← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 103

Sashe 56

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da ya yi magana na tuna da karyan da na yi masa.
Da sauri na ce" Ban fito ba. Na kira su Hauwa sun ce mu bari gobe da safe kawai."
Bai ce komai ba ya ce Allah ya kaimu. Ni ban kira su Hauwa da na yi ƙarya da su ba, washegari da safe da ya bar gidana asibitin ya fara biyawa sai ya iske Hauwa ni ina na sani ba sai da Hauwa ta kirani tana cewa.

"Sadiya me kika faÉ—a ma Tafida? Mun haÉ—u a asibiti yana ce mini ya na taho na bar ki alhalin kin ce masa tare zamu zo.'

"To sai kika ce masa me?

"Na kasa mgana. To ni me zan ce?

Na ciji yatsa kafin na ce" Kash! Kin kwafsa mini. Nan na ba ta labarin abin da ya faru.
"Ni fa ban yi niyyar zuwa ba ne"
"Ki tura mata Aniyarta ki zo ko saboda Yallaɓan."
"To bari dai mu gani. Zan je na yi barka amma ba zuwan da na saba yi a da ba."
Da muka gama waya da Hauwa na yi niyyar na je amma sai na kama ciwon ciki sai zawo, zan fita ne ina zawo na yi zama na a gida da daddare da Yallabai ya dawo sai da ya ce mini Hauwa ta je asibiti yau

"E. Ni na ce ta tafi kawai. Ban ji dadi cikina ke ta ciwo sai kuma na fara gudawa."

"Sannu ya bari ko sai mun je asibiti?

Ya faÉ—a da kulawa sai na ce ya yi sauki, ni bai nuna mini komai ba shi ya sa nima ban damu ba.
Ban kuma samu zuwa ba sai washegari da yamma bayan an sallamo Gimbiyar da safe, Munnira na kira a waya na biya gida na É—auke ta.
Sanda muka je yan Rano sun zo Mota guda su Naja da Anty Bahijja suna gidan ana ta shewa Anty Bahijja da ba ta gani ta ƙyale sai da ta ce mana.

"Jiya É—ayar ta ku ta zo ku sai yau ake ganin ku?

Wai Hauwa ce ɗayar mu. Munnira ce ta tsaya mata mgana ni gaisheta kawai na yi na wuce ciki wajen  Gimbiya. Mun gaisa da yan uwanta na Rano sannan na karisa gefen gado na zauna muka gaisa na ɗauki Jaririn sak Khalipa yana jariri, na yi masa addu'a na bata shi ba wani jima ba muka tafi, daga nan na mai da Munnira gida da motata na koma gida ban faɗa ma kowa haihuwan Gimbiya hatta su Ya Aina Jidda ta kira ni tana cewa Abban su ya kirata yana murna yana faɗa mata sun yi ƙani na ce ai fa. Ta ce har hotuna ya tura mata. To ba abin mamaki ba ne tun da farar haihuwa ce aka sake yi masa.

Tun da na je barka ban ƙara komawa ba. Ga mamakina ana jibi suna Yallaɓai da zai fita sai ya ce mini na shirya na je na duba mai jego.

"Na je ai na duba ta."

"Na sani. Ya kamata ki sake komawa kafin suna."

Kamar zan yi magana sai ban yi ba, na ce to yana fita ko na ce ba in da zan je. Ranar yini na yi barci ma da ya dawo bai tambayeni amma na san ai ya fara biyawa ta gidan ta. Tun da Baaba Asma'u ta zo wacce ta zauna mata da haihuwan Anwar shi ya sa yake kwana a gidana. Ni ce da kaina na faÉ—a masa ban je ba ba na jin daÉ—i.

Na ga ya kalle ni amma ganin bai sauya fuska ba ya san ban damu ba.

"Allah ya sauwaƙe."

Na amsa masa da Amin Amin

Kuma ko washegari ban je ba na yi zamana a gida. Munnira dai da Hauwa sun leka aikin suna ni dai sun kirani na ce musu ba in da zan je.
Ranar suna na yi niyyar lekawa shima ba da safe ba. Danan na cire mata atamfa É—aya da pampers sai mayukan yara cikin saura na Yumna na saka a leda na ce in na leka goben zan kai mata.

*Janafty**TKGB3N014*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX

Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732

Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰

A daran da Yallaɓai ya dawo yake faɗa mini sunan yaro Muhammad. Na ce Allah ya raya mana Muhammad cikin addinin islama ya ce Amin Amin. Tare muka kwana cikin farinciki, da wuri ya fita saboda ya ce akwai mutanen da ke jiran shi a can office amma ya sha wankan shi ya ci gayu cikin shadda dark blue amma ba mai babban riga ba. Sai ya fito a angon ƙarninsa ina zolayansa kafin ya fita.

Bayan na dawo raka shi na yi ma Yumna wanka na goya ta na fara ayyuka Baby daman ita ta fara fita kafin Yallaɓai. Jiya da daddare na ji ta fara faɗin yau sunan Anty Gimbiya ba za ta je makaranta ba tun kafin Yallaɓai ya ji labari ya ɗaure mata kugu na ja mata kunne shi ya sa yau da safe ba ta yi rigiman ba za ta je ba. Shara na yi sannan na yi mopping gidan duk ya yi ƙura kwana biyu ban yi ba,  da man Jidda ne ta sangartani yanzu kuma tana makaranta Baby kuma ga makaranta ranar weekend kuma tana Tahfez in ma ta dawo wanke-wanke kawai ya isa ta fara tura baki tana faɗin ita duk ta gaji shi ya sa ban ma dogara da ita domin na fahinci ko a zamanin baya Baby ta fi ni lalaci.

Har ga Allah ban yi niyyar zuwa sunan da wuri ba. Wajen sha É—aya na safe sai ga wayar Hauwa tana faÉ—a mini na shirya na ce mata ni fa ba yanzu zan je ba sai anjuma.

"Don Allah ki shirya mu taho gidan ki mu wuce tare."

"Ke da wa?

Na faÉ—a ina tura baki kamar tana ganina.

"Ni da Munnira mana. Mutanen Rano ma suna kan hanya yanzu muka gama waya da Ashen mu."

Cikin mamaki na ce" Ikon Allah suma duk za su taho ne?

"E tare da yan gidan su Gimbiyar ne. Hajiyarsu ta aika ma Mama shi ne ta ce ashe ta shirya ta bi su."

Ni dai sun takura mini ba ni da yadda zan yi sai na ce bari na shirya. Mun gama wayar da ita kenan Marwa ta kirani ashe har da ita a masu tahowa suna kuma a can gidan sunan za su sauka jin haka ya sa sai na ce bari na shirya kawai mu wuce tare da su Munnira. Ni daman yan gidanmu ban faÉ—an ma kowa ba Ma'u ce kawai ta sani kuma na san ba a bakina ta ji ba, ta yi mini maaganar ashe Gimbiya ta haihu na ce e ta yi fatan alheri ba ta zo ba kuma. Domin gabaÉ—aya alaqar su da Anty Bahijja ya ja baya. Ni yadda ma Ma'un take faÉ—a mini Amaryan Alhaji Mustpaha yanzu ita dangin shi suka rike ita da Hajiya Zainab ina jin har Anty Bahijjan ta yi ma Ma'u batulci. Na san ta sarai za ta aikata tun da ita daman ba ta da alkibla.

Kafin na shiga wanka na kira Hauwa a waya na ce na chanza shawara su biyo mun sai na ɗauke su a motata mu tafi tare sai ta ce mini to. Sai da na yi wanka na shirya cikin wani leshina sabo ne yana daga cikin kayan da na samu da sunan Yumna ɗinkin bubu doguwar riga. Leshin mai kalan maroon ne sai na yi amfani da mayafi kalan shi takalmi ma da jaka ina da maroon da su na yi amfani. Yumna kuma na yi mata gayu cikin kaya yan kanti jajaye harta takalmin kafanta da safa ja ne, haka hulan da ke kanta na gyara mata gashin kanta. Ta biyo a sumar kai amma Yallaɓai ba ya bari a yi mata kitso sau ɗaya Maman Nana da ta zo yi mana kitso ni da Baby  na ɗan ce ta yi mata kalaba aka sanya mata band kitson ya yi kyau amma ta yi ta kuka saboda ba ta saba ba.
Chapter 56 · 0% Book details