Sashe 4
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka na tsai da shawara da ni da zuciyata ko Amina ba ta sani ba. Washegarin da muka yi maganar da ita Gwaggo ta kira waya ta har gabana ya faɗi na ɗauka ma ko maganar ba na gida ta je musu ne amma sai na ji ta ce kwana biyu ta ji ni shuru ne ya sa ta kira ni. Ga ma Alhajinmu nan ya na ta cigiya har ta ba ni Alhajin mu ka gaisa ya na min zolayan shi da ya saba na Hajiya Dubu kwana biyu. Sai na yi ƙaryan ba na ɗan jin daɗi ne shi ya sa har muka gama waya ina ɗari dari saboda ba na so su ji wani abu yanzu na fi so komai mai zai faru ya zama na tsakanina da Yallaɓai ne kamar yadda aka saba. A ranar har Marwa ma mun yi waya da ita amma itama ban faɗa mata ba saboda da ta ji Kawu Abba ya ji shi kuma in ya ji zai yi shuru ba faruwan haka sai Yallaɓai ya dauka shi ɗin ya isa ne shi ya sa na kai ƙaran shi wajen abokinsa kuma ɗan'uwan shim shi ya sa ban bari ma ta fahimci wani abu ba.
Ranar da na ke da kwana ashirin a gidan Amina da daddare Gimbiya ta kira wayata. Har sau biyu ban ɗauka ba saboda ban san me ya haɗa ni da ita da za ta kirani ba sai da na ga kiran ya ƙi ƙarewa sannan na ɗaga kiran amma maimakon na ji muryanta sai na ji muryan Jidda.
"Jidda."
Na faÉ—a ina mai tashi zaune saboda mamakin jin muryan ta ban za ta ba.
"Na'am Umma mun yi kewar ki yaushe za ki dawo?
Ta faÉ—a cikin sanyin ta a koda yaushe.
" Ina nan dawowa Jidda. Kuna lafiya? Ina Baby?
"Ta na can falo ita da Abba da Anty Gimbiya."
Wani abu ya tsaya min a ƙasan maƙoshi da ƙyar na ce" Wa ya ba ki waya?
"ÆŠauka na yi Umma ba ta sani ba. Ina ta tambayan Abba yaushe za ki dawo ya ce kin je Kaduna gidan Umma Amina."
Ashe dai bai manta da in da na je ba. Lallashin Jidda na yi da cewa zan dawo kwanan nan, na ce ta gaishe min da Baby ina nan dawowa muna magana wayar sai na fara hawaye a ƙasan zuciyata ina ta tsine ma Yallaɓai domin shi ne ya yi sanadiyar da na yi nesa da ƴaƴana. A ƙasan raina ina jin daɗi in na tuna yau ni na samu ciki duk da ya zube amma dai na samu sassaucin cewa wataƙila mahaifata za ta iya ɗaukan ciki ba shike nan ba kamar yadda na ke tunani a baya. Ke nan gidan Gimbiya ya tarkata yaran ya kai mata? Oh itama ta ji in da daɗi godiyar ta ma ɗaya daga Jidda har Baby ba yara ba ne ban da girki ba ɗawainiyar da za ta yi musu girkin ma Jidda ta iya makaranta ne kaɗai cikas ɗin ta.
Da safe na tashi fuska a kumbure. Sai kuma Amina ta ke faÉ—a min Dr gobe zai dawo sai hankalina ya tashi.
"Amina zan zo na tafi ba zan bari Dr ya dawo ya same ni ba."
"Me ya sa?
"Da kunya Amina. To zaman me na ke yi a gidan sama da sati biyu?
Itama sai ta yi shuru domin ta hasaso abin da ni na na hasaso.
"Abin kunya ne fa Amina. Ke ƙanwata ba yayata ba."
"To Ya Sadiya ba sai na faÉ—a masa matsala kuka samu da Baban Jidda ba?
Hararanta na yi kafin na ce" Ban saka ki ba. Ba ki da hankali yarinyar nan."
Ina tunanin wucewa Yashe ya kamani gwara na fara shiri yau na wuce.
"To ina za ki je? Ko gida za ki koma?
"Ba zan koma ba Amina. Zan dai nemi wani wajen na je kawai"
"Ina to za ki je?
Sai na kalleta amma ban yi mgana ba na wuce cikin É—aki sai ta biyo bayana ta na na cin sai na fada mata in da zan je.
" Ke ki ƙyale ni "
Na faɗa ina jawo akwatina sai ta riƙe ta na faɗin" Don Allah ya Sadiya ki zauna Allah ba na son ki tafi."
Ta faɗa cikin shagwaɓa sai ta warce shi daga hannunta ina faɗin.
" Na ki wasa ne yarinya"
"Abuja za ki je?
Sai na kalleta shuru ina wani nazari ni ban kawo gidan Ya Auwal a raina ba saboda in dai na je sai ya ji ba a si ba kuma zai kira Yallaɓai. Dama dai Ya Hamza ne shi ne ɗan goya min baya amma shima ba zan je gidan shi ba saboda shima zai iya kiran Yallaɓai ni kuma ba na so ya ji a ran shi na damu da shi ne shi ya sa na je na kai karan shi yadda ya zaɓa nima haka na zaɓar ma kaina.
"A'a ba zan je can ba."
Amina sai ta kasa mgana, ni kuma na fara haÉ—a kayana kenan wayata da ke gefen gado ta fara kuka alamun ana kira Amina ta fi kusa da wayar ba tare da na kalleta ba na ce.
"Wa ye ke kira hala?
"Yallaɓai na."
Amina ta faɗa a hankali da sauri na kalleta cikin mamaki a kallo nawa ganin haka yasa sai ta miƙa min wayar na karɓa cikin san yin jiki.
A hannuna wayar ta yanke kuma ba daɗewa ya sake kira. Sai da ya yi min kira biyae bi da bi ban ɗauka ba sannab shuɗewar mintina huɗu tsakani saƙon shi ya shigo.
"Yaushe za ki dawo ne? Yara sun damu da tambarki."
 Yara ne suka damu ba shi ba, to tun da shi da ya ijiye ni bai dami ba shike nan yara kuma shi ne uban su tsaki na yi na dankwar da wayar gefe na cigaba da haɗa kayana Amina ta ɗau wayar ta na dubawa kafin ta ce.
"Ka ji wani kutumar uba wai yara sun damu? Shi ne fa ya damu ya rasa abin da zai ce shi ne ya fake da yara."
"Mtsewww.!"
Muka ja wani dogon tsaki a tare ni da ita sannan muka kalli juna muka yi dariya.
*Janafty**TKGB30B2*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
Itama Amina sai ta samu gefen gadon da nake zaune ta zauna lokaci ɗaya tana saka hannu ta na taya ni nin ke kayan da na zube kan gado muna kuma sakawa a cikin ƙaramar akwatina.
Allah ya sa ma sauran kayan Amina ta haɗa cikin wankin su mai wankin su ya zo ya karɓa an wanke su tas an kuma goge. Waɗanan da muke ninkewa zannuwa na sakawa a gida ne sai rigunan barci da wanduna sai unders su ne jiya da na samu sauƙin jiki na wanke su da kaina Amina ma ta yi ta yi na bari ta wanke mini na ce ta bar su zan iya yi da kaina.
"Ina za ki je daga nan Ya Sadiya?
Amina ta ƙara tambaya na ni kuma sai na yi mata shuru har muka gama ninke kayan gabaɗaya na ja akwatin na rufe daman sauran kayan na ciki na ja ta can gefen wardrope in da take a jingine sannan na koma in da na tashi na sake zama.
"Na ƙi ba zan faɗa miki ba."
"Don Allah fa na ce."
Ta sake marairaicewa kamar wata ƙaramar yarinya.
"To Yashe zan wuce."
Sai ta ƙwalalo ido ta na kallona kafin ta ce"Yashe fa Ya Sadiya?
Sai na gyaÉ—a mata kai kafin na ce" To ina zan je in ba can ba?
Sai Amina ta gyara zama har da matsowa kusa da ni ta na faÉ—in" in ba ki shawara Ya Sadiya?
Ina kallonta sai na gyaÉ—a mata kai kafin na ce" Me zai hana? Ina sauraran ki."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce" Gaskiya in dai za ki ji shawarata kar ki je ko'ina. In dai ba za ki zauna anan ba sannan ba za ki je Abuja gidan Ya Auwal ba, ko gidan Ya Hamza ba to shawarata ita ce da dai ki je wani wajen gwara ki koma gida kawai Ya Sadiya."
Ta gama faɗa har tana ɗaga mini hannu ni kuma daman kallonta nake yi kafin na daƙuna fuska ina faɗin.
"Wani gidan kenan?
"Gidan auran ki mana Ya Sadiya."
Wata uwar harara na jefa mata kafin na yi ƙaramin tsaki ina faɗin" Ai ni da ke na faɗa miki megidan har gorin gidan ya yi mini ko?
"To ai bai kore ki ba Ya Sadiya ɓacin rai ne."
"Oh kina nufin na koma duk cin kashin da ya yi mini ya tafi a banza kenan ko?
Da sauri ta ce" Ni ban ce ki ƙyale shi ya tafi a banza ba."
"To me kike nufi Amina?
Na faɗa a ƙufule.
"Ba ki ba ni dama na gama maganata ba ne shi ya sa."
"In jin ki."
Na faɗa a tsume har ina kauda kaina domin ita kanta Aminar sai na ji ta fara ba ni haushi so ta ke yi ni ta kwaye min baya ta goyo bayan Yallaɓai?