Sashe 32
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Kar ka ce kuma za ka wanke ka bari su Ya Aina su zo don Allah.'
Sai ya ce minI to, sai da ya dawo ne na ce ya miko mini wayata, tana falon su Jidda ya je ya ɗauko ya kawo mini jikin sa na rawa. Jaririyar na jikinsa ya nace sai da na ba shi ita.
"Kar ta ɓata ma ka jiki. Kasan gogewa kawai na yi ba a yi mata wanka ba.'
"To ai jikin nawa ya riga da ya ɓaci ba matsala in ta ƙara ɓatawa"
Sai da ya yi magana na lura shima dogon wandon da ke jikinsa duk ya ɓaci da jini har farar vest ɗin jikinshi wa ya ga maza yau sun yi aiki.
Ya Aina na kira na ce mata ta zo gida na haihu.
"Ke Sadiya"
"Wallahi da gaske Ya Aina. Na samu ƙaruwan mace."
Sai ta yi kabbara kafin ta ce min gata nan zuwa domin na ce ta yi sauri ko yarinyar ma ba a wanke ba
Sai da na gama wayar na duba lokaci sha biyu ne da wani abu zai iya zama gab da sha biyun na haihu ko kafin ma.
Saboda na kira Ya Aina ya sa na matsa Yallaɓai ya je ya yi wanka jikin sa ya ɓaci.
"To ke da ita fa?
"Za mu yi in Ya Aina ta zo.'
"Amma za mu je asibiti a duba mini ku ko?
Sai na yi dariya kawai ganin yadda ya kama jaririyar ya rumgume.
"Za mu je asibiti mana. Ka je ka yi wanka kafin ta zo"
Da kyar ya ba ni jaririyar nan ya tafi ya yi wanka nima ya bar ni rumgume da ita har lokacin ina yi ma Allah kirari. Ina jin jini na zuba ta ƙasa na Allah ya sa na samu wani zani na tara a ƙasa na kafin na yi wanka. Na yi ta ma Allah kirari ina riƙe da kyautar da Ubangiji ya sake yi mini bayan na fidda rai. Ina ta hailala da kabarbari a cikin zuciyata domin Allah shi kaɗai ne wanda kum fa ya kum ne a lokacin da ya so a lokacin komai yake faruwa.
Ina nan zaune Yallaɓai ya fito wanka, yana ma saka kaya ne Ya Aina ta kira wayata da cewa ga ta nan a bakin get shi ya sa a gurguje Yallaɓai ya shirya ya fita ya je ya buɗe mata suka taho ciki a tare yana gaba tana bin shi a baya har cikin bedroom ɗina sai ga shi ta ganni a zaune gefen gado riƙe da jaririya ai sai ta riƙe haɓa kafin ta ce.
"Ikon Allah da gaske dai kin haihu?
Sai kawai na yi mata dariya ba tare da na yi magana ba.
"Wallahi Ya Aina ni kaina na yi mamakin haihuwar nan, abin da bai gaza mintina goma ba har ta haihu."
"Sannu Dubu. Sannu Dubu na ce barkan mu da arziƙi."
Ta faɗa lokaci ɗaya tana karɓan jaririyar da ke hannuna ni kuma sai na sakar mata ina faɗin" Yauwa Ya Aina."
Na faÉ—a ina mata mirmishi, gefena ta zauna a kan gadon ta na kallon jaririyar kafin ta ce" Ma sha Allah. Ga ta nan ko kamaanninki ta É—auko Sadiya"
"Shi ya sa na ce ta gama cin sunan Mama."
"In sha Allahu."
Yallaɓai ya ba ni amsa lokaci ɗaya yana kallona nima shi na kallah ina mai jadadda masa godiyata ta idanuwana. Ya Aina ko sai washe baki take yi cikin hamdala. Yallaɓai ne ya yi maganar tafiyar mu asibiti ya sa ta tashi ta ce bari ta saka ruwan zafi ta fara yi ma jinjirar wanka sai na ce akwai ma ruwan zafi a hiter ta tiolet
Sai ta ce to bari ta yi amfani dashi bam damu ba sanin duk abin da ya kamata za ta yi kamar yadda ta yi mini a haihuwan Baby ita ta yi jinyata a asibiti har muka dawo gida shi ya sa nake ganin ƙimar Yaya Aina ta na yi ma zumunci kara da jikinta da aljihunta.
Nan ta bar ni da Yallaɓai zaune mun ta sa jinjira muna kallo bakin mu ya ƙi rufuwa sai da ta ɗebo ruwan a baho sannan ta karɓe ta. Tas ta yi mata wanka bayan ta yi ta sauya ruwan Yallaɓai na faman kai da kawo, ta saba saboda in dai na haihu kaf dangina da dangin Yallaɓai sun san shi ba mai zama ba ne, da shi za a yi ta shiga da fita in na kamawa ne ya kama sai ya ga jama'a sun taru ne yake haƙura ya fice daga gidan. Na taɓa jin Anty Maimuna na yi masa tsiya a haihuwan Anwar wai yadda suka san shi da hidima a kaina in na haihu amma Gimbiya an mata aiki a asibiti ya bar gida kaca kaca bai iya gyara komai ba. A gabana ne ranar na je giden bayan an sallamota kai tsaye ya ce Sadiya kika ce, ba lalle abin da na ke yi a can na yi shi a nan ba. Sannan bai zama dole shima abin da na ke yi anan na je can na yi ba. Tana jin haka sai ta yi shuru ni ko a fili ma sai da na murmusa ban ji wani mamaki ba saboda sai da a ka yi mini kishiya na fahimci abu kaɗan ma da bai kai ya kawo ba in ba ka kai zuciyarka nesa ba sai kishi ya turniƙe ka.
Shi ya jawo mata akwatin da na haɗa kayan haihuwan ta shirya jaririyan cikin kayan sanyi masu kyau bayan ta shafe mata da man zaitun ta kuma gasa cibiyar sosai ta saka mata mgani saboda ta yi saurin faɗi, ta nannaɗeta cikin towel ta miƙa ma Yallaɓai da yake jira daman. Faɗa mini yake yi yanayin jikinta irin na Baby ne ƙatuwa ce mai kiɓa haka na haifi Baby kuma har gobe ta na nan da ɗan jikinta kuma wannan jikin na su Anty Bahijja ne ko na ce na Nene domin har yanzu da shekaru suka tura akwai jiki a tare da ita. Nan muka bar Yallaɓai Ya Aina ta iza ƙeyata tiolet ta kama mini na gasa jikina kuma sosai na ji daɗi a ciki ta bar ni ta fita zuwa kitchen ashe tea ta haɗo mini mai kauri da ƙwai sannan ta kawo min saban buredi ta bincika ta ga ma ina da garin kunu amma ba shi da yawa sai ta yi ma Yallaɓai maaganar gero sai ya ce in ya fita zai yi magana za a kawo.
Ko da na fito shi yake faÉ—a mino ya yi ma ta huÉ—uba da suna Rukayya bayan ya lasa mata dabino a bakinta.
"Allah ya raya mana Ruƙyyaatu Yallaɓai na."
"Na gode. Na gode. Na gode da wannan martabawan na ka. Ubangiji ya yi maka sakamako da wannan karan da ka yi mini."
Kafin ya yi magana Ya Aina ta dawo ɗakin tana tambaya ta omo sai na ce ta duba a dirowan kitchen duk da bai da yawa sai Yallaɓai ya ce in rubuta duk wani abu da ake bukata za a kawo anjuma.
Ta juya da nufin fita sai na kira ta ina faɗa mata Yallaɓai ya yi mata huɗuba da sunan Mama.
"Ma sha Allah. Allah ya raya mai sunan Mama. Allah ya sa ki biyo halin mai sunan."
Dukkanmh muka amsa mata da Amin Amin nan ta fice ta bar mu. Yallaɓai na riƙe da ita na shirya na saka wata doguwar rigana sai gashi ta shige ni, na ɗan ragu amma ciki na nan kamar ban haihu ba sai da Yallaɓai ya ce ko akwai twin ɗin Rukayya ne a ciki ba mu sani ba ina dariya na ce wani twin jini ne a ciki a hankali a hankali zai ta sauka amma zan ɗan riƙa ɗaure shi saboda koyarwa iyayen mu na da kenan ka riƙa ɗaure ciki a cewarsu in ka sake shi haka shi kenan zai bi jikin ka. Pamper na saka na tare ƙasana da shi sannan na zauna ina zaman ƙaryawa na biyu domin sai na ke jin kamar na shekara ne ban saka komai a cikina ba saboda yunwar da na ke ji ina tusa buredi a bakina ina kallon Yallaɓai na yi mata hoto.
"Yallaɓai ba ka sanar da kowa haihuwan nan ba fa."
"Zan sanar yanzu."
Ya faɗa yana ƙara yi mata wani hoton har yana wani karkacewa sai da na yi dariya. Ni dai ai na sha mamakin yadda na iya ta da jug guda da tea na kuma haɗa da ƙaton saban buredi na cinye ga ƙwai manya faifai biyu lalle a gaida Haihuwa domin wani abu sai haihuwa in ba haihuwa ba da cikin jego ba ina ni ina ta da wannan uban ruwan shayin? Haka na faɗa ma Yallaɓai da na ga yana kallona sai ya yi dariya kafin ya ce.
" Ni wallahi hankalina baya kan ki. Ban ma lura da aikin da kika yi ba. Na ce to sannu da aiki Umma Sadiya."