← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 103

Sashe 68

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ban faÉ—a masa wani abu ba shi ne muna falon shi tare ya kallemu ni da ita yana faÉ—in" Na ga chanji daga gare ku na ji daÉ—i kwarai."
Sai ta ce masa ai ni ce na yi mata nasiha kuma ta ji za ta gyara in sha Allahu. Ya yi ta washe baki yana jin daɗi ya taso ya rumgumeni yana sumbatana a ƙuncina na ture shi ina hararan shi.

"Ke ce jagoran mata na ko a gidan Aljanna Sadiya ta. Ni da duk abin da na mallaka duka na ki ne."

"Har wannan gidan?

Na faÉ—a ina dariya.
Sai ya gyara zama a hannun kujeran da nake zaune ya ce" Wannan gidan da abin da ke cikin shi ai ya zama na ki, yau ba fata nake yi ko mutuwa ko rabuwa ba wanda ya isa ya fidda ke daga cikin sa. Sai dai ni ki kore ni ma domin kin cancanta."
Ina dariya na ture shi ina faÉ—in"Bana son daÉ—in baki."
"Wallahi da gaske na ke yi "
Ya faɗa yana ƙoƙarin ya dawo ya zauna kusa da ni sai na tashi na koma kusa da Gimbiya na zauna.

" Ni za ku haÉ—e ma kai?

Ya faÉ—a yana kama baki ni da ita muka haÉ—a baki wajen fadin" E É—in."
Muka faÉ—a a tare muna dariya sai ya koma ya zauna akan kujeran da na tashi yana faÉ—in" Za ku neme ni yara "

"Yara?

Na faÉ—a ina kallon shi sai ya zare mini ido yana faÉ—in" E yara ko kun girme ni ne?
Sai na yi shuru tun da na fahimci yana jin magana ne.
Saboda jin daÉ—i sai wajen goma ya tafi kai su gida da ya dawo bayan mun kwanta sai da ya yi mini maganar.

"Na gode Sadiyata. Don Allah ki cigaba da haƙuri. Ba ki ji farincikin da na ji ba lokacin da na gan ku tare da Daughter ba"

"Uhm"

Kawai na iya cewa domin sai na ga kamar Yallaɓai na sane a duk wasu iskancin da Gimbiya ke yi. Me ya sa ba zai mata faɗa ba? Sai ni ce zai yi ta nanata ma in yi haƙuri da ita, ita ba zai ce ta yi haƙurin ba.
Ni dai na yi masa yaƙe kawai ban nuna komai ba, sabo da kauda maganar sai na yi masa maganar zazzabin da aka ce Nene ta yi kwana biyu. Sai ya ce mini ta ji sauƙi ne shi ya sa bai faɗa mini ba amma na bari weekend sai na shirya mu je da yara mu gaishe ta na amsa masa.

Haka ko aka yi ranar lahadi muka je Gwammaja tun safe muka yini. Da man su Baby sun yi hutun Tahfez saboda gabatowar azumi, Nene ta ji sauki amma jikinta ba karfi ina gidan sai ga Halima wataƙila saboda idanuwan Nene ne ya sa ta gaishe ni, nima saboda mahaifiyarta na amsa. Ni saboda ita a bangaren Maman farko na yi yini na, sabo da ba na son abin da zai haɗa ni da yarinya. In ta neme kawo mini wargi ba zan ɗauka ba. Muna gidan har dare tun da Yallabai ne ya kawo mu sannan shi ya ce zai biyo ya ɗauke mu. Motata a gida na barta. Tun la'asar Halima ta tafi gida shi ya sa na koma ɗakin Nene, duk da ba ta fito fili ta furta mini ta ji maganar hatsniyar da muka yi a gidan sunan Ammar ba a maganganunta na san jirwaye take yi mini mai kama da wanka. Hausawa suka ce ruwa cikin cokali, ya ishi mai hankali wanka.

Ta yi ta ba ni haƙuri ne, tare da nuna mini na cigaba da haƙuri ina kauda kai. Sannan ta gangaro kan maganar Halima ta na nuna mini na yi hakuri da ita akwai yarinta a tare da ita, da ta ji labari ta yi mata faɗa sosai tun rashin kunyar da ta yi mini na farko. Ni dai ban ce komai ba illa to, amma ina ganin beken Nene, Haliman ce yarinya? Mata da mijinta da yayanta ai ta san abin da take yi. Na dai nuna ma Nene komai ya wuce amma a ƙasan raina na kudiri niyyar ba zan bi ƙanwar miji ta samu damar cin kasuwa a kaina ba. Ni ko yayar miji na ga tana tozartani kama kaina nake yi ballanta ita ƙaramar alhaki.

Mune sai goman dare Yallaɓai ya biyo muka tafi gida. Mu dai mun tsaya mun ci tuwo shi kuma sai da na dafa masa Tea da Indomie ya ci kafin ya kwanta. Sabgogin gaba na kawai na cigaba da yi ga matsowar azumi, shi ya sa na saro inears da yaawa wannan sallar har da mayafai da takalma na yara da manya. Yallabai ya ba ni 100k rance a cewarsa zan biya shi in na haɗa ribata na ce na ji na karba da shi na samu na ganganɗa na ɗinko hijabai diffirent ɗinki kala kala sama da hamsi suna gida sai dai da an saka oder na saka a leda na naɗe Baby na taya ni muna sawa a jaka ko a leda. Tun da Jidda na makaranta sai Baby ke taimakona yanzu. Kuma Alhamdulillah, ana siya sosai ina samu ga Jidda ma tana saka mini a status tana yi mini talla har yan makarantan su sun ce suna so. Irin mata yan dapertment din su, akwai wata ma course ɗin  ɗaya sannan ɗakin su ɗaya Ummu Salma Hamza ɗiyar Iyan zazzau ne na garin zaria itama akwai ƙoƙari kamar Jidda shi ya sa suka fara ƙawance shima ɗin sai da Jidda ta neme shawarata ni kuma na faɗa ma Yallaɓai na ce ya saka a yi masa bincike kan yarinyar kar ya zo ta shiga jikin ɗiyarmu ta cutar damu.

Shi ya bincika kuma ya ce yarinyar ta fito babban gida masu tarbiya. Jin haka ya sa muka ba ma Jidda izini ta saki jiki da ita, to ita ce ta siya hijabai sama da kala ashirin kaloli dabam-dabam. Ni kuma sai na ba ta kyautar ɗaya da dogon wando da sikat da pant saboda kyautatawa mai son ɗiyata. Cikin saƙon Khaleesat na saka musu sakon su can gidan suka je suka karɓa. A lokacin suka fara test ni dai addu'ata ko da yaushe Allah ya tsare mini yarana Jidda kuma ina yi mata fatan sa'a da nasara. Yallabai kuma yaƙini gare shi a kan Jidda da cewa in sha Allahu za ta saka shi alfahari wata rana.

Cikin haka muka shiga watan Ramadana, Jidda sai kusan salla ta dawo gida hutun na su ma na sati ɗaya ne ana fice salla ta koma saboda suna shirye-shiryen fara jarabawar farkon zangon karatu. Mu dai muna gida muna bin su da addu'a sai da suka gama jarabawa suka samu hutu ta dawo gida, duk ra rame sai ɗan wuya da tsawo. Yallabai ya yi ta faɗa wai kar ta saka ma ranta karatu ta mutu saboda naci. Ta riƙa hutawa tana cin abinci, dawowar Jidda na sake saka mata ido ko zan ga wani canji ban ga komai ba sai ma girma da hankali da natsuwa da Jidda ta kara. In ina kallonta sai na cika da alfahari na ce Ubangiji ka gama yi mini komai tun da ka ba ni Jidda. Baby ce dai wannan ko aure ta yi na tabbata sai na rika yi ina kwaɓa mata. Shegen rawan kai ne da surutu gare ta.

Kafin su koma Ummu salma Hamza ta kawo mata ziyara takanas ta zaria. Direba ya kawo ta a ranar kuma suka koma, ni kaina har da ni a masu yi ma Ƙawar Jidda Hidima. Itama na ganta mai kyau da ita age mate ɗin Jidda ce, ita ta fi Jidda haske da kiɓa amma tsawon su ɗaya. Itama a zuwan da ta yi na fahimci tana da natsuwa sosai.  Har Yallabai sai da Jidda ta kira shi ya dawo gida ya ga Ummu Salma suka gaaisa ni kuma ta ba ni mahaifiyarta muka yi waya. Ta ce mini tana shigowa Kano, za ta neme ni wata rana na ce in sha Allahu. Amma ta ce na karɓi lambarta a wajen Ummu sai na kirata na ce in sha Allahu. Ta kawo ma Jidda Atamfa da mayafi, sai Baby ta kawo mata doguwar riga har Yumna an kawo kayan wasa tun da ta san sunansu a baki. Nima da za ta tafi na ba ta hijabai biyu na ce ta kai ma mamanta. Sai turaren wuta da na jiki sauran nawa ne na kwashe na ba ta, Jidda daman ta yi cincin da donut ta kwashe mata aka yi raffing. Yallabai kuma 20k ya ba ta tace karɓa ya zare mata da cewa shi mahaifin Jidda ne. Kuma duk wanda yake aminta da Jidda ya tabbata shi din uba ne gare shi, shi ya sa ta karba ta duka har kasa tana godiya.
Muka rakata har waje, direban daman da ya kawo ta, tafiya ya yi sai da za su tafi ya dawo. Ni da kaina na yi ma Jidda alƙwarin itama za ta je har gida wajen Ummu salma. An ce tuwon girma miyan shi nama.

Kafin babbar salla suka koma makaranta. A lokacin na yaye Yumna, da na biye ma Yallaɓai to ba zan yaye ta ba. A cewarsa wai ba ta gama yin ƙwari ba yarinya bukekiya tana yawon ta ko'ina, tuni na cire ta a nono tana da wattani sha bakwai cikin na sha takwas. Da wajen Ma'u zan kai ta yayen, tun da ita ta yi mini magana. Har Marwa itama ta yi nacin na kai mata Yumna yaye. Ma'un da muke kusa na yi niyyar na kai mata ita ta yayeta kwatsam sai muka wayi gari da rasuwar mijin Baaba. Ma'u na can Kura mu ma mun je mun kwana ɗaya mun dawo har Amina dake Kaduna ta taho. To Allah ya sa dai ita ce uwar yayen Yumna ita tafi da ita Kaduna a can ta yi babbar salla. Tun tana rigiman Umma Abba Baby har ta gaji ta haƙura tun da akwai yara a gida. Yallabai ya gaji da korafi na ɗauki hakkin yarinya ya haƙura shima.
Chapter 68 · 0% Book details