Sashe 47
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Tab ciki ko gashi nan har ya fito ba ki gan shi a jikinta da salla ba ne da kuka haÉ—u?
"Ban lura ba"
Na faÉ—a ba tare da na sake yin wata magana.
"Ai ko ciki gare ta. Da Suwaiba ta yi magana ta ce ba an ce likita ya ce ta huta ba Anty Bahijja ta ce likita ai ba Allah ba ne. Lafiyan ta ƙalau kuma za ta iya haihuwa da kanta gwara ta yi ta haihuwa tun da Mijinta mai son ƴaƴa ne"
"Ba shakka"
Na faɗa ina jinjina kai, na rasa me zan ce ma. Ita dai Gimbiya haihuwa ce a gabanta ita a dole sai ta fini yawan ƴaƴa a raina na ce ta yi ta haihuwa ko duniya za ta haifa ba ta gaba na. Na tuna ko bayan haihuwan Anwar ni da Yallaɓai mun yi magana ya ce za ta yi planning ko na shekara biyu saboda dokar likita ban sani ba ko ba su yi tsarin iyalin ba ne. Shuru na yi da bakina na yi kamar ban ji ba ko Yallaɓan da bai faɗa mini ba nima ban nuna masa na ji ba, kowa kuma ban yi maganar da shi hatta ko da su Munnira. Sai ma Hauwa ce ta kira ni a waya ta na faɗa mini a Rano ta ji labarin Gimbiya na da ciki na ce mata e da gaske ne.
"Ba likita ya ce ta huta ba?
"Ba ta son hutun ne Hauwa. Ki barta ta yi haihuwanta."
"Allah ya sauwake."
Haka muka rufe maganar muka shiga wata, mun É—an jima muna magana kafim mu yi sallama Munnira ma da ta ji ba ta yi mini maagana ba sai da na je gidanta ranar daga asibiti na kai Yumna tana da fama da ciwon ciki, shi ne muke maganar da ita.
"Ai kishiyar nan taki munasura ce Sadiya. Ta ce ita haihuwa yanzu ta fara a gidan Tafida ba ta ma yi komai ba tukunna."
"Allah haka ta ce?
Munnira ta ce"Haka ta ce, ta ke faÉ—a a gidan su nima Hauwa ce ke faÉ—a mini da ta je gidan su ta ji maganar."
"To Allah ya ba ta masu albarka"
"Addu'a za ki yi mata?
"To zan ce ne kar Allah Ya ba ta masu albarka ne Munnira? Allah ya ba ta masu albarka ko ba komai ai ai ƴa'ƴan Yallaɓai ne. Kuma duk saurin ta sai dai a kira su ƙannen su Jidda ba dai yayyen su ba"
"Wannan gaskiya ne."
"To kin gani. Ku bar ta lokaci ne wata rana sai labari."
Har na baro gidan Munnira ba mu ƙara ma ta da hiran Gimbiya ba, ni ma da na dawo na cire abin a raina na watsar nima na gode ma Ubangiji tun da har ya ba ni biyu ya kuma ƙara mini a lokacin da na cire tsammani, ita takamar tana da ya'ya maza ita ce ta haihu ni tun da mata ne yarana ban haihu ba ko alama ba ta gabana harkan rayuwata kawai na ke yi. Kuma yadda shima ya yi shuru bai taɓa mini maganar nima ban yi masa ba sai ranar da ya ke gidanta har dare bai zo ya duba mu kamar yadda ya saba sai a washegari da safe ya zo yana faɗa mini a jiyan Gimbiya ce ba lafiya a asibiti suka yini, amma an sallamota tana gida in na samu lokaci na shirya mu je ni da yara mu duba ta a gida.
Kamar zan je sai mun samu lokacin sabo da ban manta wulaƙancin da ta yi mini da cikin Yumna ba ni ko ba zan ƙara rawan jiki a kanta ba. Na ce masa za mu je ranar da su Jidda ke gida na masa Allah ya ƙara lafiya amma ko gaisheta ban ce ya yi ba. Kwana biyu tsakani ranar lahadi Jidda na gida ta je Hadda ba ta dafe ba ta dawo tun da sun gama haɗa Qur'anin su suna bita ne kafin a yi musu waliman sauka. Daman a gidan ya kwana yana ganin su dukkansu a gida sai ya ce mu shirya mu je mu duba ta daman na kudira a raina ba zan je ba. Sai kawai na nemi waje na kwanta na ce ba na jin dadi wai to bari a fasa sai gobe in na samu sauƙi.
"A'a ku tafi kawai ku gaishe ta."
Na faÉ—a ina daga kwance a saman gado
Sai ya ce to bari su tafi amma har da Yunma Baby ta É—auka suka tafi, tun bayan la'asar sai dare suka dawo sai ga su da yara niki niki Anwar da Khalepa da kayan su, sannan ba su dawo da Jidda ba wai tana can za ta kwana saboda Gimbiyar ita kadai ce yaran ma tace a kawo mini su sun dame ta da hayaniya ga shi ba ta da lafiya.
"Topha. Ai nima ba ni da lafiyan kuma daman Jidda ce ƙarfin aikin gidan yanzu."
Na faÉ—a a tsume bayan duk ya gama rattabo mini bayaninsa. Wato ga jaka dole ta ce a kawo mini yara.
"Ga Baby za ta taimaka miki da wani abun. Ita ma Jidda zuwa jibi za ta dawo tun da ranar laraba suna da jarabawa."
Takaici ma ya hana ni mgana, tun da yaran nan suka zo hutu na ya ƙare tun da Jidda ba ta nan dole na ke tashi da safe na yi musu shirin makaranta. Har Anwar da ke ɗan shekara biyu an saka shi makaranta ajin yara ban sani ba da man a can uwar su ke kai su yanzu kuma tun da suna gidana Salisu ne.
Ko Yallaɓai in bai fita da wuri ba, sai da Jidda ta kwana uku ta dawo da na ke tambayanta Antyn ta su a kwance take?
Sai ta ce mini.
"Wani kwance Umma? Ta ji sauki fa ta yi ta chart da waye wayenta abinci ne ma in ta ci wani lokacin ta ke Amai."
Jinjina kai kawai na yi, a raina na ce ban ga laifinta ba wanda ya samu rana ga igiya ai sai ya yi ta shanya. Yallabai ne ya ɗaure mata gindin yara kuma na yi magana ya ga ɓakina. Amma me ya sa bai kai su gidan Naja ko Anty Bahijja ba? Sai ni ko wacce suka raina to ai ya yi kyau ni kaɗai ranar na rika masifa a cikin gida kuma har lokacin bai faɗa mini ciki gare ta ba, nima ban tambaya ba sai ranar da ya ke gidana har mun yi shirun kwanciya ya fita ɗakin yara sai ga shi ni kuma ina kwance ina ba ma Yumna Nono ta farka ta fara mini jananun kuka.
"Meke damun Gimbiya ne haka da take ta rashin lafiya?
Da gayya na yi masa tambayan ya na sauya kayan jikinsa zuwa na barci yake amsa mini.
"Laulayi ne."
"Laulayi?
Na maimaita cikin sigan tambaya.
"E ciki gare ta. Ba ki sani ba?
Sai da na balla masa wata uwar harara kafin na ce" Na sani mana tun da ka sanar da ni."
Sai ya yi dariya lokaci É—aya yana hayo gadom har kusa da ni, hannunsa ya sa ya É—an shafa fuskar Yumna zuwa jikinta.
"Kar ka ja ta da wasan ka. Ka ja mana tsayuwar daren dole."
.
Dariya ya fara yi ni kuma na kanne ina fadin" Ahto domin kai zan haÉ—a da ita na yi kwanciya ta wallahi."
"Na ji ba komai. Ai na iya reno nima."
"Ka iya fa."
Na faÉ—a cikin gatse,shi kuma yana ta mini dariya.
Ganin na gimtse fuska ne ya sa ya saussauta murya ya na faÉ—in" Da gaske ba ki san Daughter na da ciki ba?
"Na sani na ce ba ka faÉ—a mini ba?
Na faÉ—a ina masa wani kallo.
"Yi hakuri ma yar da wuƙar wallahi na ɗauka fa kin sani shi ya sa ba mu yi maganar da ke ba."
Uhm"
Na faÉ—a kafin na ce" Allah Ya raba lafiya.'
"Amin ai da sauƙi ma bai wahalar da ita kamar cikin Anwar ba."
Na yi masa banza na cigaba da ba ma Yunma Nono.
"Kin san likita ya ce ta huta. To da na yi mata mganar ko za ta yi tsarin iyali ne ai kin san mun ma yi maganar da ke ko?
Ya faÉ—a yana kallona sai na gyaÉ—a masa sai ya cigaba da faÉ—in" Sai ta ce ita ba za ta yi ba. Wai ba ta son yi saboda ba ta so ta yi itama ta samu matsala irin na ki."
"Jar Uba!
Ban san na yi ashar ba sai da na ji ya fito. Yallabai ya yi ƙasake yana kallona. Cire Yumna na yi daga nono na kwantar da ita gefe ina kallon Yallaɓai.
"Zagi kuma Sadiya?
"Dole na yi ashar na ga matarka na neman rena mini wayau ne."
"Na me fa?
Ya faÉ—a shima ya É—an sauya yanayin shi.
"Saboda ta raina ni sai ta yi kwantance da ni ni kaɗai ce macen da ta taɓa tsarin iyali ya sakar mata matsala? Ko tsarin jikin mu da jinin mu ɗaya ne. Wata ƙila ita in ta yi sai ta wanye lafiya ai komai na Allah ne amma don tsabar renin wayau sai ta fake da ni? Ina ruwanta to da rayuwata"
"Ki tsaya ki fahimci ne ita fa ba haka take nufi ba."
"Ya take nufi? Kar ka wani kare mata. To ni ba ni da wata matsala ba kuma zan gani ba in sha Allahu sako na baka ka sanar da ita ni Sadiya ba ni da matsala ban kuma tare da ita wanda ke ƙababa mini ita ma ya je Aniyarsa ta bisa wallahi."
Na ƙarishe faɗa a fusace saboda raina ya gama baci ina gidana amma ta na can tana raina mini wayau.
"Topha ni ce Aniyata ta bi ni ko Daughter?
"Oho ni dai na ce ba ni da matsala mai neman kuma goga mini ita sai ta faÉ—a kan shi Ehe."
Na fada ina sauka daga gadon gadon bi na ya yi da kallo ya yi kafin ya ce" Yi hakuri kar ki dake ni."
"Ban isa ba kuma."