← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 103

Sashe 95

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya tambaya a daƙune ganin ya ji haushi ya sa na ce" Ni tsarin ne ya ba ni dariya wai ranar girkin ki da key ɗin turaka ki je ki gyara in kin fita ki rufe"
Shima sai da ya yi dariya  kafin ya ce" Maganin ƙorafi na yi. Kowa da turakanta magana ta ƙare."
To ni dai ko rawan jiki ban yi ba tun asali na tsani turakan miji wallahi, Shi ke nan Yallaɓai ya fara buɗa jiki in kina da girki sai dai ki bi shi har dining ya saka a bangaren na shi duniya sabuwa. Ni fa ranar girkina mantawa na yi na yi barci a bangarena da safe na tuna tsarin har abinci a can za ki haɗa masa ke fa can za ko tare sai kin fita girki ni ko na ce ba zan iya ba ya'yana fa. Yallaɓai ya ce to na yi ta kwana a bangarem nawa shi dai ya gama bin kowacce daƙinta tana yi masa yanga.

Ina gani Rabi'atu da Gimbiya ana gogawa. In suna da turaka aka kasa zaune aka tsaye. Rabi'atu in ranar ta ce ƙamshi turare har haraba. Ita da Salima kanwar Antyn tasu su zage a yi ta girke-girke. A sauya zanin gado a yi wannan a yi wannan haka itama Gimbiya sai suka koma suna gasa shi ko Yallaɓai na jin daɗi sun zaɓi dakunan su ni na karshe suka bar mini, na san dai in dai ranar girkina ne da safe zan je na gyara ko na saka Baby  ta gyara na kuma shiga ɗakin na gyara na wanke tiolet a bangarena na ke yi abinci na kwasa na je na jera masa bana yin wannan rawan jikin na su to Allah na tuba wani kuma dare ne jemage  bai gani ba  ai sai daran mutuwarsa? In muka kwana da asuba nake gudawa bangarena sai dai in zai fita ya biyo ni ranar har ce mini ya yi in bana son  kwanan nan ne na faɗa masa.

"Aa kawai dai ban saba ba ne wallahi ina jin wani iri."

Wani kallo ya yi mini kafin ya ce" Gwara ma ki saba malama turaka yanzu kika fara zuwa."
Shuru kawai na yi, ni bai san ban wani damu ba ta kaina na ke yi, duk da wannan rabawan da ya yi bai hana an samu matsala ba Gimbiya ta ce Rabi'atu tana ɓata kitchen da falo ba ta gyarawa haka take fita tun da can take girki, saboda da daga Rabi'atu sai ni ne daga baya abin ya birkice ni na dawo farko, sai Rabi'atu sai Gimbiya, rigima sosai sai da ya tsawarta musu da cewa zai kori kowa a turakan na shi sannan aka zauna lafiya bayan an yace kowcce ta zo ta ɓata waje ta gyara kafin ta fita ni ina gefe ban shiga ba ina ruwana na yi magana ya ce ina yi masa shissshigi. Na koma gefe na zama yar kallo tsakanin Rabi'atu da Gimbiya ne suke ƙwama film acikin gidan nan wani abun ma kamar ka yi ta dariya wani abun kuma hauahi ka ji kamar ka yi ta dukan su.

Cikin Rabi'atu har ya fito wata biyar amma ya yi girma sosai. Har ni kaina ina mamaki, sai da ta yi scan Yallabai ya zo bakin shi kamar  zai kai kunne yana faɗa mini an ce yan biyu ne a cikin Rabi'atu mace da namiji. Sai a lokacin ya ke faɗa mini wai maman Rabi'atu yan biyu ne namijinta ya rasu ne. Labarin yan biyu Rabi'atu za ta haifa kusfa kusfa Yallaɓai ya kai labarin nan da man fa yana da shegen surutu da faɗi ba a tambayeka ba. Gimbiya ko ta ce ya dai bar murna domin likita ba Allah ba ne, shi ko ina ruwan shi yana ta shirin haihuwa kamar an ce gobe ne ballanta yanzu da kuɗi suke huda shi ai komai ma zai yi.
Haka nan muke zaune muna gungura rayuwar mu, ba a sati Gimbiya da Rabi'atu ba su yi tsiya ba, kuma duk fa kan turaka da miji, ni wallahi har na gaji da baa su haƙuri na saka musu ido, kuma in dai aka yi sai Gimbiya ta zama mara gaskiya saboda ta cika ƙorafi da mgana ita kuma Rabi'atu wayau da bariki da haka take cutar da ita ba ta sani. Ni dai ba mai yi da ni Yallaɓan ma kan shi isata yake yi na tattara shi na bar musu ranar har mgana ya kwaɓa mini wai ya fahimci na koma gefe yanzu na yaye shi kamar ba mijina ba, ba na damuwa da al'amuran shi.

"Ba haka ba ne. Gani na yi bayan ni kana da biyu irina masu kula da kai."

Hararata ya yi kafin ya ce" Wato ina da biyu! Ai ko goma ne ina nan a matsayin mijin ki kuma dole a ce ma mijin iya Baba."

"Dole ne wannan"

Na faɗa ina masa dariya ganin ya shaƙa sai kawai ya jinjina kai yana faɗin"Na gano ki wato kin gama cin moriyar gangan za ki yada ƙwaron ta ko?
Dariya har ina faÉ—owa daga kan kujera.
"To wallahi ba ki isa ba."
Yallaɓai da karfi hali shi wai a dole ban shiga ana kishin sa da ni ba a raina na ce ba kuma zan tusa kaina ba, ai ni tun da na yi karatun namiji na daina ta yar da hankalina a kan shi.
Ya gaji da mitan shi ya haƙura domin ni kam ta kaina na ke yi, haƙkin shi dai ina ba shi ina iya bakin kokarina amma ba na rawan jiki da na ƙafa a kan shi. Na gama yin wannan tun a baya yanzu duk abin ma ya fita kaina. To jiya ai ba yau ba.

Siyayyya kayan haihuwa komai biyu aka siya dangin Yallaɓai kowa uwar biyu yake kiran Rabi'atu  da shi har Nene fa in ta kira waya sai ta ce ina uwar biyu? Na ce lalle duniya juyi juyi yanzu uwar biyu ce a layi ba mai farar haihuwa ba. Cikin Rabi'atu na wata bakwai ya yi ƙasa ga shi ya girma yana rinjayan ta, ba ta aiki komai da man daga kwanciya sai in za ta shiga makaranta ya ma hana ta driving shi ya ke kaita ko Sadi, Salima na nan tare da ita tana kula da ita amma da wannan ƙaton ciki ba ta fasa zuwa turaka ba tana ganin ƙya shin ta haƙura har sai ta haihuwa na ce yar wahala kawai in dai namiji ne ke ce a baya ba shi ba.  Danginta sun yi maganar a al'adansu gida za ta koma ta haihu megidan ya ce bai amince ba da kan shi ya zo yana faɗa mini na ce Allah ya kyauta ban san yadda suka ƙare ba daga baya ya ce mini in ta haihu an yi suna za ta je can Maiduguri ta yi wanka tun da sun matsa a raina na ce to ni ina ruwana? In na yi magana ya ce ina yi masa shisshigi ni dai iyakata Allah ya kyauta da Allah ya raba lafiya.

Ciki na kai wata tara ta daina fita ko'ina saboda ta yi nauyi ba sai an faɗa maka ba kana ganinta sai ka ce amma dai yan biyu ne acikin nan ko? Saboda girman shi ya yi yawa gaskiya Rabi'atu ta zama ɓukekiya ciki ya ma yar da ita babban mace. Edd ɗinta bai gama cika da kwana goma ba aka yi mata aiki ta haihu a wani daran jumma'a.  Da ya kama 13 Nov. 2023.
Ni Yallaɓai ya taso ina barci lokacin da ta fara naguda da man cikinta na shiga wata tana ya tara mu ni da Gimbiya ya ce zai riƙa kwana a bangaeen Rabi'atu saboda cikinta ya shiga watan haihuwan shi, ni dai ko a jikina na ce Allah ya ba da sa'a. Gimbiya ce ta ɗan nuna ba ta yadda ba ya shi ba yardanta yake bukata ba shi ya sa ba ma amfanin mganar tun da abin da ya  yi niyya ba zai fasa ba.

Ta kasa haihuwa da kanta sai da aka yi mata C.S an fito da jarirai biyu mace da namiji. Kwana muka yi zaume a asibitin nan ni da Yallabai da Salima sai da safe aka fito da ita sannan ya kikkira jama'a ya sanar da su. Da safen na koma gida ni na ke ma faÉ—a ma Gimbiya da yara Rabi'atu ta sauka an samu yan biyu. Su Baby suna ta murna, Sai da huta can da yamma na koma asibitin Gimbiya ta ce mini sai gobe za ta je shago za ta leka.
Ko da na je asibiti ta cika makil da dangin Rabi'atu da na Yallaɓai su Anty Bahijja  ana bakin gadon mejogo ana ta yi ma jarirai hotuna. Faɗi take yi an yi haihuwan da ba a taba yi a gidan Tafida ba haka ta yi posting ma a status. Shi kan shi angon ƙarnin ya kasa sukuni ina jin all contact ya yi wajen tura sakon an yi masa haihuwa saboda yadda yake yini amsa wayoyin yan barka.
Washegari tare muka koma da Gimbiya da yamma da yara ai ko ta sha mamakin ganin su Anty Maimuna ana ta rawan ƙafa a gabanta ma sun sake faɗa an yi ma Tafida haihuwan da ba a taɓa yi masa ba ta cika ta yi fam har tana ba su amsa da cewa sai dai a kira su da ƙannen su Khalipa Anty Maimuna ta ce ta yi mata rashin kunya ba aure gare ta ba ta san ita kanwarta ce dukan tsiya za ta yi mata suka bar Gimbiya da tura baki tana ƙwalla ni dai ban tofa ba amma da man na san wata rana itama za ta ji irin abin da na ke ji a can baya.
Chapter 95 · 0% Book details