Sashe 96
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanan Rabi'atu shidda a asibiti aka sallamota suka dawo gida. Yayenta biyu sun taho daga Maiduguri da kanwar babansu Yakumbo ita za ta zauna da ita har bayan suna. Gida fa sai kamshin masu jego, an shirya suna gagarumi tun da haihuwa ce da ba a taɓa yi ba. Kuma mun ga haka mukan mu kowaccen mu 100k Yallaɓai ya ba mu ni da Gimbiya na fitar kayan suna. Jidda ma ta zo gida lokacin ai dole ta zo Yallaɓai fa haka ya dinga kiranta wai ta zo gida ta ga k'annenta yan biyu. Kuma yara sun ci sunan Sulaiman da Aisha. Ya cika alƙawari ya yi ma Alhajinmu takwara. Alhajinmu ko har gida ya taho barka ya kuma turo Gwaggo. Tun da an yi ma ubana takwara ai dole na ware kudi na yi hidima cikin kuɗin da ya ba ni ne na siya ma yaran riga da pampers uwar kuma atamfa na yi mata. Gimbiya dai kayan jarirai kawai ta yi ni kuma ba ni da da man zillewa Yallabai ya gama yaɗa ma Duniya Alhajinmu ya yi ma takwara shi ma can Alhajimmu ya gama yaɗawa shi ya sa kaf yan gidanmu sai da suka zo barka na nesa su Amina suka kira waya.
 Sa guda Yallaɓai ya gada da raguna biyu, shagalin suna abinci ma daga reataurant aka dafo shi. An yi kayan rabo su robobi jaka memo da hotunan yara, Jidda dai ta yi kayan fulawa su cake da donut uban kuma ya ba da kuɗi ta yi har da cake, Rabi'atu kuma ta shiga ta fita da kayan alfarma. Ni dai kala biyu na saka da man ina da su Gimbiya ko da man tana da sutura ina tunanin ba ta yi ma sabon ɗinki ba. Yan uwansu na Maiduguri ba su zo da yawa ba gaskiya saboda nisa sai dai dangin Yallaɓai ne suka cika gidan har da mai kiɗan kwarya su Halima suka kira suka cashe, wata zabiya cikin masu kiɗan ƙwarya tana waƙe mai jego.
"Ina mai jegon ta ke ne? Rabi'atul badawiyya farar mace alkyabban mata. Farar mace fitilar gida. Amaryan Yusuf mai yan dubu dubu kin iya haihuwa da kika tashi biyu kika haifa ki shigo fili ki taka domin yau ranar ki ce"
Anty Maimuna ta fito da maijego suna ta mata barin kuɗi sai ga Yallaɓai ya zo gidan zabiya na ganin shi hau yi masa kirari.
"Ga ni ga Alhajin Naira. Alhaji yusuf angon Rabi'atu mijin fara baban farare. Mijin mai kyau daga Maiguduri, uban biyu kake dole dai a ce da mijin iya Baba."
Nan fa Alhajin naira ya zaro bandir ɗin yan dubu dubu yana ta ɓari waje ya ruɗe da murna da ihu. An yi hotuna mai hoto kam ya haska ya fi kala ɗari, mu dai muna gefe muna mirmishi in ka yi baya ace kana bakinciki Gimbiya tana bangarenta ma ba ta fito ba. Su Anty Bahijja sun kuma haɗa ma Rabi'an kayan suna ya kai atamfa goma ga kayan jarirai ga kuɗi, Mimisco kanta da ba ta kasar suna spain ita da megidanta super ta aiko Naja da shi da less mai tsada. Ana ta ɗagawa ana yabawa, Baban biyu ma ai ya yi wasa da naira yana da shi yanzu komai ma zai yi ba ya ƙya shi.
An yi suna lafiya an gama an yo soye soye kuma duk sun ba mu domin lokacin ma da suka gama sai da suka kirani na ce su dibar ma mejego da mijinta sai na bangaren su da namu bangarem mu dai yan gida gabaɗaya suka dibar mana da yara na dangin Yallaɓai Gwammaja akai tare da yaji mai yawa da turaruka. Na Yallaɓai kam har naman sai da ya kai ma Alhajinmu da kan shi na sunan takwaran shi kuma Alhaji shima za a riƙa ce masa. Alhajinmu haka ya zaunar da ni da na je yana yi mini faɗan na zauna lafiya kar ya ji kar ya gani na zama silar tashin hankalin mijina ai ba ni da ta cewa. Yallaɓai ya gama kama Alhajinmu a hannu da makircin su na maza
Macen kuma Ayush za a riƙa kiranta. Tariq ya zo ya ga jarirai ya yi barka haka ma Kawu. Abokan aikin Yallabai duk sun zo barka shi ya sa sai bayan suna da wajen kwana goma Rabi'atu da y'anuwanta biyu da Yakumbo suka bi jirgi zuwa Maiduguri sauran kuma suka bi motar haya da kaya. Sun yi mana sallama da za su tafi muka rabu da faɗin Allah ya sa mu gana.
Tun da Rabi'atu ta tafi sai da ta yi wata biyu a gida sannan Yallabai ya je ya kwana biyu suka dawo tare. Su Alhaji sun yi kiɓa ɓulɓul kamar Yumna tana ƙarama sai dai su farare ne irin su uwar su, bayan ta dawo kuma ta fara ɗan zaga gidajen dangin miji ga shi kuma da man karatunta ma ya tsaya na ji Yallaɓai na faɗin diparing za ta yi. Rabi'atu ta dawo da sarkan ƙafa na kwalliyar mata da hudun hanci Yallaɓai kuma ya ce ya yi mata kyau ta yi kiba ta ƙara yin kyau sannan ta dawo s da wata yarinya Zafira ɗiyar yayarta ce wata kila a wajenta za ta zauna megidan dai bai ce mana komai ba.
Satin da ta karɓi girki Yallaɓai kamar zai yi hauka saboda rawan ƙafa, har zuwa ya yi ya same ni wai tun da ta daɗe ba ta nan mai zai hana mu bata sati ɗaya na ce ni na bata sati biyu ma sai dai Gimbiya. Itama ban san Aljanun sukunin da suka shiga kanta ba ta ce su yi ma wata ba ta damu ba ina ga itama ta fara dawowa daga rakiyan Yallaɓan ne shi ya sa aiko ya ji daɗi suka yivta gwangwazan amarci, daɗin da ya ji ne a watan ya sauya ma Gimbiya sabuwar mota balle ma mun shiga sabuwar shekaran 2024 harkoki suna ta budewa. Yallaɓai yanzu sai godiya ya samu kwangila ginin wani kamfani a zaria zai je ya yi kwana biyu ba kwana kwana ya ce Rabi'atu ta raka shi muka ce Allah ya tsare baban biyu da uwar biyu sun fi kwana huɗu sannan suka dawo Jidda ta ce sun kawo mata ziyara ita yanzu ajin ta uku a Jami'a Baby ce ke SS3 Yumna da Ammar tuni an saka su a makaranta.
Watan su Ayush shidda Gimbiya ta fara laulayi da azumin watan ramadana ashe ciki ne. Bawan Allah ya yi ta murna domin Yallaɓai na son yara a rayuwan shi. Nima yana ta mini dan biki wai ban gama sai na ƙara ko ɗaya ne, ba ni da sanin gaibu amma sai na ke jin kamar na gama haihuwa tun daga kan Yumna. Itama Gimbiya cikin na ba ta wahala kuma tabbas itama ya kula da ita amma fa uwar biyu da biyunta dabam suke, su ke shan sharafinsu na ɗauka son da yake yi ma su Khalipa na daban ne sai da biyu suka zo na gane su Khalipa ba su ga komai ba in dai gata ne.
*Janafty**Ƙarshe*
Yau ta kama asabar ɗin karshen mako ne tun bayan da na idar da sallar asuba na koma barci kamar ƴar maye, sakamakon a gajiye na ke, wancan satin muka yi bikin yar gidan Ya Aina ƙanwar Marwa ta biyu, tun da satin bikin ya kama ba mu huta ba muna ta zirga zirga da shirye-shirye, sannan Amarya Katsina muka kaita ni da Ma'u da Rahila muka je, bayan mun dawo kuma aka yi mana rasuwa a Yashe ƙanin Muntarin Rahila ne ya rasu magidanci kwanan mu uku acan sai jiya da daddare muka dawo, na kuma dawo gidan na iske Yallaɓai baya nan yana Abuja kan wani project da man mun yi mgana a waya ya ce mini sai yau asabar yake saka ran dawowa.
Barcin gajiya na ke so na yi shi ya sa ma da safe da Baby ta ce za su je Gwammaja su yini na ce ta tattara yaran su tafi gabadaya. Yan biyu kaɗai aka bari wajen uwarsu, Gimbiya kuma ba ta fita kwana biyu megidan ke faɗa mini ta yi ta fama da zazzaɓi sannan itama da ta kira ni ta ƙara yi mini gaisuwa na ji muryanta shake nan take ce mini ba ta da lafiya mura da zazzabi. Jiyan dai da na dawo sun shigo ita da Rabi'atun sun yi mini barka da dawowa.
Su Baby na tafiya na rufe kaina a ɗakin barcina na kuma kashe wayata na kwanta ina ta barci ban san meke faruwa ba sai da na ji ana ta buga mini ƙofar bedroom lokaci ɗaya ana kiran sunana.
"Umma"
Can a cikin barci na ji buga ƙofar bayan na ɗan motsa sai kuma na ji kiran sunan nawa, da hanzari na miƙe zaune ina mutsike idanuwana.
"Maman Jidda"
Na ji an sake kira sai na diro daga saman gado ina laluban hular da zan rufe gashin kaina, ina kuma tunanin waye? Kamar ban É—au muryan ba.
"Waye?
Na faɗa ina isa kusa da kofar, hannuna guda ɗaya ina ƙara tusa gashin kaina da ya hargitse cikin hulan da na sanya yanzu yanzu.
"Ni ce"
"Salima?
Sai da ta ce ita ce na ganeta.
Na buÉ—e kofar lokaci É—aya ina kiran sunanta.
Salima ce ƙanwar Rabiatu.
"Lafiya kuwa Salima?
Na fada cikin mamakin ganin ta har ƙofar ɗakin barcina abin da ba ta taba yi ba iyakarta falo ko ɗakin Baby.
"Anty Rabi'atu ne da Maman Khalifa suke faÉ—a."
Ta faɗa tana haƙi, ai sai na yi sansarai domin kamar an mantar da ni ma ko su waye sai daga baya na fahimci mganarta.
"FaÉ—a? Innalillahi a ina?
Na faÉ—a ina yin gaba sai da ta biyo bayana lokaci É—aya tana faÉ—in" A can bangaren Maman Khalifa."
Ban tsaya ko saka takalmi ba, daga ni sai rigar barci Allah ya taimaka ma doguwa ce, kuma tana da kauri haka na fito haraba na kwashi gudu zuwa bangaren Gimbiya Salima na bin bayana hankalina a tashe.