← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 103

Sashe 26

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni dai ban samu na furta ma kowa yanayin da na ga Ma'u ba har muka kai Yallabai gidan Zaintuna ya yi mata gaisuwa mu can ya bar mu ya wuce.
Da ya ke ba nisa. Ya Abubakar ya siya wani ƙaramin gida a can ƙasan layin gidanmu shi ya sa sai suka dawo kusa.
Mu na gidan sai bayan la'asar muka koma gidanmu. Nan ma ana ta shigowa maƙota da abokan arzuka duk wanda ya zo sai a yi masa kwatancen gidan Zaituna. Ya Murja da Ya Aina su suka yi abincin rana tun da akwai mutane.
Muna gidan har dare ni dai da wuri na tafi bayan mangariba Yallaɓai ba gidana yake ba, sai da muka koma ya kira ni ya ce zai zo ya ɗauke mu na ce mu kan muna gida.

Washegari ma ban jira shi ba. Tun safe na ta da Jidda ta taya ni muka dafa abinci shinkafa da wake muka saka a babban kula ƙarama da babba.  Babban a ɗakin Gwaggo karamar kuma na ba ma su Jidda su ka kai gidan Zaituna. Ƴan'uwan Yallaɓai duk sun kira sun yi mini gaisuwa da ya ke Yallabai in wani abu ya faru na jaje ko na murna ya kan saka a group ɗin su. Ranar biyu Hauwa da Munnira suka zo mini gaisuwa. Sai ranar da a ka yi uku Gimbiya ta zo lokacin ma ta iske su Suwaiba da Jamila sun leƙo mun gaisuwa. Shi ya sa ba ta wani daɗe ba daga ita sai Anwar Suwaiba ce ma ta tambayi  Khalipa sai ta ce ta baro shi a can Rano. Ni dai ban ko tambaye shi ba tun da ba ta ma wani daɗe ba ta ce za ta tafi na yi mata rakiya har waje. Ta zo da mota har ta rage ma su Suwaiba hanya zuwa Gwamnaja. Na ko ga sabuwar motar ta a fili ma ɗaukan ido take yi.

Bayan an yi uku ne ban sake komawa ba sai ranar da biyar. Ranar lahadi kenan da su Ya Hamza suka zo ba su kwana ba a ranar suka koma. Shi daman Ya Auwal ya ɗan zo yin wani abu ne a reshen su na nan Kano kuma ba shi kaɗai ya zo ba shi ya sa bai jima ba ya tafi da cewa daga can kawai za su koma Abuja ne. Kuma tun daga ranar ban koma ba sai ranar bakwai a gidan Zaituna, muka zauna a ranar su Inna Mariya suka zo gaisuwa an manta da su sai da Amina da ke kaduna ta kira wayar Inna ta faɗa mata. Da suka zo tana ta faɗa ni dai na ba ta haƙuri na ce wallahi an sha'afa ne. Matar Kawu Tasi'u ta zo da fanke da yawa na sadaka sai bayan la'asar suka tafi. Dukkan mu muna gidan har Ma'u da ranar ba da wuri ta zo ba ashe ba ni kaɗai na fahimci Ma'u ta susuce ba sai da Rahila ta yi mini mgana.

"Sadiya wai Ma'u ciwo ta yi ne?

Ta ke tambayata sai na kalleta kafin na ce" Ni ko ta ina zan sani? Nima dai haka na ganta duk a firgice tun ranar da a ka yi rasuwar na."

Rahila ta jinjina kai kafin ta ce" Nima wallahi na tun ranar na lura. Kamar wacce ta yi jinya duk ta firgice."
Sai na jinjina kai ina ƙara kallon Ma'u. Wallahi har idanuwanta sun zumar ma. Sannan na daina ganin Zainab ƙanwarta da ke wajenta ko ta koma gida ne oho? Sannan ba ta ma zo da yara ba tun da a ka yi rasuwar ita kaɗai take zuwa ba. Kuma ban ga Alhaji Mustapha ba na ji dai a bakin Ya Aina ranar da a ka yi rasuwar da shi a ka yi jana'iza.

Duk da ba na shiri da Ma'u na ji na damu da ganin yanayin ta. Na tuna a shekaran da ta wuce na taɓa zuwa gida Alhajinmu ya kirani yana mai tambaya ta.
"Kina zumunci da Æ´ar'uwan ki Asma'u kuwa Dubu?
A lokacin ban ɓoye ma Alhajimmu komai ba gaskiya ta na faɗa masa.
"Ina dai yi maka kara Alhajimmu. Ina gaisheta in mun haÉ—u sannan in abu ya kama na jaje ko na murna ina yi mata."

"Kin kyauta Dubu. Kin yi mini kara sannan kin yi ma zumunci kara."

Daga lokacin bai ƙara matsa mini ba. Tun da dai ya samu tabbacin ba ma gaba da juna. Nima hakan ya fi mini tun da yanzu na samu sauƙin ta. Sai yanzu da na gan ta sai na fahimci itama ta na can tana fama da kanta ne. Ko da ga ganin yanayin ta wani al'amari ne mai girma ya gigita tunaninta Ma'u  fa macen da ba komai yake razanata ba. Ba a cika ganin gazarta ba amma yau na ga kasawa a yanayinta da idanuwanta.

Ashe ba ni da Rahila duk muka fahimci Ma'u ba ta hayyacinta ba har da Ya Aina da Ya Balki. Ita dai Ya Balki Zainab ta fara tambaya da yara sai Ya Murja ta amsa da cewa Zainab ta je ganin gida. Su Alhaji ƙarami kuma suna gidan iyayen Alhaji mustpha sun je hutu.

"Oh shi ne na ga Ma'un duk ta yi wani sanyi haka? Kewar yaran ce?

Ya Aina ta faɗa cikin zolaya. Ma'u yaƙe kawai ta yi ta kasa mgana.
Ina lura da Ya Murja ta na son mgana amma kuma sai ta fasa yi shuru.

"Wai ni kam ina labarin Shema'u? Na daÉ—e ban ganta ba ina jin tun auren ta."

Sai Ma'u ta rausayar da kai kafin ta ce" Tana can Gombe. Mijinta kulle yake yi mata."
"Kuma ba ta da ciki?
In ji Rahila.
"Ba ta da ciki gaskiya."
Ta faÉ—a a sanyaye ni dai kallonta kawai nake yi. Maganar Allah Ma'u ta rame ko ni kaÉ—ai ke ganin ramar na ta? Na faÉ—a a cikin raina.

"Shi ya sa ba ta yawan zuwa kenan." To Allah ya zaunar da ita lafiya da man wasu mazan akwai kulle. Kuma itama Shema'u sai da haka in da ya bar ta da duk sati za ta iya zuwa Kano a shirmen ta."

Sun cigaba da tattauna mganar Shema'u. Ma'u na gefe ta yi tagumi ta yi shuru da ga gani ta shiga zurfin tunani kamar ba zan yi mgana ba sai na muskuta da cikina a gaba. Wata doguwar riga ce a jikina da na saka a ka ɗinka min su bubu tun da duka kayana sun yi mini kaɗan. Sai na siya yaduka da ƙananun atamfofi na ba da a ka mini ɗunkunan masu ciki su na ke sawa ina jin daɗin su.

"Wai ni kaÉ—ai na lura da Ma'u duk ta rame?

Na faÉ—a ina kallon su Ya Aina sai suma suka kalle ni sannan suka koma suna kallonta duk sai ta tsargu.

"Nima wallahi na lura. Ba har na yi magana ba ranar."

Rahila ta faɗa, Ya Aina ko sai ta yi shuru kafin ta ce" Ni kaina na ga haka tun kwanaki da na ganta. To na yanzu ma abin ya ƙara lalacewa idanuwanta duk sun zurma"

"To ko ciki ne da ke Ma'u?

In ji Ya Balki. Sai Ma'u ta kasa mgana ta dukar da kai tana wasa da kwalliyar material É—in rigar da ke jikinta.

"Ma'u me ke faruwa da ke ne? Mu Æ´an'uwan ki ne. Kina ganin bai kamata mu san matsalar ki ba?

Kawai sai Ma'u ta saka kuka. Ni fa har ina buɗe baki saboda mamaki. Na daɗe ban ga kukan Ma'u na haƙika ba sai ranar. Duk sauran kukan  da na saba gani na makirci ne amma na yau na gaske ne fitowa yake da sauti daga ƙarkashin zuciyanta.

"Subhanallah me ya faru Ma'u?

Ya Balki ta faÉ—a. Ni da Rahila ma mun kasa magana. Ganin yanayin Ya Murja ya sa na san ta san abin da ke faruwa.

"Ya Murja fa ina ganin ta san wani abu."

Na faÉ—a ina kallon su Ya Aina duk suka mai da kallon su kan Ya Murja.

"Murja me ke faruwa?

Sai ta kalli Ma'u kafin ta ce"Uhm aure Alhaji Mustapha zai ƙara. An kusa karshen shekaran nan."
Yadda na zaro ido kamar na ga wani abun tsoro
Kowa sai jikin sa ya yi sanyi. Duk da ba na son Ma'u itama ba ta so na amma jini ya yi aiki a kaina wallahi na tausaya mata matuka. Kishi bala'i ne ba wanda ke gane yanayin sai wanda ya faru a kan shi. Ni da ya ke Victim ce ai na san irin yanayin da take ciki.

Na ji na ƙara tausayinta da Ya Murja ke faɗin karamar yarinya ce yar sha takwas zai aura kuma sai da a ka saka ranar ta ke ji bakin Uwargidan shi. Matsaloli da dama yanzu ya daina ma rawan jiki a kanta da ta yi masa mgana bai faɗa mata sai da suka yi tsiya har ya ce in ba za ta iya zama ba ta tafi shi bai hana ta ba ashe  gurmu a ka yi har sai da Baaba ta zo garin nan amma Alhajinmu bai sani ba. Itama Ya Murja ta ce faɗan su na biyu ne Ma'un ta zo gidan ta, ta na kuka shi ne ta san abin da ke faruwa ita da mijinta suka mai da ita. Yadda ta ke faɗa yadda Alhaji Mustapha ya ɗauko auren nan to uwarsa ce kawai za ta ce kar a yi ya saduda. Amma ba Ma'u ba ya ce ko za ta mutu sai ya yi auren ita ba a aure ya aure ta. Yadda Ya Murja ta ce Ma'un ta faɗa mata ita uwargidan sai daɗi ta ke ji tana ƙara zunguran Alhajin da maganar auren.

"To daman me zai dame ta tun da ba ita za a yo ma wa ba?

Na faɗa ina jin wani motsa daga ƙasan zuciyata. ta ba ni tausayi kishi ai masifa ce.

"Haka ne. Amma ita ma Ma'u ta kwazzaɓi kanta tun da ta san ba zai fasa wannan auren ba, me ya sa ba za ta kwantar da hankalin ta ba?
Chapter 26 · 0% Book details