin tozarcin da ya yi mini ba. Amma kina maganar wai da ban taho ba na zauna mu fahimci juna. Tun da ke a yanayin da kika gan shi kin ga alama yana buƙatar hakan."
"Ki yi haƙuri Umma "
Ta faɗa a sanyaye amma ni sai na ji kamar ana hura ma ɓaçin raina wuta ma na cigaba da faɗa ta in da nake shiga ba ta nan nake fita ba, saboda ni gani nake yi goyon bayan Yallaɓai take yi ni kuma tana ganin laifina domin na bar masa gidan sa kamar yadda ya buƙata.
"Umma da kin taho da ko Yumna ne?
"Ba zan taho da ita ba É—in. Lokacin da ya auro ni ai ba da ita Alhajinmu ya haÉ—o masa ba. Su zauna gidan ubansu nima gidan nawa uban za koma."
"Umma tana ta kuka fa"
"Ke zan ci ubanki fa Marwa in ba ki ƙyale ni da waɗanan mganganun naki ba. Kina ƙara tunzarani."
"Allah Ya ba ki haƙuri"
Ta faÉ—a tana sunkuyar da kai kamar munafukar tsabar yadda ta ba ni haushi kamar na kai mata duka.
"Namiji ya yi maka irin wannan wulakancin kuma don ba ka da zuciya sai ka cigaba da zama? To ko ke Kawu ya yi ma haka ni uwarki na ba ki Umarnin ki baro mishi gidan shi ki dawo gida domin ya san ubanki na da gida ba a daji ya auro ki ba."
Ba ita kaÉ—ai har mai Adaidaitan sai da ya juyo yana kallona na haÉ—e rai ina harare harare.
"Hajiya a dai yi haƙuri. Rayuwar auran yanzu duk ɗan hakuri ne."
Hararan bayan shi na yi, domin ni yanzu duk wani namiji na gama sallama shi wallahi. Duka halin su ɗaya ba su da adalci sannan butulai ne. In za ka yanki naman jikinka kana ba su suna ci wata rana sai sun nuna ma duniya kai ne mara amfani a wajen su. Ni yau Yallaɓai ya kalla ido cikin ido ya ce ina da mugun nufi a kan matarsa wai har yana faɗin an targaɗa masa mata a sanadina. Ai na ɗauka yadda ya zo yana cika yana batsewa zai rama mata ne, sai wataƙila ya ji huce daga raɗaɗin taba matar so da aka yi. Ban ga laifin su ba duk mganganun da suka shirya masa in har ya yi amfani da hankalin shi da tunanin shi bai kamata ya fara da haka ba, da sai ya fara yin bincike kafin ya zartar da wata mgana.
Har muka sauka a Dorayi ni kadai na ke cika ina batsewa ina karkaɗa kafa. A bakin titi muka sauka Marwa ta biya shi kuɗin shi da taka da kafarmu muka ta ka zuwa gida. Lokacin ana ta kiraye kirayen sallar isha'i a wasu masallatan anguwan. Ai ban ji wani kukan baƙin ciki ya taho mini ba sai da na ji kafafuwana sun taka zauren gidanmu. Bayan shekaru ashirin da wani abu yau Yallaɓai ya bar mini tarihi. Tarihin ma mai nauyin da na ke jin sa har a cikin zuciyata.
Ni ce a gaba Marwa na bin bayana. Ba wutar nepa amma akwai hasken tocila a tsakar gida sai da muka ƙariso tsakar gida sannan na ga Alhajinmu duke yana alwala. Gwaggo ce ke tsaye tana haskamai da fitila. Ni na yi sallama amma muryata ta shaƙe da farko, sai da na sake yi kamar a tare ni da Marwa.
Gwaggo ta amsa lokaci É—aya ta nai mai hasko fitila cikin mamaki.
"Sadiya.';
Gwaggo ta faÉ—a cikin mamaki da har ya bayyana a muryanta
Alhajinmu kuma sai da ya idar da alwala sannan ya miƙe yana mai kiran sunana.
"Dubu"
Kamar yana tantama É—in ce ko ba ni É—in ba ce.
"Na'am Alhaji."