← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 103

Sashe 74

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta faÉ—a cikin sanyin murya. Ta tambayi su Jidda na ce suna nan gida an yi hutu.

"Ina ta yi ma Yallaɓei magiyan ya kawo mini su ya ce sai ya tambaye ki "

Ina kallon shi na ce" Ba ruwana ai shine shugaba abin da ya ce shi za a yi. Yadda ya dama haka muke sha."

Tana ta dariya ni kuma na yi mata alƙwarin in su Khalipa sun yi hutu zAi kawo mata su gabaɗaya sai da na ba shi wayar ya kashe bayan ya ce mata zai kira daga baya yake faɗa mini karshrn watan nan itama za ta je maiduguri. Sai dai ya kai su wani sati ta gan su.

"Tana son yara na. Ko da yaushe sai ta yi mini ƙorafin na kai mata su. Jidda ma zan ba ta lambar wayarta itama zan ba ta nata su riƙa gaisawa."

"Hakan ya yi "

Domin ni yanzu yar bi ce, in dsi akan auren nan na Yallaɓai nr, ga Gimbiya tana can har an saka rana shaida ba abin da za a fasa.
Anty Zabba ta kirani a waya tana ta dariyan mugunta ta ce ai da Ya Usman ya faÉ—a mata ta buga guÉ—a. Itama har ta ji labarin Gimbiya ta yi yaji.

"Sakara kawai. Wa ya faɗa mata ana cin riban namiji in har ya tashi ƙara aure? Ai da ta kwantar da hankalinta da ta ci riba."

Ni dai ban furta ba, domin har a cikin zuciyata ban ji daɗin tafiyarta ba ba ni da yadda zan yi ne. Maganar auren Yallaɓai ta fasu a gari tun da duk an sanar a groups ɗin su na gida,nima sai na faɗa ana gidanmu. Ya Aina ta ce af ita ai ta san za a rina Ma'u ta yi ta masifa wai Yallaɓai ya cika haɗa ma har Ya Auwal ya fito ya ce ba ma son gaskiya. Shima yana da niyyar sai ya yi huɗu in sha Allahu muna ta dariya.
Hauwa da Munnira sun yi ta ƙorafin me ya sa na amince amarya ta fara tarewa a sabon gida?

"To miye a ciki? Mijin ma gabaÉ—aya za ta mu raba shi tare miye abin damuwa a gida. Ta tare can ya gama mararinta daga baya mu sai mu koma."

Daga haka na kashe bakin su, Gimbiya sama da sati biyu sannan ta dawo, shi kuma da kan shi ya faÉ—a mini har yana faharin shi bai je ba, su Anty Bahijja ne suke je suka dawo da ita Bayan Tafidan Rano ya yi mata faÉ—a sosai. Har kuma ta dawo su Khalipa na gida ba su koma ba, shi bai ma yar da su ba nima ban ce su koma ba na bar su ko itama za ta samu kwanciyar hankali. In da ta ji shawarata wallahi da duk haka bai faru da ita ba.

Kwana É—aya tsakanin faÉ—a mini da ya yi ta dawo. Ranar ma a gidan ta ya kwana da safe da ya ke ranar laraba ne su Khalipa na makaranta suna Jarabawa ne ina cikin bedroon su Jidda ke da gidan yanzu tun da suna nan daga ita har Baby ba na yin aikin komai sai dai na kwanta na tashi na ci kawai. Haihuwa mai rana
Ina cikin ɗakin Baby ta zo ta ce mini ga Gwaggo Bahijja da Anty Gimbiya nan sun zo, na yi ta mamakin zuwan su. Ban ɓata lokaci ba na saka ɗankwali na fita falon Yallaɓai in da suke zaune

Wallahi na tsausayama Gimbiya duk ta faɗa ta yi zuru zuru ba gayu yau. Na yi mamakin da muka gaisa da Anty Bahijja faram faram kamar ba mu taɓa samun matsala ba ashe alfarma aka zo ci dole a yi mimi haba haba.
Wai Anty Bahijja ke faɗa mini mu haɗa kai da Gimbiya domin mu rusa wannan auren tun da Yallaɓai na jin maganata.

"In ma auren ba zai fasu ba. To ku tabbata bayan an yi aurwn yarinyar nan ba ta ji daÉ—in zama da shi ba. Ku haÉ—e kan ku ke da ita domin ku tsira tare."

In ji Anty Bahijja.

"Kuma ma har da maganar gida. Ke sai ki amince yarinyae can ta fara tarewa? Wallahi ba zan yarda da."

In ji Gimbiya.

"Yauwa har maganan gidan ku haÉ—e kai ku ce ba ku yarda ba. Ko ya gyara ku fara tarewa kafin auren ko itama ya nena mata wajen zama ta jira ku tare gabaÉ—aya ko ba gaskiys ba."

Anty Bahijja ta faÉ—a tana kallona.

"Gaskiya ne."

Na faÉ—a ina Æ´ar dariya ina mai kallon su a É—age É—aya bayan É—aya..
Sai yanzu ne suka san ina da amfani? Wato na haɗa kai da Gimbiya saboda su mafitarsu suke nema. Ni kuma wallahi ba wacce ta isa ta saka ni na zubar da girmana. Yallaɓai ya nuna ma yarinyar nan ina da daraja a rayuwarsa shima ya nuna ma duniya ina da ƙima a wajen sa saboda kishiyar da ba ta ɗauke ni a bakin komai ba ba zan yi wasa da mutumcima ba.

"Ku yi hakuri zencen gaskiya ki cire ni a wannan lissafin ba zan iya aikata ko É—aya a ciki ba '

Na faÉ—a ina kallon su, suma ni suke kallo cikin mamaki.

"Aurn da zai yi umarnin Allah ne. Maganar gida kuma gidan shi, don ya ce ga yadda za a yi ni ban isa na ce ba haka ba. Allah na tuba mijin ma aka yi sharing ɗin sa da ita sai gida ne zama abin damuwa ? Ni a ganina wannan ba hanyar ɓulllewa ba ce, hakuri shi ne kawai. Amma ba abin da za a fasa."

"Da man na faÉ—a miki ba za ta yadda ba. Ita fa jin dadi take yi Saboda ni za a yi mawa ba ita ba tana bashi goyon baya."

Gimbiya ta faÉ—a ma Anty Bahijja.

"Naga alama."

Sai kawai na miƙe ina faɗin" Duk yadda kuka ɗauka dai dai ne. Ni dai Allah na gani ba zan yi hauka saboda Yallabai zai ƙara aure ba, in ke za ki yi haushi to ki yi shi kaɗai amma ba tare da ni ba. Sannan sai yau da zai ƙara aure na ke da amfani a wajen ku? Ai ba ki taba kawo ta ko ce mu haɗa kai ba sai yau. Saboda amfanin ku ne, to ba zan yi ba kowa tashi ta fishshe shi."

Ina gama faÉ—in haka na bar musu falon na san sun yi suman zaune da mamakina.

*Janafty**TKGB3018*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/Gkzmhd0zmnFChYrdONLFYp

Bedroom ɗina na koma na yi zama na ban san lokacin da suka tafi ba, har ga Allah ba ina murna da ƙarin auren Yallaɓai ba ne saboda kishiya ai sunan ta kishiya nima a zaman matar mijina take. Na so Gimbiya ta ji maganata ta kwantar da hankalinta saboda ta tsira da sauran mutumcinta amma taƙi jin maganata tana biye ma su Anty Bahijja. Wanda na tabbata in aka juri zuwa rafi wata rana tulu zai fashe, dole akwai bangaren da za ta nuna mata Yallaɓai ne jininta na kusa ba ita ba.

Abin da nake yi ita a ganinta ina bin bayan auran Yallaɓai ne saboda ita, abin da ba ta sani ba da na bi baya da ban bi baya ba ban ga dalilin da zai saka Yallaɓai ya fasa wannan auran ba, yau ko Nene ce ta hana shi na tabbata zai yini yana yi mata karatun da za ta gane har ta amince domin bai ɗauko maganar auran nan don ya fasa ba. Shi ya sa gwara ta kwantar da hankalinta domin ba abin da za a fasa.
Rasa wanda zan kira na tseguminta masa zuwan Gimbiya da Anty Bahijja sai Munnira ina faÉ—a mata ta yi dariya da shewa kafin ta ce.

"Sai yanzu suka san ana haÉ—a kai? Wato sai yanzu da suke neman mafitar su."

"Wallahi, ni kaina zuwan su ya ba ni mamaki. Har Anty Bahijja na faÉ—in wai mu haÉ—a kai ko ba mu rusa auran ba mu hana su zaman lafiya har sai ya gaji ya sake ta"

Na faɗa, ina riƙe baki domin sai a lokacin na ke jin ma ƙarin mamakin zuwan su da magangansu.

"Lalle. Ni ban yi mamaki da man na san za a zo wajen. To ke me kika faÉ—a musu?

"Na ce ni ba zan haɗa kai domin a yi tashin hankali da ni ba itama ina na faɗa mata gaskiyan ta bar ma komai ta kwantar da hankalinta. Amma ba ta ji ba ita a ganinta ina goyon bayan Yallaɓai saboda ita ne, ni kuma wallahi ba haka ba ne Munnira. Kin sanni ba ni da wanman muguntar, ina tausaya mata ne domin a irin rawan kafan da Yallaɓai ya ke yi a kan auran nan ni ko ita wallahi ba mu da darajan da za mu iya dakatar da shi, shi ya sa na koma gefe na zama yar kallo na shafa ma kaina lafiya."

"Haba na sani wallahi. Kin huta da man a irin wannan lokacin in baku sauke
a kai ba sai a samu matsala. Kuma su Anty Bahijja ne za su ɗora ta akan keken ɓera su kaita su baro ta."

Na amsa da wallahi, domin in ta kwaɓe su kan su ba za su iya ba. Wai maimakon su ce ta yi haƙuri ta ma yar da lamarin ta ga Allah, amma suna zugata ta yi tashin hankali da miji. Har muka gama waya da Munnira ita kanta ta ce da Gimbiya ta kwantar da hankalinta da zai fi mata alherin akan wannan haukan kishin da ta ke yi, nima abin da na hango mata kenan. Bayan Munnira ban faɗa ma kowa zuwan su Gimbiya ko Hauwa ba mu yi taɗin da ita ba, a satin na je Ɗorayi gai da su Alhajinmu ina faɗa masa ƙarin auran Yallaɓai, sai ga magana tiryan tiryan a bakin Alhaji.
Chapter 74 · 0% Book details