← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 103

Sashe 88

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na kore ki gidan ki ne ko gidana? Wallahi na gaji dake da halin ki, da man tun tuni ya da ce na kore ki, kin fara yi mini asaran dukiya wata rana rai za ki kai ma hari."

"Duk abin da ya faru kai ne sila. Domin da ka yi adalci da haka ba ta faru ba maimakon ka yi nadama amma sai ka kore ni? Ni za ka tozarta a kan wancan yarinyar?

"Ba sunanta yarinya ba. Sunan ta Rabi'atu ce matatace kamar yadda kike matata. "

Gimbiya ta sake sakin kuka kafin ta ce" Saboda ita yau kake kora ta?
"E saboda ita ne domin ita ba mahaukaciya ba ce kamar ke"

Sai Gimbiya ta fara kururuwa har tana zama a kasa hannu a saman kai tana faÉ—in Yallabai ya zageta ya ce mata mahaukaciya.

"E na faÉ—a in ba mahaukaciya ba wacece za ta yi abin da kike yi? Ita yarinyar da kike kishi a kanta wallahi na tabbata ba za ta yi haukan da kike yi ba. To tun da ni ba ki bani farimciki nima kuma ima zaluntarki gwara ki zo ki tafi garin ku na gaji"

A fusace ta mike tana faÉ—in" Nima wallahi na gaji "

"Ni na fara gajiya"

Yallabai ya faÉ—a har yana sakin tsaki, ina so na yi magana sun hanani da wannan ya dire wannan zai É—auka.

"Sai ka sake ni domin na je ma da iyayema da shaida."

Gimbiya ta faÉ—a tana tsiyayan hawaye duk sai jikina ya yi sanyi.

"Sakin kike bukata?

Yallaɓai ya faɗa idanuwansa sun yi jajir.

"E ina buƙatar shaida."

"Fine. Zan ba ki shaida."

Ya faɗa yana mai juyawa da gudu na fito na sha gaban shi ina kiran sunan shi amma ya raɓa ni ta gefe ya wuce na riƙe bayan rigan shi ina faɗin.
"Don Girman Allah Yallaɓai kar ka yanke hukumci cikin fushi."
Fizge rigan shi ya yi kawai ya shige bangaren Rabi'atu na taho ya banko mini kofa a fuskata sai na yi sororo, ba. Buga masa ganin mun riga mun bar ma Megadi abin faÉ—a duk da bai fito ba amma yana cikin É—akin sa yana jiyo duk hayaniyar dake faruwa.

Shashen Gimbiya na koma tana cikin bedroom ɗin ta, tana haɗa kaya a cikin babban akwatinta tana kuka. Duk ta zubo su daga cikin wardrope ɗin ta. Hankalina ya tashi na fara tare ta ina hanata saka kayan a cikin akwatin da ta ɗauko sai na karɓe ina faɗin" Haba don Allah miye haka kile yi?

"Ba ji ji me ya ce ba ne? Ya ce na zo na bar masa gida tun da ba na bashi farimciki."
.
Ta faɗatana mai ƙara fashewa da kuka. Duk taƙamar cikin mintina har ta fita kamaninta sai na dafa kafaɗanta ina lallashinta.

"Ki yi hakuri kema bacin rai ne shima haka in zuciya ta yi sanyi za a daidai ta."

"A'a Maman Jidda ki bari kawai na tafi. Sakina fa yaje ya rubuto ya kawo mini zaman me zan yi?

"Ba zai sake ki ba. Ba aure ki don ya sake ki ban"

Na faɗa ina mai kara dafata, cikin kuka ta ce" Ya ce fa da kanshi ya gaji Maman Jidda. Ni wai yau Yusuf ke yi ma wulaƙanci saboda wata ƙaramar yarinya?

"Laifin ki ne me ya sa kika fasa motar nan? Duk da shima bai kyauta ba amma da kin yi shuru kin jira ki ga iya gudub ruwan shi. Sannan ai shi mijin ku ne shugaban ki, bai kamata yana faÉ—a kina faÉ—a ba. Duka ranku ya baci shi ya sa kuka yayyaba ma juna mganganu."

Cikin hawaye ta kalleni kafin ta ce" Na kasa haƙuri a nan wajen na ke jin ƙuna in na ga Yallaɓai na fifita wannan yarinyar a kaina? Na kasa hakuri ne"
Ta faɗa tana mai nuna mini saitin zuciyarta sai kuma kawai ta yi zaman dirsham a ƙasa tana cigaba da gurzan kuka. Sai na bi ta nima na zauna a gefenta ina ɗan bubbuga kafaɗanta alamun lallashi.

"Shi ya sa na sha ce miki Gimbiya ki yi haƙuri domin duk abin da haƙuri zai ba ka rashin sa ba zai ba ka ba. Da kin yi hakuri don Allah duk wannan abin da ya faru zai zo ya faru?

Sai ta yi shuru ta kasa mgana sai kuka ni kuma sai na cigaba da faɗin" Kana gani za a cuceka ayi maka abu na rashin adalci amma sai ka yi shuru ka yi haƙuri ba wai don an fi karfin ka ba sai domin hakurin shi ya fi alheri. Tashin hankali ba shi da daɗi da a ce kin same shi ta lalaba kin tambaye shi Baban Jidda ni fa tawa motar sai yau she za ta zo? Duk amsar da zai wuce kema na ki na hanya ba ai yana da ilimi ya kuma san abin da yake yi. Ba ina kare masa ba ne amma ina so na faɗa miki gaskiya. Yallaɓai na kamanta adalci, nu ya faɗa mini zai siya ma Rabi'atu mota saboda makarantar ta, duk da bai yi mini bayani ba na san ya fara siya mata ne saboda ita ke ɓukata yanzu. Ke kuwa kina da shi canji kike so nima haka shi ya sa ya fara siya mata kafin ke daga baya."

Sai na ɗan dakata ina kallonta ganin ta natsu tana saurarena amma ba ta shassheƙan kuka ba.

"Da kin yi abin cikin lalaba da duk wannan abubuwan ba su faru ba. Ga shi yanzu zuciya ta ɗebe ki kin aikata abu. Ran ki ya ɓaci shima na shi ya ɓaci fisalillahi ina daɗin shi.?

Cikin jan majina ta ce" na kasa hakurin ne. Wallahi na kasa."
Ta fada hawaye suna mata ambaliya sannan ta sake kecewa da kuka kamar wata ƙaramar yarinya.
Duk surutun da na gama yi a banza domin Gimbiya ta miƙe ta cigaba da haɗa kayanta ta kuma ce sai ta bar masa gidansa tun da ya ce ba ta bashi farinciki.
Ganin ta ƙi saurarana ya sa na fita zuwa shashena na iske su Baby sun yi jugum har da ita kanta Rabi'atu ni saboda tsshin hankali na manta da yau suna da makaranta sai da Baby ta yi mgana.

"Kun makara ki shiga kitchen ki sama muku abin da za ku ci. Rabi'atu yau ba ki da shiga makaranta ne?

A sanyaye ta ce suna da lecture, sai na ce ta koma bangarenta ta shirya mana. Ta amsa mini ni dai na shige ƙurya na dauki wayata na danna ma Nene karon farko domin mi ban taɓa kiran ta da sunan wata matsala ba sai dai gaisuwa. Bayan ta ɗauka mun gaisa ba ɓata lokaci na zayyana mata duk halin da ke faruwa ta ja salati ta dire kafin ta ce" Ya sake ta ne?

"Ban sani ba amma dai ya shiga É—aki ya rufe kansa."

"Innalillahi Saudatu ba ta jin mgana. Sadiya don Allah ki hana ta tafiya bari na kira Zuwaira."

Sai na amsa mata da to, muna gama wayar na fito sai na ga ba Rabi'atu Baby kuma tana kirchen yaran kuma sun saki suna ta wasan su sai na fita, haraba na ci karo da Rabi'atu tana buga ƙofar shashenta.

"Yana ciki ki yi magana in ya ji muryan ki zai bude."

Ban tsaya ba na shige bangaren Gimbiya na same ta har ta gama haÉ—a kayanta ta zurma hijabi, na janye akwatin na ce ba ta za ta tafi ba.
"Maman Jidda ki bar ni na tafi, ya ce sakina zai yi"
"Shi bai ce ba ya dai ce ki bar masa gida amma bai ce zai sake ki ba ke ce kika furta haka"

Cikin kuka tace" To ai manufarsa kenan. Miye ma'anar miji ya kore ka daga gidan shi? An ya an taɓa yi ma wata mace tozarci kamar yadda yau Yusuf ya yi mini?

Ina mata mirmishi na ce" Nima mun taɓa faɗa da Yallaɓai na ce zan bar masa gidan sa ya ce na tafi bs zai hana ni ba'
Sai ta kalleni baki buÉ—e tana mai mamaki.

"Wallahi kuma a kan ki ne. Ban taɓa faɗa ma kowa ba ranar a gidanmu na kwana."

Sai na ga ta koma ta zauna gefen gadonta amma na kasa mgana, ni ma sai na zo na zauna a gefemta amma ina riƙe da akwatinta a hannuna.

"Shi ya sa na faɗa miki haƙuri ake yi ba kyau yanke hukunci cikin fushi."

"Ya ce ki bar masa gida? Ke ma É—in!

Sai na gyaɗa mata kai ina dariya kafin na ce"Yes na kuma yi tafiyata saboda lokacin raina ya ɓaci komai ma zai iya faruwa."
"Wa ya dawo da ke?
"Alhajinmu ya yi mini faÉ—a ya nuna mini kuskurena. Sannan shi kuma ya zo ya tafi da ni washegari da Safe."
"Da man kuma samun sabani a kaina?
Na É—auka ke ba ki da kishi Maman Jidda?

Ta faɗa tana kallo na kuma da gaske take yi abin da ke ranta ne ta faɗa. Ban san na kyalƙyalce da dariya ba sai da na ga ina yi.

"Da gaske ina ta so na tambayeki tuntuni. Miye sirrin ki da ke ba ki damu da mu ba? Lokacin komai matsala za mu samu ni ce zan zama sila ba ke ba. Kuma sai na ga kamar ba ki da kishi a kaina, ga ma Rabi'atu yadda kike mu'amalamta kamar ba kishiyarki ba, da gaskr nake yi na sha tunanin ko dai ba ki da zuciya ne? Ba kya jin irin zafin da muke ji in mun gan shi da ke?

Kai na girgiza ina faÉ—in" Me ya sa ba zan ji kishi ba ai nima mace ce Gimbiya ina da zuciya a kirjina.'

"Amma me ya sa ba ki nunawa?
Chapter 88 · 0% Book details