Sashe 48
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kin isa ma tun da gashi kin rufe ni da faɗa daga mgana. Na gaji fa wallahi zan daina raga muku daga ke har ita ba daman in yi magana a kan ku da ɗaya daga cikin su sai cibi ya zama kari daga mai cewa ba na yi mata adalci sai yi mini tsaki, sai mai cewa in an cuceta Allah ya isa. Yau dai mai kankat kin ce ni din nan wai Aniyata ta bini, daga magana ko barina ma na ƙarisa maganata ba ki yi ba kin rufe ni da faɗa kamar wani ɗan ki."
Ya faɗa a fusace, jijiyoyin sa na sake miƙewa kamar daman yana jira na ne.
"Kai ba ka ga laifin matarka ba?
"E ban ga laifin ta ba. Na faɗa miki daga yau ba zan ƙara raga muku ba. Ba ta yuyuwa ina mijinku kuna ƙarƙashina amma kuna ƙokarin rika sarrafa ni, saboda kawai ina muku kawaici? Kaina a ka fara auran mata biyu? Na gaji wallahi ku fita hanyata kafin wata rana ku harzuƙa ni na yi muku abin da ba ku yi tunani ba."
Ganin yadda ya fusata ya sa sai na yi shuru, salaf salf na fice zuwa tiolet ina kunshe dariyata ashe itama can rufe shi take yi da faɗa a kaina. Ina ga ita ce ta yi masa Allah ya isa ni dai ba ni ba ce, kama ruwa na yi na fito ina saita kaina ko da na dawo ya ja Yumna ya rumgume yau sai dai na ci kaina kenan mirmishi na yi, na shafa ma hannayena da wuyana turare sannan na kashe fitilar ɗakin na kwanta muka saka Yumna a tsakiya na ja hannun shi ina so na sarke tare da hannuna ya ƙi ya damƙe hannun shi, na tsugule shi a hannun amma ya damƙe sai ma ya rike hannun Yumna cikin na shi na ya jimƙe.
Ni da na ke son rigima sai na taso daga in da na ke na haura tsakiya na raba shi da Yumna na shige jikinsa mamaki ya hana shi magana ina kallon shi ta É—an hasken dake shigowa ta waje ya É—an murmusa.
Ya rumgumeni, na kwanta a saman kirjinsa muna kallon Dama ni da shi dukkanmu mun sarƙe hannayen mu waje ɗaya mun rumgumo Yunma ina jin sa ya yi mana addu'an barci ya tofa mana. Ba mu daɗe ba ni da shi barci ya ɗauke mu, Yumna daman ta rigamu komawa tun da ta sha Nono ta koma barcinta.
Asuba ta gari. YUFSAD.
*Janafty**TKGB30L12*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
Washe-gari haka Yallaɓai ya tashi yana mini cin magani ina masa magana da ƙyar yake amsa ni, sai ya koma ma ya na ba ni dariya. Sai da na sallami yara zuwa makaranta sannan na yi ma Yumna wanka na shiryata na bashi ita ya riƙe ta na koma kitchen ina duba dankalin turawan da na saka amai kar ya ƙone.
Har Jidda yau suna da paper ta tafi daga ni sai Yallaɓai a gida sai Yumna ina daga Kitchen ina jiyo dariyan ta yana yi mata wasa. Mirmishi kawai na yi, in dai Yumna ne yanzu har ta waye da wasannin Yallaɓai ƙiyuwa ta fara yi ma Jidda saboda ita ba ta yi mata wasa amma da Baby ne ko su Khalipa da ba ma ganin su take yi koda yaushe ba har tana zillo in ta gan su. Yallaɓai ko ta riƙa harba ƙafafuwa kenan in ta gan shi in ko tana zaune ne sai ta tsintsira tun ina mamaki har na daina.
Yallaɓai da wuri ya ce mini zai fita, zai fara biyawa ta Gwammaja ya duba Nene kafin ya wuce office. Shi ya sa da wuri ya yi wanka ya shirya nima wankan na yi sannan muka zauna a kan dining muna karyawa sai kiran shi ake yi a waya harkokinsa can dai.
"Yallaɓai ka ce harkokin sun buɗe?
"Alhamdulillah."
Ya faɗa fuskarsa ba walwala lokaci ɗaya yana tusa dankalin a bakin shi sannan ya bi da ruwan tea ɗin dake cikin ƙaramin mug a gaban shi.
"To duk fushin na mene ne mijin Sadiya?
Kallona ya yi sai kawai ya É—auke kan shi ya cigaba da cin dankalin shi da tea.
"Mene ne uhm? Ni ce? To yi hakuri ka ji Yallaɓai na. Ba na son ina ganin ɓacin ranka"
"A baya ne ba ki san ganin ɓacin raina amma ban da yanzu."
Ya faɗa ba tare da ya kalleni ba, sai na yi mirmishi kafin na ce" To na ji yi haƙuri ka ji?
"Uhn"
Ya faÉ—a kawai yana cigaba da tura dankali bakin sa.
"To ka ce ka haƙura mana?
"Me kika yi mini? Ba ki yi mini laifin komai ba so ki daina ba ni haƙuri"
"Na yi mana. Maganar jiya ko?
Na faɗa ina kallon sa, ni dai na san ran shi ya ɓaci kuma ya na jin haushina ko don ganin yadda yake magana yana cin magani.
"Ka yi haƙuri ni ba da kai nake ba"
"To da wa kike?
Ya faÉ—a yana kallona sai na kasa magana saboda ya zura mini idanuwansa cikin wani yanayi yana kallona.
Kai kawai ya girgiza sannan ya mai da kansa ƙasa ya cigaba da shan tea ɗin sa ba tare da ya ƙara wata magana ba ni kuma sai jikina ya yi sanyi sosai nima sai na debo dankali ina mai turawa a bakina cikin sanyin jiki da na zuciya.
Bai wani ci da yawa ba ya share bakin sa da tissue É—in da ke saman dining sannan ya É—ago yana kallona nima shi na ke kallo.
"Har ka ƙoshi?
"Alhamdulillah"
Ya faɗa yana mai miƙewa sai kuma na ga ya koma ya zauna yana mai duba agogon fatan da ke tsitsiyan hannun shi na hagu, sannan ya sake ɗagowa yana kallona kafin ya kira sunana a kausashe.
"Sadiya"
"Na'am"
Na amsa ina kallonsa cikin natsuwa ganin kamar magana zai yi ganin yadda ya kira sunana.
"Kin yi mini laifi jiya kuma har na ji haushin ki. Amma sai na yafe miki kafin na kwanta saboda ba na so ki kwana da fushin Mala'iku a kan ki."
Sai na kasa mgana na yi jagale ina kallon shi.
"Ba zan hana yin magana ba saboda bakin ki ne. Amma ina so ki sani ni mijin ki ne, ki san irin kalaman da za ki riƙa amfani da su wajen mgana da ni, mijin ki ne ni ba kanin ki ko ɗan ki ba, bai kamata ina fara magana ki rufe ni da faɗa ba kina ta faɗin mganganu son ranki, daga karshe ma har zagina kika yi."
"Zagi kuma? Ni?
Na faÉ—a ina nuna kaina cikin zaro ido.
"E zagi ko ƙarya zan yi miki?
Ya faÉ—a yana kallona, sai na kasa magana na dukar da kaina ina fadin" Ni fa ba da kai na ke yi ba. Kawai na"
"Kawai me! Ai ni ne na ke yi miki maganana. Ya kamata ina magana ki ce mini jar uba!?
Ya faÉ—a yana mai kafe ni da ido sai ya karya lagona. Saboda na san ban kyauta ba amma na kasa magana ba.
"Kar ki sake, ba na so in kuma kina so ki ƙure hakurina ne to shike nan ki ciga ba. "
ÆŠagowa na yi ina kallonsa ganin ya mike tsaye alamun zai fita.
"Ka yi haƙuri."
"Na haƙura na faɗa miki ne saboda ki kiyaye."
"In sha Allahu."
Na faÉ—a cikin sanyin murya kamar ba shi ba sai na ga ya yi mirmishi ya matso ya É—an ramkwafa ya sumbaci goshinaa.
"Sai na dawo."
Na miƙe ina shirin masa rakiya da sauri ya saka hannuwan shi ya ma yar da ni zaune ya na faɗin" Ki gama ba sai kin yi mini rakiya ba."
"To sai ka dawo. Allah Ya ba da sa'a."
"Amin ki kular mini da kanki. Ke da Yumna."
Sai na gyaɗa masa kai, ina kallonsa har ya fice daga falo ya bar mini ƙamshin turaren shi, ina zaune a wajen na ji tashin motarsa da fitarsa sannan na ji karan jan get an ma yar an rufe, ajiyar zuciya na sauke sannan na cigaba da tura dankalin gabana nima sai na ji cikina ya tushe sai kawai na tattara na rufe ma su Baby in sun dawo makaranta su ci, da yake da safen ma ba su tsaya ci ba amma sun tafi da shi. Khalipa da Anwar amma Jidda tuni ta daina ɗaukan abinci ta ce na yara ne. Baby ce ba ta girma ita wannan uwar acicin ma ranar da ba ta je da abinci makaranta haka za ta dawo kamar ta ci babu.
 Bedroom na koma saboda na baro Yumna tana barci, wayata na ɗauka ina latsawa bayan na zauna a gefen gado Data na buɗe na shiga yanar gizo-gizo ina ganin abin da ke faruwa, waɗanda suka yi mini magana duk na amsa su yawancin duk masu oder hijabai ne da yake na kwana biyu ban kawo su amma ina haɗa kan kudaɗen hannuna ne, ko na salla babba ban saro hijabai ba, na dai saro su inners ɗin saboda ba ishashun kudaɗe a hannuna. Daga nan I. G na shiga ina ta kalle-kalle na sai da na gaji jin na fara jin barci sannan na ijiye wayar na kwanta ban tashi ba sai bayan azahar Allah ya taimake ni yau Yunma barci take sha ko tashi ba ta yi ba amma na san za ta taɓa kukan dare tun da ta yi barcin rana sosai haka.