Sashe 78
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya faɗa cikin farinciki ina jin ta hayaniya ta wayar sai ya kashe. Sai da na ji tahowar ƙwalla amma sai na yi saurin yar da ita. Na yi kwalliya tun da har mai kwalliya na kira na gayyaci su Maijidda da samira duk sun taho mini biki. Waina aka yi da shinkafa sai alele sai zoɓo ga ruwan gora da lemuka sai wanda ka zaɓa. Na diba abincin tun da aka gama na aika da shi Gwammaja. Su Suwaiba ne suka zo mini bioi sai su Jawahir, sai su Hauwa da yan gidanmu duk wanda bai zo ba yana gidan Gimbiya. Na ce duk abin ta dai ga shi ba a fasa ba. Sai ga Ummu Salma da mahaifiyarta sun zo mana biki kuma wallahi na ji daɗi har da su turarenka wuta ta kawo mini da mayukan gyaran jiki ba su kwana ba, bayam la'asar suka juya ta ce sai za mu koma sabon gida za su dawo in sha Allahu. Haka na yi taron biki lafiya aka gama lafiya mun shan ankuna mun sha hotuna kuma duk na tura ma Yallaɓai shima ya turo mini na su da su Kawu sai na shi shi da Amary ta sha lafaya yar maiduguri sak ba ta yi makeup ba fuskarta sak ta bayyana.
Mimisco ta watsa hotunan a can group ɗin su na gida Musbahu ma dake can ya riƙa turowa ma su jin haushi suna gefe suna ji ba su da yadda za su yi. Tun kafin su Yallabai su ta so ya kirani ya faɗa mini, ya ce akwai ma wasu y'an uwa Rabi'atu da tun jiya suka taho. A yi abimci na tarban Amarya na ce ma to. Su Munnira na bar ma aikin,shinkafa suka dafa priderice, sai ferfesun nama da pepe chickenn da kuɗin hannuna na yi amfani ya ce in ya dawo zai ma yar mini. Ba a samu kunin aya ba amma an yi zoɓo sannan ga lemuka da ruwa
Da aikawa na so na yi amma Yallaɓai ya kirani da kan shi ya ce na je gidan na tarban masa Amarya.
"Sai na je? Ba ga Gimbiya da su Anty Bahijja?
"Na san da su na ce ke. In kuma ba za ka yi mini ba ne sai na ji."
Ina jin haka na ce masa ya yi haƙuri zan je, ina ma gidan Mimisco ta biyo ɗaukata ita ta yi tsire ne mai yawa na tarban Amarya nima da su Hauwa da Munnira da Farida muka fara yin gaba sauran kuma na ce su hawo adaidaita. Motata kuma Amina ta tuƙo yan gidanmu zuwa cam. Mun iske bangaren Gimbiya cike da su Halima itama bangaren Amaryam akwai yan uwata a ciki masu jiran tarban ta. Saboda dai a zauna lafiya sai Mimisco ta ce mu fara sauka a bangaren Gimbiya amma na san ita kanta ta yi nadama. Wulakanci suka yi mana, kamar ba su taɓa sanin mu ba, Naja ba ta gaisheni ba amma ta gaishe da uwarta Anty Bahijja ba ta gidan sai Anty Maimuna kamar ta kashe nu in tana da iko. Sai Gimbiyar da ƙawayenta sai yanuwanta daga can Rano. Haka suka yi mana kallon banza wai ni Halima ke yi ma habaicin a yi dai mu gani in tusa za ta hura wuta.
Da Mimisco ta ce in Amarya ta zo a fita gabaɗaya a yi tarba shuru suka yi wallahi da ta iso ƙin fotiwa suka yi, Adnan ne ya ɗauko ta da ita da ƙawarta da kanwar mamanta daga filin jirgi, dagqani sai tawagata sai Mimisco muka yi tarban amarya. Mimisco ta yi tarba da Turaman zannuwa uku da 50k. Nima na yi da 20k da cimgam da su minti kuma wallahi sun ji daɗi, Rabi'atun tana cikin lafaya fara ne a rufe amma tana ganina sai da ta gane ni ta riƙe mini hannu.
."Barka da zuwa Amarya."
Bi sa al'ada bangaren Gimbiya muka fara yi musu jagora. Kanwar mamanta ta tambaya an ce tana da abokan zama guda biyu. Mimisco ta nuna ni ta ce ni ce uwargida ban riga na tare ba ne amma na taho tarban Amarya sai Gimbiya. Wacce ba ta ma fito falon ba duk da ko Mimisco da kanta ta kirata amma wallahi ta kunya ta mu a gaban mutane abin gudun ban takaici. Kanwar maman Rabi,a ta ɗan fahimci wani abu sai ta yi ta cewa a yi haƙuri da juna a zauna lafiya. Rabi'a ƙanwa ce a gare mu mu tsawarta mata in ta yi ba dai dai ba, haka nan muka kwashi sanyin jikin mu muka raka su bangaren Amarya. Ni na ɗauka a gidan Nene za tafara sauka Mimisco ta ce sai gobe za a kaita. Itama ranta ya ɓaci na ga ta kira Naja da Maimuna tana yi musu faɗa ni dai ba mu zauna ba, muna danƙama dangin Amarya abinci muka yi ta kan mu bayan na sanar da ita in tana bukatar wani abu ko ta kirani ko ta kira Yallaɓai za a kawo mata ta ce to.
A daran ma Yallaɓai ba a gida ya kwana shi da su Kawu a hotel suka kwana sai washegari da safe na gan shi da suka shigo gidan. Yallaɓai ana ta baza baban riga yana washe baki da an kira shi Ango ya yi dariya har tana fidda sauti.
*Janafty*
/*TKGB3019*
*EID MUBARAK FANMILY. ALLAH YA MAIMAITA MANA. SON SO.
Da ma Amina ce da Faridan Tariq sai Marwa suka kwana a gidan. Yallaɓai yana ganin Amina ya washe baki yana ce mata ashe ta zo?
Ita ko saboda ta kunna shi sai ta ce ai zuwa bikin nan ya zame mata dole. Ba kunya ya ce ya ji daÉ—in zuwanta. Megidanta ya tambaya da yara tace suna nan lafiya.
Faridan Tariq kuma tsiya ta fara yi masa wai ya yi biyu ba zai haƙura ba sai ya haura uku.
Yallaɓai na dariyan nishaɗi ya ce" Ta in da za ki gane ni gwarzo ne ba. Ba matsaroci irin mijin ki ba."
Ya faÉ—a yana nuna Tariq wanda ke gefe yana magana a waya ne tun shigowarsu gidan
Kawu Abba kuma muna gaisawa da shi ne.
Shewa Farida ta yi kafin ta ce" In dai tsoro ne to Allah kar ya cire masa wannan tsoron har abada."
"Muguwa kike Farida?
In ji Yallaɓai yana dariya.
"Sadiya kina jin kawarki ko!
Ya faÉ—a yana kallona ina dariya na ce" Bar ta sai dai in bai gano wata yar faka faka kamar yadda ka gano ba."
"Wallahi da man na ga a can yana bin yan mata gidan su Rabi'atu da kallo ko ya ga ni yana so ne?
Ya faÉ—a yana dafa kafaÉ—an Tariq daidai lokacin da ya gama wayar.
"Nima na lura da munafukin yana ta kallon wata yar fara nan ƙasa ƙasa."
Kawu ya faÉ—a yana shafa sajen sa, Farida ta ce ba su gani da kyau ba tana kare ma mijinta.
"To ke ina ruwan ki? Ba shi da bakin mgana ne?
Yallaɓai ya faɗa yana dariya.
Kawu ya ce ina zai yi magana ya san gaskiya.
"Ko dai kai ne ka ƙyallo wata kana son ka yi mini kage Kawu?
Tariq ya faÉ—a yana kallon Kawu shi kuma sai ya buÉ—e baki amma ya kasa mgana ni da Farida muka fashe da dariya.
"Ina matarsa? Ina marwatun? To ta shirya wata ƙila za mu koma Maiduguri karshen shekara."
"Tariq haka ka zama?
Kawu ya faÉ—a yana rike baki.
"Ƙarya na yi? Kai Tafida ba ka gan shi a ranar ɗaurin aure da muka je gaisuwan surukai yana tambayan sunan wata budurwa ba?
"Kamar fa na gan shi."
Yallaɓai ya faɗa yana danne dariya.
Kawu ya jinjina kai kafin ya ce" Yaran nan abin tsoro ne. Mu ɗan bangaji juna ne lokacin da za mu shiga za ta fita ita kuma, sai ta ba ni haƙuri na ce ba komai amma saboda ku magulmata ne har kun hango wai ina tambayan sunan ta ba?
"Ashe dai ka yi magana da ita."
"Na yi sai ka hana ni Ubana."
Kawu ya faÉ—a sannan ya kalleni yana faÉ—in" Surukata ni fa ban ga matata ba ban ga yayana ba."
Ina dariya na ce suna ciki bari na yi mata mgana.
Sai ya koma ya zauna saman kujeran falon yana faɗin" Yauwa Uwargida ran gida. Ke ce ke da gidan gabaɗaya. A ɓata miki rai mu yi tawaye wallahi "
Ya faɗa yana hararan Yallaɓai kamar ya san da shi ake yi ya ɗaga sannu alaman sarander kafin ya ce" Ba ma mai ɓata mata. Ni kaina in na ɓata mata abin a yi mini hukunci ne "
Kawai ba zato zan wuce na ji Yallaɓai ya rumgumeni ta baya ina ƙoƙarin ƙwace kaina ya sumbace ni a gefen fuska yana faɗin.
"Na gode Abar ƙaunata. Ubangiji ya ruɓanya miki a ranar lahira."
Farida da su Tariq suka amsa da Amin har da Kawu.
"Gaskiya Sadiya tana da kawaici. Wallahi ni ba zan iya abin da ta yi ba har ga Allah. Tun auran Gimbiya na san ita jaruma ce to ga wannam ma. Gaskiya na jinjina mata."
"Gaskiya abin a jinjina mata ne."
In ji Tariq.
"Shi ya sa nake ƙara jadaddaa ma Tafida cewa ya riƙe ta da kyau. Domin kaf cikin matansa ba mata kamar Sadiya. Domin a wannan zamanin ka samu macen da ka yi mata abubuwa da dama ta kauda kai, ta yi maka kara ta mutumta rigarka a idanuwan danginka da danginta ba abar tozartawa ba ce."
"Gaskiya ne."
Tariq ya sake faɗa, ni kunya ma suka kamani na ƙwace kaina ina faɗin" Ka bari mana Yallaɓai.
"Wai ina miki godiya?
Ya faÉ—a yana kallona da ka gan shi za ka san yana cikin farinciki.
"Ni me na yi? Ai umarnin Allah ne ban isa na ja da hakan ba."
"Duk da haka Na gode miki."
Ya faÉ—a yana mai kallona tare da yi mini mirmishi.
"Muna godiya Madam"
Tariq ya faɗa sai na amsa shi da cewa" Kai dai kana tsoro ko? Ko ƙawata ta bake ko'ina ne?
Na faÉ—a ina dariya, ita kuma Faridan tana cewa ita ba ruwanta ya yo mana ai ba kanta za ta zauna ba.