Sashe 83
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gaskiyan magana ba ruwanta ba ta da hayaniya ga kunya. Hatta su Munnira sai da suka yabe ta ga girmama na gaba da ita. Su Suwaiba da su Jamila duk sun zo mini amma ban ga su Anty Bahijja ba Mimisco ta zo ta ga waje ta saka albarka. Maƙotana na can anguwan da na shiga na yi musu sallama suma sun zo mini ganin gida sun saka albarka. Ga wargajejen fili, ga motata, ga na Gimbiya ga na Yallaɓai amma ko rabi ba a cika ba sannan ga maigadi, na yi hoton shashena na tura group ɗin gidanmu su Ya Hamza suka ga gaggani, suka saka albarka Amina na ta santi ta ce wallahi shashema duk ya fi kyau haka su Munnira suka ce, har fentina ya fi kyau sannan Yallaɓai ya siya mana manyan palasma guda biyu ni ɗaya Gimbiya ɗaya. Sai na yi amfani da na tsohon na falona a falon yara na tsohon faalon Yallaɓai kuma na saka shi a falona na yanzun sabon kuma na saka shi a sabon falon Yallaɓai.
Sai na raba abun falon farko na Yallaɓai ne na biyu kuma nawa na ukun na yara. Bedroon na farko na nawa ni da Yallaɓai na biyu kuma na yara sauran kuma sai na bar shi a na baki. Sannan kitchen ɗina na nan wargajaje har fridge dina da frizer anan na saka su disspanser ne kawai na saka a falon Yallaɓai.
A satin kaf ban samu fita ba ana ta leƙo mini Allah ya sanya alheri, Baby da Yumna kamar an saka su a aljannah. Sun haɗe gida ɗaya da su Khalipa in sun dawo makaranta haka za su yi ta wasa a haraba.
Rabi'atu kuma in dai tana gidan ba ta je makaranta ba tana tare da yaran
Ni da ita zaman mu lafiya. Amma Gimbiya ta ware kanta gefe, ni da man ba ta yi da ni ballatana Rabi'atu yar baya baya. Ban san tsakanin ta da Yallaɓai ba tun da ba faɗa mini abin da ke faruwa a tsakaninsa yake yi ba.
Ba ni na fara fita ba sai da aka shiga satin bikin Datti sannan muka fara zaryan zuwa ÆŠorayi.
*Janafty**TKGB3020*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX
Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732
Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰
Bikin Datti ya taho gadan-gadan mu mun ɗauka ma za a ɗaga bikin ne ganin ba a yi shirye-shiryen komai ba amma su Ya Hamza suka ce ba za a ɗaga ba tun da Datti ya kusa gama haɗa lefensa ta hannun Anty Laila a can Abuja. Gidan da za su zauna kuma haya ya kama anan garin Kaduna kusa da ma'aikatansu.
Ya Hamza ya turo da kuɗi Ya Abubakar da Ya Muntari sun yi ja gaba an yi fentin gidanmu ciki da bai. Sannan an gyara ɗakin Mama an yi waje da wasu kariki tai an rufe shi saboda nan Amarya za ta sauka sai sun yi sati sannan za su wuce Kaduna ita da angonta. Duk da can za a yi mata jere amma Kano za a fara kawo ta in ji Datti. Kuma y'an uwansa suka yi naam da haka mu da man namu kawai to ne da bi, saboda ƙurewar lokaci shi ya sa ba mu tara kuɗi masu yawa ba amma kowa ya yi abin da zai iya dai'dai ƙarfin sa mun damƙa ma Datti, amma ni da Amina mun ƙara masa da leshi guda biyu da atamfa aka ƙara cikin lefen shi. Gida da man su Ya Hamza sun ɗauke komai hatta da abincin da za a ci har a gama biki, balle kuma Alhajinmu na da hatsi a store sai abubuwa suka taho mana da sauƙi.
Ana saura kwana huɗu aka kai lefe. Daga Abuja Laila suka kawo shi Zaria bayan duk mun gama ganiwashegari ni da Ya Murja da Ya Aina da Inna Mariya muka tafi da su Kaduna muka haɗu da Amina a gidanta sannan direban mijinta ya tuƙamu zuwa gidan su Amaryan mai suna Badariya. Mun samu kyakyawan tarba sai godiya akwati bakwai muka kai kuma mun yi daidai abin da ya kamata wanda ba za a raina ba. Kuma ba su raina ba ɗin mun ci mun sha har da guzuri sannan sun bamu tuƙwaici muka ce ma ba za mu karɓa ba suka matsa mana. A gidan Amina muka kwana sai washegari har da ita da yara muka tattaro Kano gabaɗaya. Muna zuwa muka iske mutanen Zaria sun iso da mutanen Yashe gida ya fara ɗaukan harama. Dangin Mama na gandun albasa da man ni ce na sanar da su bikin suna ta faɗa domin ba a faɗa musu da wuri ba amma duk da haka sun haɗa kudaɗe sun aiko mana da shi, har gobe ba su yada wannan zumuncin ba.
Jidda ta kira ni a waya har tana mini shagwaɓa wai na bar ta tazo bikin Uncle Datti na ce mata ni ba ruwana ta kira babanta, ita kanta ta san ɓata ma kanta lokaci ne ba zai bar ta ba, nan da nan ya ce ta zauna makaranta ta yi karatunta ga bikin Adnan nan in ya ga cancantar ta taho zai tura aje a ɗaukota. Ta kirani kamar ta yi kuka tana faɗa mini ina yi mata dariya. Sai a lokacin ma take faɗa mini har Rabi'atu ta saka ta yi ma baban na su magiya amma bai amince ba ni ta so na saka baki ni kuma na ce ba ruwana ta zauna ta yi karatunta kamar yadda ya ce ba a gama ba, ga bikin Adnan nan tsakaninsu sati uku ne su har sun fidda anko ma, mu dai na Datti ba mu fitar ba lokaci ya kure kowa na shi zai saka.
Ban raba cinghan ɗin gayyata ba amma na sanar da baki. Kaf dangin Yallaɓai suna da labarin ƙanina zai yi aure. Balle ma na san Yallaɓai zai sanar a group ɗin su na gida nima kuma Munnira ta sanar a wanda muke ciki ta ce muna gayyatar kowa da kowa. Rabi'atu da Gimbiya ko kowacce har shashenta na kai mata kati na sanar da ita. Rabi'atu ce ke murna ita da Baby amma Gimbiya ce mini ta yi itama ranar tana da biki a Rano can ma za ta kwana. Ni kuma sai na ce in ta yi ma addu'a ya wadatar. Yallaɓai kuma ya ce mini zai je ɗaurin aure sannan Datti ya kirani ya ce na taya shi godiya 100k Yallaɓai ya tura mai da na yi masa godiya sai ya shafa kumatuna yana faɗin" Nima ai Datti ƙanina ne."
Sai na jinjina masa kai amma duk da hakan dai na yi masa godiya.
Ana gobe biki acan na kwana ni da Yumna kaya ma Baby ce da safe suka taho mini da shi ita da Rabi'atu. Na ga kara sosai su Munnira tun safe suka zo mini biki su Suwaiba duk sun leƙe min har Mimisco ta zo, ta ba ma Gwaggo 10k. Gimbiya dai da safe ta leƙo ko minti talatin ba ta yi ba ta ce mini za ta wuce Rano na yi mata godiya na rakata har waje. Da yake ɗaurin auren na safe ne zuwa la'asar tuni har yan ɗaurin aure tun kamo hanya da Amarya. Yallabai da Kawu sun je ɗaurin aure Tariq da dake can ya samu zuwa, mu kuma muna gida muna shirin tarban su, sun iso wajen biyar na yamma kai tsaye gida suka taho da ita muka tarbeta a ɗakin Mama aka sauke su ita da y'an uwanta da ƙawayenta abinci da komai ba su da matsala duk mun tanada.
Marwa tun jiya itama ta na nan, Mubeena ce kawai ba ta zo mini biki ba tana gidansu ba ta da lafiya laulayi. Ta samu ciki sau biyu yana zubewa sai yanzu ta sake samu. Ma'u ma sai fama da tsohon ciki, riki riki ita abokan zamanta sun zo mata biki, ni kam da man Rabi'atu tana gidan nan tun safe sai dare sannan Yallaɓai ya zo ya ɗauketa suka koma gida. Ni da yara duk nan gida muka sake kwana. Dangi an haɗu gabaɗaya kamar kar a rabu yan gandun albasa ma sai ranar lahadi suka koma, mu kam sai litini sai da aka ci aka suɗe a ranar duk su Ya Hamza suka koma da matan su, a bikin ne muka ji an saka ranar auren Anti ɗiyar Ya Murja, Ya Balki ma ta ce mai son Firdausi an turo, ina tunanin bikin nan zai yi mana rudgudu, yanzu dai sai dai in Ma'u ta haihu za mu sake haɗuwa. Muka baro gida da Amarya sai Gwaggo da Baaba amma dangin ta sun kawo kayan fulawa da kololi, da sauran kayan al'ada kuma duk an rarraba mana har dangin Mama suma an ɗibar musu na su kason