← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 103

Sashe 38

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na faɗa ina shiga tsakiyar su saboda Amina ta ta so tana faɗin" Wallahi ƙarya kike yi. Kin san ko daga yanayin mu za ki san mun fi ƙarfin wannan abun da kike haƙilo a kan shi. Ni mijina ba mai kuɗi ba ne amma yana da rufin asiri kuma a gidan ubana mun fi ƙarfin abincin shekara. Kaf yayyena suna gidan mazajensu cikin rufin asirin mazan kuma akwai ma'aikacin banki da ma'aikacin bankin kuɗin duniya wato CVN kin ga ko tsakanin ni da ke sai a nemi wanda ke rigima kan tsire. Tsiren da dubu biyat ɗin ki ta gama biya miki bukata amma kin tsaya kina ta da jijiyan wuya. An daɗe ba a gamu ba miyau ya tsinke ƙwadayi ya tashi ba."

"Amina."

Haka na ke kiran sunanta amma ce min take yi" Ya Sadiya don Allah bar ni na ga karshen rashin kunyar yarinyar nan."

"Ni ba mara kunya ba ce. Sannan yarinya na bayan uwarta."

"Ke Halima."

Na daka matsa tsawa domin raina ya gama baci na ga tana shirin zagar mini uwa ne a gaba na kuma a gidana.

"Ni da gidan yayana ke É—in banza?

"Ƙwarai kin fita iko da shi. Abin da a ka hana ki ma ai yayan na ki ya siya ko?

Naja ta shigar mata, Amina na ja ina mata faÉ—a.

"Me ya haÉ—a ki sa'in sa da ita?
"Ya Sadiya ni fa ban shiga harkan ta ba, ba kin ce na riƙe na bakin mu a hannuna ba, kawai ta na ganina da shi ta ce sai na ba ta leda ɗaya ni kuma sai na ga ai ga shi nan a hannunta Munnira ta ba ta, amma matar nan ta na ce sai na sake bata sai na ce ita ta samu wasu ba su samu ba ta bari a sallami waɗanda ba su samu shike nan ta fara zagina ta na gaya mini mangaganu duk yadda na kai ga haƙurina sai da ta ƙure ni."

"Nima na zo ina yi ma Haliman magana tana neman yi mini rashin kunya."

Munnira ta faɗa tana kallona sai na kaɗa kai ina faɗin" Amina dauka ki ba ta. Ko ba yayanta ya siya ba matar yayanta ce ta siya. Ko guda goma take so ki ba ta ai arziƙi ne a zo wajen ka har kana da abin da za ka ba da."

Ina faɗin haka sai Amina ta miƙa mata leda ukun da ke hannunta, su Ya Aina ma suka ce shikenan ko rigima ta ƙare.
Amma sai Halima ta ƙi karɓa sai ma falati da ta yi da ledan daga hannun Amina. Suka watse mini a tsakiyar falon na yi jagale ina kallon Halima na ɗauka iya nan za ta tsaya amma ba ta tsaya ba kamar ta na jirana.

"Ai ni nafi ƙarfin wannan abun. Ke dai ki kara akai gida."

"Kin fi ƙarfin shi kike rigima don an hana ki?

Munnira ta katse Halima. Ya Balki ta saka baki da cewa kowa ya yi hakuri ta duka ta na kwashe wanda Halima ta zubar Hauwa ta amshe ta. Amina za ta sake mgana Ya Aina ta tare ta ni ko daman ina ta danne zuciyata ne amma ba domin haka ba wallahi Halima ba ta isa ba. Gimbiyar ta su na zaune ta haÉ—a kafafu tana kaÉ—awa

"Na gode Halima. Tun da masalahan da na nema da ke baki yarda ba, ba na son tashin hankali zo ki fice ki bar mini gidana."

Na faɗa ina nuna mata hanya. Yadda ta kalle ni cikin mamaki ne ya sa na ƙara haɗa rai na.

"E ki fita ki bar mini gidana na gode da sunan da kika zo amma ni ba na son rigima"

"In fita fa ba kika ce?

"E ki fita na ce"

Na ina ƙara jadadda mata sai ta juya tana kallon su Naja suma da mamakina a fuskokinsu.

"Sadiya ƙyaleta kawai. Ai Aminar an shiga da ita ciki maganar ta ƙare."

In ji Ma'u sai na juya ina kallonta kafin na ce" Wallahi sai ta bar mini gida. Ta zo ta fita kawai."
Na faɗa cikin ɓacin rai, ina sake nuna mata hanyar fita.

"To ba zan fita ba."

Ta faɗa tana ƙara cijewa har da riƙe kugu.

"Ba zan fita ba, tun da nan É—in ai ba gidan ki ba ne."

"Ok to ke gidan ki ne?

Na katsete cikin ina saita kaina domin wallahi in na harzuƙa zan iya jawo ta na yi mata bugun tsiya ba ruwana da aurenta ballanta ya'yan ta.

"Ba gidana ba ne amma gidan yayana ne na fi ki iko da shi. Kuma ai nan É—in ba gidan ubanki ba ne"

A bazata na ji maganar duk lalacewata a idanuwan Halima ban É—auka za ta iya zagin ubana ba.

"Ke Halima Sadiya kika zaga?

In ji Suwaiba da ta shigo falon yanzu daman na bar ta a É—akina tana salla.

"Ita wace ce da ba za a zage ta ba. Na ga za ta nuna mini iko ne da gidan Yayana. Alhalin ba ta isa ba ita É—in banza abanza k"

"Tas!

Sai ƙaran saukan mari suka ji na sharara ma Halima mari sai ga ta dafe da ƙuunci.

"Ko giwa ta mutu ba ta yi lalacewar da kiyashi zai ja ta ba. Ba ki isa ki zo har gidana ki ci kasuwa a kaina ba ƙaryan ki yarinya gwara tun wuri ki shiga hankalin ki, ki kuma kwashi jikinki ki fice mini a gida kafin raina ya ɓaci wallahi na yi miki dukan tsiya"

"Ni kika mara?

"In ba ki fice mini a gida ba duka zan yi miki wallahi."

Na faÉ—a ina nuna mata zan iya ya É—in. Munnira ta kwashe da dariya Suwaiba da Jamila suka ce da kyau.

"Me ya sa kika mare ta a kan gaskiyan ta?

Naja ta miƙe tana challanging ɗina.

"Na mare ta ko za ki rama mata ne?

Na faÉ—a ina kallonta domin kaÉ—an na ke jira yanzu sai na saka a yi musu dukan tsiya su bar mini gida amma sai na ga Gimbiyar ba ta yi magana ba.
Kuma ba ta tsawarta ba.

"In nan gidan Yayanta ne ni kuma matar yayanta ne da gidan da shi kan shi yayan nata a ƙarƙashin ikona suke. Kuma ko shi bai isa ya zo yana mini wulaƙanci ba, ballanta ita ɗin banza. Duk wacce ba lafiya ya kawo ta ba, ta zo ta fice mini a gida kafin na haukace muku."

Kawai sai na fara masifa ina faɗin ni da gidana ba shege ko shegiyar da ta isa wallahi. Amma suka ƙi fita na ce zan yi ma Halima duka Ya Murja da su Rahila suka rike ni ashe tun fara faɗan Gimbiya ta kira Yallabai ana cikin haka sai ga su shi da Kawu ashe ma suna hanyar zuwa ne ta kira shi wai gani nan na kori Halima har ina marinta. Lokacin da suka shigo na gama harzuƙa yana tambayan ba'asi ni ban bi ta kan shi ba Suwaiba ce da su Munnira ke ma yar musu da zence.

"Wallahi sai Halima ta bar minI gida in kuma ba ta fita ba ni zan fita na bar mata gidan."

Na faɗa ina numfarfashi Kawu ne ke ba ni haƙuri har yana cewa" Gwara da kika mare ta. Kuma kina dai-dai da ki kore ta tun da, ba ta da kunya."
Yallabai da suka yi tunanin zai goyi bayan su sai ya kware musu faÉ—a ya yi mata kaca kaca ya kuma ce ta fita ta bar gidan tun da ba alheri ya kawo ta ba.

"Amma Uncle."

Naja ta tare shi za ta kare ma Halima.

"Rufe min baki kawun me? Me ya sa ba ki tsawarta mata ba?

Ta yi shuru ta kasa mgana Gimbiya ma tas ya yi mata ya ce ta iya kiran shi ta faÉ—a masa na mari Halima amma a gabanta Haliman na yi mini rashin kunya ba ta iya mata mgana ba.

"Ni miye nawa a ciki? Na saka baki sai a ce kishi ne. Ba ruwana kar ka sakani a ciki "

Ta faɗa tana wani tura baki ni saboda haushi ciki na koma ban san yadda suka ƙare ba amma na so wallahi na yi mata dukan tsiya. Kuma ta ƙara dawo mini gida ta gani sai ta raina kanta. Sameena ke faɗa mini daman suna jirana ne sunq ta zagina wai na yi albuzurranci da kuɗin Tafida na ce bakomai na isa ne. A nan ta ke faɗa mini yadda suka yi mata wai ta shige mini saboda munafunci ita kuma ta ce tana tare da ni tuntuni saboda Gimbiya ba za ta ja baya da ni ba.

Ranar raina ɓace na kwana da safe a hanyar mu ta zuwa asibiti ya ke sake ba ni haƙuri na ce bakomai. Mun je an duba ɗinkina suka ce ya kusa warkewa sannan an sake yi ma Yumna allura. Mun dawo gida na iske suna ta suyan ragunan da aka kawo su a yanke yau da safe. Daman na san magana za ta je ta dawo sai da Anty Bahijja ta kirani wai me Halima ta yi mini na mare ta? Na ce rashin kunya ta yi mini buɗe bakin ta sai ce mini ta yi ashe ba daɗi ni ba na yin rashin kunyar ne? Ni kuma na ce ni ban bi kowa gidan shi na yi masa rashin kunya ba itama gidana ta zo kuma ko yau ta dawo wallahi ta ƙara mini rashin kunya duka zan mata ba ma mari ba. Ai sai ta ce to kar na fasa mu ka kashe waya zukata na ƙuna.
Chapter 38 · 0% Book details