Sashe 54
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ya faÉ—a na kalleta can gefen Baby ta yi zuru tana kallona kamar tana jin abin da na ke faÉ—i, sai na hau dariya ita kuma ganin babanta yasa ta mike da gudu tana faÉ—in" Aba Aba."
Da yake ta fara mgana tana kiran Aba Uma, Ya Jido da Baby ita dai na yi na yi amma Yumna bakin ta ya saba da Baby ba ta kiran ta Yaya.
ÆŠagata sama ya yi yana faÉ—in" My chubby Daugther."
Saboda har yanzu Yumna da kibanta.
Tana ganin ta a hannun babanta sai ta fara zillo tana kamo habarsa, ita a dole sai ya yi mata wasan da ya saba mata. Ɗaga ta sama ya yi ya dawo da ita haka ya riƙa yi mata sai ka ji ta fara bangala dariya. Yumna daman ai yar son mugun wasa ne ko jiya sai da na cauleta da bulala Baby kuma ta ci dundu saboda sun ɓata mini falo, wai da sunan wasa, bai zauna ba sai da ya ga ta kusa siƙewa saboda dariya sannan ya zauna ya zaro chaculate a aljihun wandon jikinsa ya ba ta ɗaya, ɗaya ya ba ma Baby ɗayan kuma ya ba ma Jidda amma ni ina zaune bai ba ni ba.
"Ina nawa abin daɗin Yallaɓai?
"Kin yi girma da yawa abin yara ne."
"Lalle na ga son kai."
Na faÉ—a ina girgiza kaina kai tsaye ya ce mini nima na so kaina bai hana ni ba. Na ce ya ci bashi ne wallahi zan rama ya ce sai dai na rame.
Kiran sunan Jidda ya yi ganin ta yi shuru tana É—agowa ya gane ta yi kuka.
"Jidda me ya faru? Kukan kewan gida kike yi?
Sai ta gyaÉ—a kanta da hannuna ya nuna mata kusa dashi yana faÉ—in" Taho nan Mamana."
Sumu sumu ta tashi ta ƙarisa kusa da shi ta zauna Yumna na kan jikinsa ya buɗe mata chaculte ɗin ta fara sha duk ta yi dama dama da shi a bakinta.
"Kar ki damu kin ji ko? Zariya ai gida ce ba wata matsala ki dai ki ma yar da hankalinki a wajen karatu. Make us proud Jiddan Abban ta."
Sai ta gyaÉ—a mai kafin ta ce" In Allahu Abba."
Kanta ya shafa kafin ya ce" Allah ya yi miki albarka. Allah ya ba ki sa'a a dukkan karatun ki."
Ni da shi da ita muka amsa da Amin sai ya cigaba da ce mata in ta ji ganin gida kawai ta hayo mota ta taho, in kuma ba dama ta kira shi a waya shi sai ya je ya ganta. Sannan ga Uncle É—in ta Hamza ga Abban ta Tariq. Duk wandr ta ke son gani ko take bukatar wani in ta yi musu mgana za su yi mata ta ce to Abba.
Ina daga gefe na ce" Tariq ai ya yi nisa Ya Hamza dai da suke kusa. Da na kira shi ina fada masa ga Jiddan nan za ta zo makaramta a kular mana da ita. Kañiyarki Dubu ya ce mini wai ni ce na ke masa kashedin ya kula da Jidda?
Na ƙarishe faɗa ina dariya. Yallabai ya ce shima sun yi waya kusan abin da ya ce mishi shima haka ya ce masa amma shi bai zage shi ba, amma dai ya ce masa daga shi har ni kar mu ƙara kiran shi a kan Jidda tun da mu ba mu da kara.
"Kai Ya Hamza ba dama."
Na faÉ—a ina dariya. Yallabai na taya ni dariyan
Ina maaganar ko Weekend bayan sati ta ji kewan mutane sai ta je ta yi musu acan.
"Bai yi nisa ba?
"Ba wani nisa. Ina samaru ina pizzet?
Sai ya jinjina kai kafin ya ce" Ya yi nisa mana. Karatu Jidda za ta yi so in dai ba hutu suka samu ba ba zan so ta rika barin cikim makaranta ba."
Sai na yi shuru kawai ina kallon Yallaɓai da mamaki ba ya so ta je gidan Yayan nawa ne me ya ke nufi da maganarsa?
"Akwai wata ƙawar Daughter da suka yi karatu tare a BUK. Tana auren wani H.O.D na department ɗin Computer Science kuma acikin Abu samaru suke zaune. So Daughter ta ce ta yi mata mgana nake ga zai fi in ta ji kewan gida ta je wajenta tun da duk cikin makarantar ne."
"Ba shakka."
Na faɗa ina kallon Yallaɓai yadda ya dage yana bayani.
"Ai kin ga ba za ki haÉ—a cikin makaranta da wajen makaranta ba ko?
"Ba zan haÉ—a ba. Amma ai ba garin za ta bari ba, duka duka mintina nawa ne tsakanin makarantar da Gidan Ya Hamza? Kenan kana so ka ce Æ´a ta tana karatu a garin da Yayana ke zaune kenan ba za ta je ba ko? Sai gidan wata bare ka amince ta je kenan?
Na faɗa ina yi masa wani kallo, kallona ya yi kamar zai yi magana kawai sai ya ja tsaki ya kauda kai yana gyara ma Yumna bakin ta. Na ji zafin tsakin da ya yi mini, amma ban nuna ba sai na yi shuru ban ƙara mgana ba a ƙasan zuciyata na ce na ga mai hana ta zuwa gidan Yayana. Ko shi Yallaban bai isa ba ballanta wata matarsa.
Gajiya na yi da zaman na ga sai magana yake yi da yayan sa. Sai kawai na mike na miƙa hannu na ƙarɓi Yumna ina kallon Jidda da Baby kafin na ce" Ku kwanta da wuri kun san muna da tafiya gobe"
"Ina za ku je?
Yallaɓai ya tare ni lokaci ɗaya yana mai kallona.
"Za mu yi ma Ya Jidda Rakiya makaranta ne Abba.".
Baby ta famshe ni, ga mamakina kawai sai na ji Yallaɓai na faɗin" Ke da wa kenan?
"Ni da Umma da Yumna"
Na juya zan bar falon saboda nu na gaji da wannan shan ƙamshin na Yallaɓai kawai sai na ji yana faɗin" Ke dai da su Khalipa. Ni Umman ki ba ta faɗa mini za ta je ba. Tare da Daughter na shirya ita da ta ce mini za ta je."
Kan uba.!
Na faɗa a fatar bakina, na juyo ina son kallon fuskar Yallaɓai amma ya ƙi bari mu haɗa ido.
"To Umma fa Abba?
Jidda ta tambaya cikin Æ´ar damuwa.
"Ba ta ce za ta je ba an riga ta."
Haka ya faɗa ko a jikin shi, saboda bakin ciki ya sa na juya kawai na shige ta kitchen zuwa ɗakin barcin mu. Ni Yallaɓai ke nuna ma iyakata akan y'ar da na haifa, wai ni ina uwar Jidda yana faɗa ma yayan shi cewa ban tambaya da wuri ba an rigani. To in sai na tambaya sai dai kar na je in har ya ga bam chanchanta ba, to ya je da wacce ya ke ganin ta cancanta. Na kasa sukuni maganar Yallaɓai ya tafasa mini zuciya shi ya sa da ya shigo mini sallama zai tafi ina saka ma Yumna Pampers lokacin da ya ce mini zai tafi sai da safe ko amsa shi ban yi ba shima ya san tsiyar da ya yi sai bai damu da ya tsaya ba ya fice na raka shi da uwar harara.
Ni fa akan iyakata da Yallaɓai ke nuna mini akan matarsa haƙurina ya kusa ƙarewa. Ni ina yi mata kara amma ni ba ta yi mini kuma yana gani bai taɓa magana ba, sai a kaina ne sai ya riƙa cin kasuwarsa yadda ya ga dama to bai isa ba. Kwana na yi da takaicin Yallaɓai tun asuba da muka tashi ba mu kwanta ba saboda tafiyar Jidda. Ban shirya ba mutumin da ya ce wata ta rigani ai in na shirya sai ya tozartani a gabanta shi ya sa sai na kama kaina amma fa bai ci bulus ba wallahi. Ƙarfe tara da wani abu suka shigo gidana shi da Gimbiya da su Khalipa da suka sha gayu, Gimbiya ce ta ba ni mamaki cikinta fa ina jin ya kusa shiga wata na takwas amma ita ya zaɓe ta taje tun da ita yake so, ni kuma banza a banza ba zan je ba. Ko daga ganin yanayin dressing ɗin da ta yi na san ta shirya ma tafiyar. Ta ci wani leshi doguwar riga ta ɗora ɗauri ta zubo kitson ta na baya da ta yi, fuska ta sha kwalliya har da jan baki mayafi a saman kafaɗa tana wani cin cimghm ita yar iska. Ban ji haushin ta ba kowa ya jawo mini wannan renin ba sai Yallaɓai shi ya sa ni ko kallo bai ishe ni ba.
Har da abinci na ga sun zo da shi, shi ma shadda ya saka mai kalan sararim samaniya shi da su Khalipa suka yi anko. Yallaɓai har da babban riga an ci uban gayu sai na fahimci kawai ya fake da guzuma ne zai harbi karsara. Amma wannan tafiyar ba ta Jidda ba ne ta su ce shi da matarsa ne. Saboda ma ta ƙure ni tana ganina ban shirya ba sai da take ce mini.
"Madam ya na ga ba ki shirya ba? Ko ba za ki je ba ne?
"Ba zan je ba, haba mun yi yawa ga ki? Ke ma ai uwar Jidda ce in kika rakata kamar ni ce na rakata duk É—aya ne.'
Yallaɓai na wajen na yarfa musu magana shi da ita. Ni zai yi ma tozarci, shi ya sa ko gaishe shi ban yi, shima bai yi mini magana ba kamar da man can yana jin haushina.
Shi da ya fiffita da kayan suka loda a booth wasu ma sai da aka sanya su a baya. Baby na ta murna, Yumna ganin haka sai ta fara kuka na saka zani na goya ta domin ba na son ma ta fara yi mini rigima. Ban yi fushi ba haraba na yi musu rakiya Amarya an kame a gaban mota yaran na baya Jidda da ba ta shiga ba ta rumgumeni sai kuka nima har ta sakani hawaye duk dauriyana sai da na yi kuka.
"Ki yi hakuri Jidda kin ji? Karatu ne za ki je, za mu rika mgana ta waya ba matsala."
"Umma"