Sashe 52
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jidda ta kalli Babanta kafin ta ce" Mun gode Yallabai Allah ya karo buÉ—i."
Baby ta ƙyalƙyace da dariya kafin ta ce" Abba Yallaɓai "
Ni da shi muka yi dariya gabaÉ—aya.
Daran nan da kyar na iya barci gani na ke yi kamar mafarki waahegari ni na kai Baby makaranta a mota ta, daga can ɗorayi na dira Yallaɓai na bari a gida shi da Jidda daman na ce sai in da mai ya ƙare.
Sai da su Gwaggo su ka ganni da mota na ce su fita ita da Alhajinmu suna ta murna da saka albarka. Daga nan sai gidan Ya Abubakar shima na kai masa ya gani. Na je har gidan Ya Aina na nuna mata sannan na koma gida na É—auki hoton motar na yi status da ita sannan na yi caption a kasa da cewa.
"Alhamdulillah. Yallaɓaina ya gwangwaje ni da mota jiya. Matar Yallaɓai ta yi mota jama'a ku ta ya ni murna."
Nan da nan aka yi mini caa Sadiya kin yi mota! Congratulaton Mimiaco ta ce kin chanchanta ta Yallabai. Ita ce kaɗai ta yi mini murna sai su suwaiba da Nasara da Jamila. Gimbiya ta gani amma ko Allah ya tsare ba ta ce ba, Ya Hamza ya turo mini rawa kafin ya ce" Lalle Yallaɓai ya iya gwangwaja danƙari. Allah ya tsare "
Adanan kuwa faÉ—i yake yi" Ya Sadiya kin rigani yin mota? Na ce to ka zauna ni ai na yi gaba.
Su Maijidda da Samira suna ta mini fatan alheri.
Munnira da Hauwa gida suka zo yi mini murna, da za su tafi na tuka su na kai kowacce gidan ta. Ni fa tun da na yi mota na dai na zaman gidan ni ce can ni ce nan, har Jidda ni ke kai ta wajen koyon kwalliyarta tun da sun gama na snacks, sati mai zuwa ma zata je zariya yin POS UME. Ni ce har Gwammaja na kai ma su Nene mota suka saka albarka. Lokacin Jawahir da Umma Salma sun zo ganin gida suma sun saka albarka suka ce ai na caancanci mota na kuma chanchanci na shiga na fita. Yallaɓai ai nawa ne an sha gwagwamarya.
Wajen sati biyu ban zauna a gida ba, Yallaɓai ya gaji ya ce na zauna na huta har abada fa motar nan tawa ce sannan na hakura gani nake yi kamar zai ce na kawo key ɗin an fasa za a mayar ma da masu shi. Faridan Tariq ta ce itama a satin Tariq ya siya mata na ce mun yi amarya a tare. Anty Zabba da muka yi waya ta ce ta yi mini murna yayan shi da ya ji sai ya ce ya kyauta muka yi ɗan tsegumi har tana ce mini yanzu sai Gimbiya ta daina yi mini gani gani anan ne ma na ke faɗa mata ita da su Anty Bahijja ba su yi mini murna ba.
Ta ce na raba su hassada ne da bakin ciki na ce sai dai ya koma musu kuwa. Ba sa gabana ta ce ya fi haka.
Ni ina gida ban san wainar da ake toyawa ba. A satin da Jidda ta tafi Zariya gidan Ya Hamza ta sauka bayan ta gama jarabawar ba ta dawo Ya Hamza ya ce sai sakamako ya fito za ta dawo. A Safiyar litin Ni kaɗai a gida Baby na makaranta daga ni sai Yumna da ta koyi shegen ɓarna tana tafiya turba turɓa da ƙyar, Yallaɓai ba gidana ya kwana ba bai kuma shigo da safe ba sai na yi tunanin fitan gaggawa ce ta kama shi, da man wani lokacin in bai samu dama ba sai dai mu yi gaisuwar ta waya.
Wajen sha ɗaya na safe Sameena ta kira waya muka gaisa tana yi mini murna. Har ina mata tsiyan ta makara ta ce mini wallahi ba ta ji labari ba sai satin nan da ta je gida ta ji ana ta rigima kan motar. Ashe har yaji Gimbiya ta yi akan Yallaɓai ya siya mini mota. Saboda ta yi masa maganar siyayyan kayan haihuwa ya ce ta jira sai ya siya mini mota sannan zai dawo kanta shi ne ta suka yi tsiya fata fata har ta yi yaji. Kwananta hudu a gida amma ta dawo shekaranjiya yara ma can Gwamnaja aka kai su wajen Nene.
Na yi ta mamaki domin Yallaɓai bai ba ni wata alama ba, tun da ni dai bai zo gidana ya kwana ba ashe shi kaɗai ya riƙa kwana don kar na fahimci wani abu. Sameena ta ce tana gidan shekaranjiya asabar Yallabai ya je can Rano tare da Kawu aka zauna ana ma yar da magana Gimbiya tana ta kuka tana faɗin ba ya yi mata adalci komai ni komai kamar na shanye sa shi ne ya ce e na shanye sa ne, itama za ta iya shanye sai bai hana ta ba mota ne ya siya mini haihuwa kuma tun da ba gobe ba ne ta jira ta gani in bai ba ta kudin siyayyan ba sai ta yi magana. Sai da Tafidan Rano ya shiga maganar sannan ta biyo sa suka dawo gida tare.
Na jinjina lamarin Gimbiya a raina sosai. Hasashena ya kasa hasaso mini tsanar da matar nan ta yi mini ta zo ta same ni da mijina amma tana neman ta hana ni zaman lafiya! Kwana na yi ina auna abin a kasan raina wai ta yi ya ji saboda an siya mini mota. A bakin Sameena na ke ji tana cewa itama ai ta yi ta yi ya sauya mata mota ya ƙi. Amma ni ya siya mini shi kuma ya ce ita tana da shi, ni kuma ban da shi shi ya sa ya fara siya mini tun da ni ce uwargida. Ta jira in ya samu kuɗi sai ya sauya mana gabaɗaya ta ce Hajiyarsu na ta yi mata faɗan ita ba ta ga ƙoƙarin da ya ke yi ba miye don ya siya ma matarsa mota shekara nawa suna tare bai siya mata ba sai yanzu? Ita na za ta gode ma Allah da ni'imar da ya yi mata sai ta bari sheɗan na yi mata susa a kunne. Ta bakin Sameena ta ce bakin ciki ƙiri kiri Gimbiya ta nuna akan an siya mini mota. Ni ko da gayya na ce ta ko fara gani in sha Allahu sai dai ta mutu in ba za ta iya ba ta fi ta bar ni gidana da mijina daman a ciki ta zo ta ganni na matsa mata amma shi ne za ta yi mini butulci.
Kamar in yi ma Yallaɓai magana sai na fasa ganin shi bai faɗa mini amma na riƙe ta a raina, a satin da na ji maganar muka haɗu a Gwamnaja Maman farko ce ta zame daga bene ta samu gocewa shi ne na je dubata kuma da motar na je a ɗakin Nene a gaban Anty Bahijja da ita kanta Nenen na kalli Gimbiya na ce mata.
"Gimbiya Yallaɓai ya siya mini mota kowa ya yi mini murna ban da ke ko ba ki sani ba ne?
Da gayya na faɗi haka, ai sai ta ji kunya ta fara kame kamen wai kwana biyun nan ba ta ji daɗi ba ne ta so ma ta zo har gida ne ta yi mini murna. Kallonta kawai na ke yi ni sai na raina wayan ta. Matar da ke da shago guda amma ɗan abin da Yallaɓai yake yi mini ya hana ta sukuni.
"Allah Ya sanya alheri."
Na amsa da Amin ina kaÉ—a key É—in hannuna.
"Kema Anty Bahijja ba ki yi mini murna ba."
Duk na kunyata su, ita da yake akwai isa kai tsaye ta ce" Kin kawo mini ita har gida ne kika ga ban yi miki murna ba?
Sai na nuna mata na fita iya bariki kai tsaye na ce" Ban kai miki gida ba amma yau ga ta can a haraba na zo da ita. In za ki fita ki duba ta, ki saka albarka Anty Bahijja."
Sai ta kasa magana Nene na wajen ta saka baki ta ce ba su kyauta. Abin alheri ne ya same ni yana da kyau su yi mini murna sai ga shi jiki an sanyaye da zan tafi suka fita ganin motar suna saka albarka na ciki na ciki. Halima ina haraba ta shigo yadda ba ta gaisheni ba, nima ban nuna na ganta ba, na shige mota ta ni da Yumna na yi tafiyata suka bini da kallo har na fice a raina na ce ku yi ku gama. Babu yadda kuka iya da ni nan gani nan bari É—umammen Manya.
*Janafty**TKGB3M013*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LgZezgwmkmy8ZCuNsHiNxX
Assalamu Alaikum Fanmily, mun fara saro muku kayan Kitchen ko wani nau'i, duk abin da kuke bukata na gyaran Kitchen ɗin Amarya da uwargida duk za ku same su a JANAFTY KITCHEN ITEMS, kayan mu masu kyau ne da inganci sannan za ku same su akan rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina a falin Nigerian nan. Domin karin bayani ku tuntuɓe mu ta waɗannan lambobin kamar haka.
09069067488.
+234 706 234 9732
Muna maraba da masu siya ɗaya ko sari🥰
Shuru na yi da bakina kamar yadda Yallaɓai ya yi shuru bai faɗa mini ko ya nuna mini sun samu matsala da matarsa saboda ya siya mini mota. Nima sai na yi kamar ban ji wata magana ba na cigaba da sabgogin gabana. Addu'a kawai nake yi ma Jidda akan Allah ya ba ta sa'a ta samu gurɓin karatu a jami'ar bayero saboda ta ƙwallafa rai sosai akan makarantar.
Cikin ikon Allah satin ta ɗaya a Zaria Khaleesat ta kira ni tana faɗa mini Jidda ta ci Jarabawar da ta yi, na yi ta murna da farinciki Yallaɓai na dawowa na faɗa masa sai ya ce mini Jiddan ta kira shi ta faɗa masa, har yana cika baki da cewa shi da man ya san abin da ya haifa he is sure za ta tsallake, baki na saki ina kallon Yallaɓai yana yaɓon ƴar sa, har yana kallona yana ce mini ƙwakwalwarsa ta biyo shi ya sa take da hazaƙa.
"Me kake nufi Yallaɓai?