Sashe 18
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun yi fa abubuwa Gimbiya da gayya ta ke komai amma ni ban biye mata, sai mangariba a ka tashi sai a lokacin Ant Zuwaira ta zo tana zuwa kuma ta nemo ni ni da Munnira da Anty Zabba ta ce mu shirya da mu za a je Kaduna kai Amarya.
"Anty Zuwaira ina fama da kaina'"
"Ai kin ji sauƙi ko ba za ki iya zuwa ba ne?
Sai na kasa musa mata sai ta buga kafaÉ—ata da cewa" Ku ne matan kawunne manya saboda haka da ku za a je."
Sai na ce to Allah ya kai mu Hauwa a ka ce ba za ta je su sai daga baya ba a son a je da yawa ne. Anty Zuwaira ta ce ba da ita ba Anty Maimuna ce da Nasara sai Suwaiba da Halima a yayyen uwa iyaye kenan sai Maman farko da Hajiyar Tafida da ƙanwar baban Sulaihat ɗin a kakkanin Amarya. Sai ƴaƴan yayyen baban ta guda biyu ƙawayenta. Sai a nan aka zaɓo ɗiyar Anty Maimuna sai yar makarantar su guda ɗaya ƙawarta. A Rano kuma an saka yayar Gimbiya amma ita ban ji an saka ta ba sannan har da Faridan Tariq Marwa ma an saka ta ita kaɗai a ce a matan kawun ne. Ana so a yi lamarin da tsari ne kamar da angon ya bukata ba su son cikowa abun ka ga masu kuɗi. An ce matukin jirgin kasa ne Captain akwai kuɗi a hannun shi sannan zuru'an su suna da kuɗi nima duk a bakin Munnira nake ji tsuliyan gari.
Da na koma gida ni kaɗai yara duk suna can na baro su za su kwana. Sai ga Yallaɓai ba a gidana yake ba sai ya ce Gimbiya da yara can za su kwana sai washegari jumma'a ranar walima muna karyawa ya ce.
"Za ki iya zuwa kaduna kuwa?
Ya Zuwaira ta matsa mini sai ke dai kin je."
"Nima haka ta faÉ—a mini jiya. Ni da Munnira da Anty Zabba."
Yana kurɓa tea ɗin dake hannun shi a mug ya ce" Na ce ga Daughter tun da ita ce ta ce minibza ta je kai Amarya amma sai ta ce a a dole sai ke tun da ke ce Babba."
Ban yi magana ba amma ni kaina na san Gimbiya za ta ce sai ta je kaduna kai amarya yadda ta ke rawan jiki da bikin nan.
"Shike nan tun da za ki iya zuwa sai ki shirya. Amma please ki kular mini da kanki da Baby na."
Ya faÉ—a ya na mini murmishi.
Nima sai na yi masa murmushi kafin na ce" Da na ce ko ita Gimbiyar ta je?
"A'a gaskiya Ya Zuwaira ta faɗa ke ce Babba kuma ke ɗin ce wakiliyata so ke ɗin ya kamata ki je tun da kin ji sauƙi."
Sai na gyaÉ—a kaina ban saka aka ba wallahi.
Ranar mun je walima ban san me ya faru ba mun haɗu da Gimbiya a ƙofar shiga falon Anty Bahijja ina washe mata baki ta yi kamar ba ta ganni ba ta ɗauke kanta. Har ta na ture kafaɗanta sai da muka shiga ciki ne Suwaiba ke faɗa mini kan tafiya kaduna ne an ce su bari sau ranar lahadi sai su je tare da wasu kayan ita da Naja shi ne ta ce ita tuni su yi mgana da Tafida kuma ya ce za ta je Kaduna. Ita kuma Anty Zuwaira ta ce ni ce zamu tafi da Amarya gobe shi ne ta fita tana ƙunƙuni
"Topha."
Na faɗa a fili a raina na ce ni ban ga abin ɓacin rai ba.
Munnira ta ce ta raina wayon ta akan kai amarya sai kace zuwa madina?
Ni dai Allah ya kyauta kawai na ce kuma a ranar sai da Anty Zuwaira ta tabbatar mini da na shirya da ni za a je.
Ranar ma ba ta yi mini mgana ba sai fushi take yi tana cika ta na batsewa. Ma'u ta ba ni tausayi da bikin nan kamar ba a santa ba, ita kanta Anty Bahijja ta na fama da mutane ba ta bi ta kanta ba, sai dai tana raɓe wajen dangin mijinta da a ce muna zaman amana ne ni da ita za mu haɗe to da yake ba ta da hali sai ta zama kamar mujiya ga shi Shema ta yi aure da a da ne tare za su zo.
An sha wa'azi malamai uku aka gayyato mata suka yi ma amarya wa'azin zaman aure da zamantakewa sai mangariba a ka tashi. Yallaɓai ya zo ya ɗauke ni wajen taran dare kuma ko gidan bai shiga ba. Bayan mun koma na ga ya na ta waya abin da ya sa na fahimci da Gimbiya yake mgana saboda maganar da ya yi mata.
"Me ya sa kike da taurin kai ne Saudatu? Na ce miki ba za ki je ba Sadiya ce babba ita za ta je kuma hakan ne ya kamata."
"Ok to ki yi yadda kike so"
Ya faɗa a fusace ya kashe wayar. Ban taɓa jin ya kira sunanta ba sai ranar, ta kwaɓe musu saboda zuwana Kaduna ni ko da karambani bayan mun kwanta na ga har lokacin bai huce ba sai na ce masa na hakura ya bar ta ta je kawai.
"Wallahi ba za ta je ba. Ke ma in ba za ki je ba fine amma na riga na rantse ba za ta je ba kuma kin san ba macen da isa ta saka ni na yi kaffaran kan aikin banza da wofi."
Ai ina jin haka sai na koma na lafe a kan filo na ji shuru. Shi da kan shi da ya hucen ya matso ni jikinsa lokacin na ma ɗan fara barci ina ƙoƙarin motsawa na ji yana mini raɗa
a kunni.
"Sai da safe"
Ban amsa mishi ba saboda barcin ya fara fizgata. Na dai ƙara shiga jikinsa sosai na lafe shi kuma ina jin sa yana rufe mana jiki da bargo.
*Janafty**TKGB30E05*
Washegari asabar muka tashi da shagalin biki. Sha ɗaya na safe a ka ɗaura aure kuma sun ce a lokacin za su tafi da amarya. Shi ya sa duk nuƙu nuƙun da a ka tsaya yi ɗaya da rabi motacin ɗaukan Amarya suka miƙa hanya. Ni mota ɗaya muka shiga da Munnira da Anty Zabba sai Marwa. Faridan Tariq tana motar Amarya a gidan gaba.
 Da yake motocin sabbi ne sannan kuma masu lafiya ne a na gudu ma sai ka ji kamar ma ba a yi. Zuwa huɗu da rabi biyar saura mun sauka a gidan Amarya. Mun iske matar Jafar Nauwara, sai ƙawayen Anty Bahijja ina ga su ƴan Kaduna nan ne da wasu dangin angon su suka tarbe mu. Ma sha Allah gida ya yi kyau ƙwarai. kuma iyayenta sun kashe mata kuɗi kayan ta kaf ba na Nigeria ba ne a ƙasar waje a ka siyo su kuma ba a sauke su ko'ina ba sai Kaduna. Kuma da ya ke akwai ma'aikata maza su suka gyara komai, mu kan mu kayan kitchen ne muka zo da shi sai su cafet da labulanya sai ɗan abin da ba a rasa ba. A nan muka yi sallar la'asar muka ci abinci sannan muka kama a ka ƙarisa gyaran daƙun nan. Muna gidan har dare dangin mijin na ta zuwa a nan ne ma mu ke jin jibi jibin nan za su bi jirgin yawo zuwa Madina, mai son ganin ɗakin Amarya sai dai ya jira bayan salla kuma in sun dawo daga Hajji.
Ba a gidan Amarya muka kwana ba. Ni da Munnira da Anty Zabba har da Marwa gidan Faridan Tariq muka kwana. Ita ma Nauwaran Jafar ta diɓi wasu ƴan'uwa. Daga ƙawayenta sai kakkaninta a ka bar Amarya da su ta kwana. Kuma bayan mun kwana can muka hantse sai wajen sha ɗaya muka dawo gidan Amarya da ke anguwan malali.
Da yake abin na yan gayu ne ba wani cikowa sannan an gyara ko'ina tsab. Muna komawa ba daÉ—ewa sai ga Naja ta zo ita da Suwaiba da Halima sai Anty Maimuna jiya ba su samu tafiya ba. Ni dai ban ga Gimbiya ba, ban kuma Tambaya ba amma Munnira sai da ta tambayi Suwaiba ita kuma ta ce Gimbiyar ce ta mata musu lokacin a na ta jiran ta daga baya ta ce su ta fi ba za ta je ba. Zuwa kai Amarya kamar wani kayan gabas ni Sadiya?
Sai da muka yi azahar muka ci abinci sannan a ka kawo mota muka É—au Amarya da su turamen atamfa da shadda sai kayan abinci da su cincin É—in da su Naja suka taho da shi.
Gidan Iyayen mijin muka je da ke NDA. Muka kai musu Amarya sannan da kayan da muka ta ho da shi. Amarya ta samu tarba da kuɗaɗe sosai. Da ya ke suna da kumbar susa ko su gidan iyayen na shi ma a abin kallo ne. Sai a lokacin suke faɗa mana tafiyar su Madina jibi in sha Allahu a ka yi ta fatan alheri. Muna gidan har wajen uku saura sannan muka yi shirin tafiya daman kowacce da shirin ta tun da sun faɗa mana daga nan Kano za a wuce da mu. Nan muka bar Nauwaran Jafar da Farida sai Hajiyar Tafida da Tariq ya riƙe ta wai ta jira shi zuwa gobe zai saka a mai da ita gida. Mu kan mu an ba mu turamen Atamfa kowaccen mu sannan da kuɗi cash 10k sannan a ka ɗauke mu zuwa Kano cikin motocin alfarma kamar yadda a ka ɗauko mu.