Sashe 19
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba mu isa gida ba sai bayan Mangariba kuma suna ijiye mu suka juya zuwa Kaduna. A gidan Anty Bahijja muka sauka tun da ita ce uwar biki ya kamata ta ga dawowar mu, amma ba domin haka ba gidana zan wuce na gaji sannan kasala duk ya rufe ni, tun da muka je ban ci wani abincin kirki ba. Na yi amai duk na galabaita barin ma yau ɗin amma ban ƙi sauka ba. A na ta yi ma na maraba da dawowa muna zaune dukkan mu a falon Anty Bahijja a na ta mai da yadda a ka yi a can Kaduna. Maman Farko na ta faɗin Sulaihait ta yi dacen surukai masu dattako sai fatan zaman lafiya sannan ga labarin kyautar ban girman da a ka yi ma na Anty Bahijja sai faman washe baki take yi. A raina na ce wato kowa na son na shi ya je ya ji daɗi. Amma ta na takura ma wasu in ta ga suna jin daɗi lalle wanzami daman a ka ce ba ya son jarfa.
Tun da muka sauka kowa na ta zuwa mana sannu da zuwa. Tun da akwai sauran jama'a a gidan har Hauwa a gidan muka same ta. Ni ban ma san Gimbiya tana gidan ba sai da na fara ganin Khalipa. Ban ga Jidda ba sai Baby ita ke faÉ—a mini Jidda na gidan Gwaggon su Zuwaira. Bedroom É—in da ke falon Anty Bahijja na shiga domin na kama ruwa na yi salla ina shiga na ga Gimbiya ta fito daga cikin tiolet É—in cikin É—akin É—auke da Anwar kamar ta wanke masa kashi ne tun da na gan shi ba pampers. Ina ganinta na washe mata baki ina faÉ—in.
"Maman Khalipa ashe kina gidan?
Amma sai matar nan ta yi kamar ba ta ji ni ba, gani ni da ita a cikin É—aki ban dandara ba na sake faÉ—in.
"Mun dawo yanzu ba daÉ—ewa a na ta hira a falo ban gan ki ba."
Na saki baki kawai ina bin ta da kallo domin zuwa ta yi ta raɓa ta gefe na ta fice daga ɗakin kamar ba ta san Allah ya yi ni a tsaye a wajen ba. Har ta na banko ƙofar a saman fuskata bam! Jikina ya yi sanyi ban san adadin sakannin da bakina ya yi a buɗe kafin na rufe shi ba. Jikina a sanyaye na shiga tiolet na yo alwala na zo na yi salla da hijabin da na samu a cikin wardrope ɗin ɗakin ina jin na Suhailait ne domin ɗakin nata ne kafin aure ya tashe ta.
Ina idarwa na fito da niyar na ce ma su Munnira ni zan ta fi gida. Sai kawai na ga Gimbiya suna mgana da Naja. Kamar zan wuce na ƙyaleta sai kuma wata zuciyar ta ce na yi mata mgana na ji ko na yi mata wani abu ne da zan yi ta mata mgana tana mini wulaƙanci.
"Anty Sadiya ba dai tafiya ba?
Naja ta faÉ—a ganin na taho in da suke tsaye a gefen falon suna mgaana. Tana ganina ta wani haÉ—e rai kamar ta ga mutuwarta.
"E yanzu na ke son tafiya ba na jin daÉ—in jikina ne."
"Gaskiya sannu. "
Ta faÉ—a sai kuma ta juya tana ce ma Gimbiya."Amai ta yi ta yi a can wallahi."
Ban san ko maganar ta suɓuce mata ba ne, ko kuma daman da niyya ta faɗa ban sani ba sai ji kawai muka ji ta ja wani ubn tsaki kafin ta ce.
" Mtswww to ina ruwana ni dai mu cigaba da zencen mu. "
Ba ni kaɗai ba hatta Naja sai da ta ji wani iri ina kallonta ta na ma Gimbiyar mgana da ido. Ni ko da farkon da na zo wajen har na sauya shawara na wuce kawai ba tare da na yi mata mgana ba tun da na ga da ta ƙara ganina ta haɗe rai amma kalamanta na yanzu su suka ɓata mini rai ya sa na ce sai na yi mata mgana.
"Amma ko dai ba ruwan ki ai mgana mai daÉ—i ma Sadaka ne in ji Annabi(SAW)"
Na ma yar mata da martani ina kallonta sai ta wani ɗauke kanta sama jikinta na jijjiga irin ƙiris take jira ɗin.
"Don Allah ki yi haƙuri Anty Sadiya."
Naja ta faɗa ta na kallona na so na danne zuciyata na yi haƙurin amma sai Gimbiya ta ɓata komai.
"Mi ye na wani ba ta haƙuri an yi mata wani laifi ne?
Ta faɗa tana mini yatsina. Na ga rainin hankali a lamarin Gimbiya fa ya fara yawa tun ina hakuri tana ƙure ni daman kuma tun da na samu cikin nan a wuya na ke abu kaɗan ke ɓata mini rai ina kiyaye mata sabo ni ba sa'ar yin ta ba ce wanda ya ijiye mu ni shi ne daidai da ni tun abun na mu na mu uku ta ja sai da mutane su ka far ga da abin da ke faruwa domin ni dai ba zan yi shuru ina kallonta ta na so ta ci kasuwa a kaina ba.
"Ba ko a yi mini laifi ba. Amma ina tunanin wata ƙila ni na yi miki laifi tun da tun shekaranjiya in muka haɗu a gidan nan in na yi miki magana sai ki yi kamar ba ki jini ba yau ma ban dandara ba ina ganin ki na yi miki mgana kika yi banza da ni. Ni ko Gimbiya me na yi miki da zafi haka? Me na yi miki da ya sa kike jin haushina?
Kawai sai matar nan ta fara ɗaga murya tana faɗin" A a malama ɗan dakata ba na son sharri ni yaushe kika yi mini mgana ban amsa ki ba? Ai ko sai dai in ban ji ki ba. Ni dai ki tsaya da mganar nan a nan ahto domin kar ta je gaba. Yanzu sai ki ji magana a gaba ana ƙokarin ɗora min jarkar tsaba."
Naja na yi mata mgana amma tana mini rashin kunya har ta na wani ƙara yarfa hannu tana cigaba da faɗin" To Naja haka kurum ina cikin zaman lafiyana ta jawo mini wani masifan. Yanzu nan sai ki ji mgana ta kai kunnen Daddy shi kuma da yake ba ta laifi a wajensa ya hau ni da faɗa. To ba na so mganar ta tsaya iya nan, maganar kin yi maganar na yi banza da ke ban san an yi haka ba wataƙila lokacin da kika yi mini maganar ban ji ba ne."
Ai sai na ma kasa mgana sabida mamaki lokacin har su Munnira sun zagaye mu suna tambayan ba'asi ita kuma Gimbiya Naja na janye ta tana ba ni haƙuri tana ce ma su Suwaiba ba wani abin faɗa ba ne na ce ne na yi ma Gimbiya mgana ta yi banza da ni sai ita kuma Gimbiyar ta ce ba ta ji ba ne. Amma ba faɗa ba ne.
"Ba faɗa ba ne ta ke faɗa minI kar na kai mganar gaba? Wato ga munafuka ko me? Kin taɓa jin wani abu ya faru Yallaɓai ya ce daga bakina ya ji? Ina ruwana da sha'aninki da za ki tsaya a gaba na balle na riƙa hirar ki da miji? Kina gidan ki ina gidana me ye haɗina da ke! Ni ma sha'anin gabana ya isheni ba ni da lokacin wannan sannan ban gane kin ce wai ni daman ba na laifi a wajen shi ba? Me kike nufi? Sannan kina nufin ni zan yi miki ƙarya ne Gimbiya? Na ci riban me? Ke ma kan ki kin san ba ki isa na yi miki ƙarya ba domin isar ki ba ta kai har haka a wajena ba"
"Sadiya me ya faru?
Maman farko da tambayeni lokacin da ta ƙariso wajen ina ƙoƙarin magana kawai sai Gimbiya ta buga shewa tana faɗin" Ahayye. Shi ya sa na ga kin yi ƙutun ƙutun kin tafi Kaduna. To ina fatan kin je kin ciwo abin da ba ki taɓa ci ba ko?
"Ke Gimbiya me ye haka?
Anty Maimuna ta faÉ—a tana shiga tsakanin mu.
"Ba dai rashin kunya za ki yi ma Sadiyar ba ko?
Anty Zabba ta faÉ—a. Hauwa ko rike ni ta yi tana cewa kar na ce komai Munnira ko faÉ—i take yi" Jaruba wallahi kika ce za ki yi ma Sadiya rashin za ki daku a falon nan wallahi."
Wata shewar ta buga kafin ta ce" Ko ita ba zan da kun mata ba. Ballatana ku yan koren ta."
"Haba Saudatu"
Maman Farko ta faɗa kamar ranta ya ƙara ɓaci Anty Bahijja ba ta wajen daga baya a ka kirata ta zo dai dai lokacin da Munnira ke sa'in sa da Gimbiya.
"Ni kaina ba kai isar da zan yi sa'in sa dake ba. Ballanata Sadiya ta fi ƙarfin ki. Kuma Kaduna ta je ke ma ya sa ba ki je ba? Kin ga kenan isar ki ce ba ta kai ba ita kuma da na ta isar ya kai miji ya sahale mata ta je duk shi ne haushin na ki? Sorry ki yarinya mijin wata kika aura dole ki zamo ta baya ko kina so ko bakya so. Kuma na san duk wannan kumfar bakin da kike yi ba a kan tafiyar mu Kaduna ba ce, haushi ne baƙin ciki kin ji labarin Sadiya na da ciki sannan Tafida na ririta ta shike nan sai hassadarki ta motsa wato kin so ne ke da kika zo kika aure mata miji sannan kuma ki zama ke ce ke ta haihuwa ita kuma ko oho ko? Sai ga shi ba ke kaɗai ke da Allah ba. Ubangiji na kowa da kowa ne. Ta samu ciki kin kasa ɓoye hassdarki shi ya sa kika zo za ki yi ma mutane rashin kunya. To ba sa'an ki anan kuma duk tsiya dai a baya kika zo sai da aura ta rage sannan kika samu."
"Ke Munnira"
In ji Anty Bahijja. Maman Farko ba ta yi magana ba Anty Maimuna ce ta ce" Munnira ke ba za ki ba da haƙuri ba sai hura wuta! Wallahi kar na ƙara jin bakin ki"