← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 103

Sashe 59

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni dai ban tashi ba Ashe da Hadiza suka mike suka mara mata baya Suwaiba na zuga su da tabbas filin naku ne. Sai kawai a ka bar musu filin Maryama ta saki baki ita da su Gimbiya. Ita Gimbiyar ba ta yi magana ba sai ita Maryam É—in ta ce"Miye haka? Ai ko fili na Anty Gimbiya ne. Domin ita ce Uwargida ita ce Amarya."

"Ina kika baro Uwargida Sadiya? Kirarinta ta Yallaɓai. Ta zama Tafida Tafida ya zama ita."
Munnira tafaÉ—a cikin sigan wasa.

Sai kawai  Maryama ta yi ja tsaki kafin ta ce" In ana babbakan giwa wake ta kiyashi? Uwargidan banza da wofi. Ai ko Amarya ita ke da Gida. Ita ta yi farar haihuwa zaranta maza har guda uku ta haifa. Kin ga ita ce gidan ma gabaɗaya."

"Ai kuma ba a nan take ba ai an take bodari ta kai."

Ashe ta mayar mata da martani Hadiza ta karɓa da cewa" Ko goma Amarya za ta zo ta haifa sai sun jira domin za su kira wasu yaya da Anty suma za a kira su yanzu kafin baya."

Tun muna ganin abin cikin wasa har aka koma jefa ma juna mganganu cikin zafi. Sai na mike ina yi ma Munnira magana akan ta yi shuru.

"In yi shuru! Daga magana na ga yarinyar nan za ta yi mini rashin kunya. Ba ta sanni ba ne ko?

"Da aurena da yayana ki kirani yarinya dan sake tunani dai baiwar Allah."
Maryama ta faÉ—a har tana tafawa hannuwa Gimbiyar na yi mata magana ta fara masifa tana faÉ—in" Ina ruwan su damu daga saka waka sai su shigo suna neman gaya mana mgana! Wa ke tsoron su?

"Na ce dai ki yi shuru ko?

Ta tsawarta mata.

"To abun na su ne kamar da gayya Anty Gimbiya."

In ji Halima ni wallahi ban ma ganta ba sai yanzu ina tunanin ko yanzu ta zo, ko kuma ta zo da safe ta je gida ta dawo.

"E mana da gayya ne. Tawagan uwargida ne ta bakin su, to wallahi mata ba ta isa ta watsa mana taro ba sai dai mu watse ta"

"Ke ai kin yi kaÉ—an ki watse mu Maryama sai dai ke mu watse ki wallahi. "

Ashe ta shige tsakanin Munnira da Maryama tana faÉ—in haka.

"Anty Munnira bar mini wannan faÉ—an koma gefe ki yi kallo"

Ta matsar da Munnira gefe tana nuna Maryama da yatsa kafin ta ce" Maryama karyan iskanci kike yi. Ni ce nan daidai da kugun ki wallahi "

Kawai sai ta saka hannu ta kabar da hannun Ashe tana faɗin" Ke Ashe kin sanni na san ki. Faɗan nan ba naki ba ne amma tun da kin shiga saboda yayarki Hauwa na ƙawar matar can mu zuba da ni da ke shege ka fasa."
Ta faÉ—a tana shan gaban Ashe har tana ture ta baya. Abu kamar wasa wasa ashe na gaske ne ni ina gefe rike da Yumna ina ta ma Munnira mganar su bari domin har da ita maryama na magana tana ma yar mata ita da Ashe har da Halima. Hauwa ma da wasu yan Rano suka je suna jan Ashe amma ta ce tun da rigima Maryama take so to ta tare shi ta same shi a wajen ta.

Gimbiya ma da Æ´an'uwanta suna ta yi ma Maryam É—in magana amma ba su ji ba.
Irin su Halima yan kan zagi suna faÉ—in daman da gayya ne.
Ga shi ba wasu manya Anty Bahijja ta tafi Anty Maimuna daman ba ta zo ba. Naja ce ta shiga tsakiyar su ta raba domin kaÉ—an ya rage afara kai ma juna duka.

"Miye haka? Daga suna na farinciki sai kuma ku ma yar mana da taro na tsiya.?
Ta faÉ—a cikin bacin rai kafin ta kalli Munnira tana faÉ—in" Anty Munni wannan ba girman ki ba ne don Allah ki ja tawagarki ku koma gefe domin a samu zaman lafiya."
Munnira kuma ta ce sun yi kaÉ—an daga abin arziki sai a nemi a ce sune suka zo da fitina.
Karaf wata ƙawar Gimbiya ta ce" Kune mana. Ina ruwan ki da waƙar da aka saka na uwargida ko na Amarya. Maganar gaskiya ku ne ba kwa son zaman lafiya. Ko kuma daman domin ku lalata mana suna kuka zo."

Munnira ta yi shewa ta dire da cewa an lalata su yi wani abun mana. Suwaiba na yi ma magana ita na samu ta jawo hannun Munnira amma sai Maryama ta ja tsiyar da cewa" Abin da ya kawo su kenan mana. Ga munafukar can ita ce ta turo su ita kuma ta koma gefe ta bakam kamar ba ta san me ke faruwa ba. Anty Gimbiya ki faɗa ma Kishiyarki ta ja tawagarta ta bar gidan nan kafin raina ya ɓaci a yi ɓaattaciya"

Maganar ta ba ni mamaki, sai kallo ya koma kaina duk sai na ji na muzanta. Naja ta zo gabana tana faÉ—in" Don Allah Anty Sadiya ki yi musu mgana su daina."
"Na yi musu magana mana Naja ko ba ki gani ba ne? Ni zan ce su zo suna ne su yi rigima da wata? Ku yi mini adalci mana"

"Ba wani adalci, ke ce munafukar da man tun da kika zo kika ga abubuwa sun tafi daidai kishin ki ya motsa ba haka aka so wai ƙanin miji yafi miji kyau."

Maryama ta faɗa tana wani girgiza jiki, sannan ta nuna Munnira da su Hauwa tana faɗin" Saboda baƙinciki sai ki ka yi amfani da waɗanan yan koren naki domin su wargazamana taro. To daga ke har su ba ku isa ba. Sai dai mu mu wargazaku mu kore ku tun da ba zaman lafiya ya kawo ku ba."

Baki na saki ina kallonta kafin in nuna kaina ina faÉ—in" Da ni kike?

"Akwai wata munnafukar ce bayan ke. Kin ga Anty Gimbiya na ta farar haihuwa. Bakin cikin ki ya kasa boyuwa sai da kika bayyana. To sai dai ki mutu aamma gida ya zama namu haka ma Yaya Tafidan shima namu ne sai mun ga dama mu ba da aron shi."

Maryama ta ba ni amsa ba tsoro ko tunanin wani. Kafafuwata suka fara rawa saboda ɓacin rai har ni na yi lalacewan da ƙanwar Gimbiya za ta ci zarafina. Yarinyar da ko Amina ta girme meta. Marwa ke rike ni tana cewa na yi haƙuri kar na tanka Suwaiba kuma tana yi ma Gimbiya mgana ta ja ma ƙanwarta kunne manganganunta suna tsauri da yawa.

"Me zan ce Anty Suwaiba? Ni ba zan hana ta ba domin duk abin da ta faÉ—a gsskiya. Taro na suka zo su watsa kuma sun ji daÉ—i.'

Kawai sai ta fashe da kuka munafunci, Munnira kuma ta fashe kawai sai ta dira kan ƙanwar Gimbiya ta shaƙo tana faɗin karya take yi, ai sune ma za su ce kishi ne ke damun yayarta domin duk wani abun da ta yi a wannan taron Sadiya ta kwaikwaya mu ba mu ce tana baƙin ciki ba sai mu ne za ki ce muna bakin ciki? To mun watse taron in ta isa sai ta yi wani abu ko ta ɗau mataki.
Ni ban san me ta buÉ—e baki ta faÉ—a ba, sai ji kawai na yi kaya kaya an fara kai duka Munnira ta fara kai ma Maryama Mari, ita kuma ta rama kawai sai suka fara dambe na ruÉ—e ina kiran sunan Munnira.

"Haba Munnira ba girman ki ba ne faÉ—a da wannan yarinyar."

Hauwa ta fada har da ni a masu rabo Yumna wajen Marwa na bar ta,ƴan'uwansu na Rano suna ta faɗa suka ce ga mota can ta dawo ɗaukan su za su wuce ba za su iya da masifa ba, da man yau za su koma, ita kuma Hadiza ganin ana faɗa da yayarta sai ta shiga suka yi ma Maryanma taron dangi suka kaita kasa. Gimbiya da Naja ganin haka suka shiga tsakani, wajen ƙokarin raba su Munnira idanuwanta ya rufe ta ture Gimbiya sai da ta faɗi gefe kusa da kujera hannunta ya bugu sai da ta yi ƙara. Kukanta ne ma ya raba faɗan sai kowa ya koma kanta Naja ta ɗaga ta irin kukan da Gimbiya ke yi ko dukanta aka yi sai kuka.

"Innalillahi shike nan sun karya ta burin su ya cika."

In ji wata cikin kawayen Gimbiyar.

"A kira Yaya Tafida mana shi sai ya zo ya ganin ma idanuwansa matarsa da Tawaganta za su nakasa masa mata."

In ji Halima, ni gabaÉ—aya kaina ya kulle ma, amma sai da na yi na Munnira masifa.

"Da wannan yarinyar ne zaki zo kina faÉ—a Munnira! Gaskiya wannan rashin sanin kimar kai ne "

Har ga Allah in na san abin da zai faru kenan da ban zo ba. Na ce su tattara mu tafi na je da niyyar na ba ma Gimbiya haƙuri ta juyar mini da kai tana faɗin" burin ki ya cika kin samu abin da kike so. Amma ki sani wallahi ba zan bar maganar nan haka ba."
Sai na ga ma tsayawa magana kamar ɓata bakina zan yi kawai sai na wuce. Har Ashe da Halima sai da na yi ma faɗa. Muka rankayo gabaɗaya zuwa waje muna fitowa Salisu na sauke Baby sai na ce kawai su juya. Motar na ce Munnira da Hadiza su shiga ya kai su gida ni kuma na ɗauko Hauwa da Ashe, tun da tace can za ta kwana sai Marwa da nima a gidana ta ce za ta kwana.
Suwaiba na cikin gidan mun bar,ta tana ban haƙuri.

"Munnira ta goga mini baƙin fanti a dangin Yallabai. Yanzu ko rantsuwa na yi ba za a yarda ba ni na saka Munnira dambe da ƙanwar Gimbiya ba "

Na faɗa cikin damuwa. Ni na san abin da na ke hange da man yaya lafiyan kura ballantana ta yi zawo. An ce ina baƙin ciki saboda ban haifi namiji ba kalaman sun yi mini dafi a zuciyata.

"Gaskiya ba ta kyauta ba. Haba ke kuma Ashe wallahi sai na faÉ—a ma Mama. Yanzu Sadiya kuka bar ma abin mgana."
Chapter 59 · 0% Book details