Sashe 98
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kasa mgana ya yi yana kallona ni ko na haɗe rai domin na yi alƙawarin yau ba zan yarda na ɗaukin renin wayau Yallaɓai da matan shi ba wallahi, gwara na tsage musu gaskiya in ba haka ba zai san ina yi mishi kawaici da kara ba ne.
Ya gama cika yana batsewa sannan ya kalleni kafin ya ce" Me ke faruwa ne a cikin gidana wanda ban sani ba?
Na yi kamar ban ji ba, saboda sai na ga tambayar ba ta shafe ni ba, tun da ya ce gidan shi a matsayin shi na megida ya saka ido mana ni ina ruwana.
"Da ke fa na ke mgana Sadiya kin yi mini banza"
"Ni?
Na faÉ—a ina nuna kaina.
"Aa ni "
Ya faÉ—a a fusace, ban bari ya sake É—auko wata mgana ba na tare shi.
"To ai na ga tambayar kamar ba tawa ba ce shi ya sa na yi shuru. Gidan nan fa naka ne in ma wani abu na faruwa kai ne shugaba kai ya kamata ka fara sani ba ni ba"
Wani kallo ya yi mini kafin ya ce" To na ji ni ina yini a gidan ne? Ke ce walikiyata duk abin da ya faru ki tsaya ki wakilceni in na dawo kuma ki zo ki sanar da ni."
"Ko?
Na faÉ—a ina kallon shi, sai ya kasa mgana su kuma sun yi shuru suna jin mu.
"E shi ya sa yau kika ɓata mini rai, ya za a yi har a yi dambe a gidana ba ki kira ni kin faɗa mini ba? Sannan kuma kika yi hukunci har kina zagin Rabi'atu kina cewa ita ce ba ta da kunya? Ita Gimbiyar kin binciketa kin san abin da ta yi mata har ta kai su ga Dambe?
Ya faÉ—a yana kallona ni baki na saki ina kallon shi, na jinjina kai na juya ina kallon Gimbiya itama sai ta kalleni baki a buÉ—e.
"Koma me ta yi mata ya dace ta yi dambe da ita! Sa'arta ne? Ban da siyar ma da kai mutumci, ji yadda ta kumbura ma matata baki? Koma me ya faru ba za a iya jirana na dawo ba ne?
Ya faÉ—a yana tsare ni da ido, mamakin shi na ke yadda idanuwanshi suka rufe akan Rabi'a..
"To ni yanzu me ye nawa a cikin wannan mganar?
Na tambaye shi ganin kamar ni ya fi jin haushi.
"Naki shi ne ba ki yi hukuncin kan gaskiya ba, kin goyi bayan Gimbiya tun da kuna tare, sannan ni ba ki kirani kin gaya mini ba? Kin kyauta kenan? Girman kenan?
Na buɗe baki haa ina kallon Yallaɓai Gimbiya ta saki sheewa ta tafa hannu ni ko na ma kasa mgana tsabar mamaki.
"Ni fa Abba abu É—aya ya yi mini zafi, wai Maman Jidda ta ce ina yi musu rashin kunya! Kuma ni wallahi ba wacce cikinsu na ke yi ma rashin kunya Maman Khalifa ce yau daga zuwa na yi mata mgana ta fara zagina"
Ta karishe faɗa har tana shessheƙan kuka, kawai sai Yallaɓai ya juya wajenta yana faɗin" Ki yi shurun ki ai na san halin kowa a cikin ku, tun tuni ba ki yi rashin kunya ba ne sai yanzu? Da man ita Saudatu fitinnaniya ce, na san za ta aikata ita kuma Sadiya ban san ta da bangarenci ba sai yau, amma duk zan yi mganin abin yanzu nan."
Ya faÉ—a yana nuna mu da yatsa, a kausashe, Gimbiya ta sake sakin shewa kafin ta ce" Za ka sake mu ne? Shi ne karshen mganin mu da ka ce za ka yi ko?
Ta faÉ—a tana tsare shi da ido, shi kuma sai ya taso mata tana faÉ—a yana faÉ—a, har yana ce mata hakuri kawai yake yi da ita darajan iyayansu. na gaji da hayaniyar sai na saka baki.
"Don Allah ku yi hakuri wannan fa ba girman ku ba ne."
Daga ba da hakuri kawai nima Yallaɓai ya dawo kaina yana yi mini masifa.
"Ai duk laifinki ne, haÉ—a kai kuka yi za ki kashe mini mata ko? Don kun gan ta yarinya ko?
Ban san na mike ba sai da na ganni tsaye kan kafafuwana.
"Dakata."!
Na faɗa da karfi ina ɗaga ma Yallabai hannu idanuwana har rufewa suke yi saboda bacin rai da bakin ciki wallahi tun da bai san ina yi masa kara ba yau sai na yi ma yallaɓai wankin babban bargo.
"Ka dakata Yusuf.."
Na sake faÉ—i cikin É—aga murya, saboda raina ya baci zuciyata ma tafasa take yi a lokacin.
Ba shi ba, har matan na shi tsayawa suka yi suna kallona saboda mamakin tsawar da na daka masa.
"Ni kike yi ma ihu Sadiya??
"An yi maka Ihu, an yi maka ihun Yusuf ka yi abin da za ka yi don Allah Haba."
Na faÉ—a ina yarfa hannu, bayan na nuna shi da hannu, sai na ga kawai ya tsaya yana kallona cikin mamaki.
"Maman Jidda yau ba Yallaɓan?
Gimbiya ta faÉ—a cikin mamaki.
"Na bi yallabai da gudu, haba ka isheni a cikin gidan nan da fitinarka, na yi maka shuru na yi maka shuru amma na fahimci ba ka san kara ba, kuma ba ka san ina yi maka kawaici ba, to wallahi na gaji, na gaji da jidalinka da na matanka na gaji Yusuf"
Na ƙarishe faɗa ina ƙara daga murya saboda a lokacin ji na yi zuciyata ta yi duhu ko gani ma bana yi saboda bacin rai.
Sai falon ya yi shuru ganin na harzuƙa.
"To yi hakuri zauna mu yi mgana."
Yallaɓai ya faɗa cikin sigan lallashi ganin yadda na taso masa ya san halina in na fusata ba ni da kyau.
"Ba zan zauna ba, lokacin da na ke zaune ba ka so a yi mganar cikin laluma ba, yanzu sai dai kai ka koma ka zauna ka saurareni domin ni ce zan yi mgana."
Ban jira cewarsa ba na cigaba da faɗin" Yusuf auren soyayya ne a tsakanina da kai, a shekarun mu har zuwa matakin yau ba ka taɓa fahimtar cewa ina yi maka kara ba ne? Ba ka taɓa jin cewa a ranka kana yi mini wasu abubuwan da suka yi kama da cin fuska ina kyaleka ba! Mene ne ba ka yi mini ba, mene ne ba ka faɗa mini akan auran ka da Gimbiya ba? Wani baƙincikin matanka ne ban ƙunsa ba? Wani takaicin yan'uwanka ne ban ƙunsa a cikin zuciyata ba? Mun yi aure tun ba ka da komai muka yi gwagwamaryan arziki tare, daga baya da me ka saka mini? Ka yi mini gorin haihuwa na yi haƙuri, ka yi mini na gida na yi hakuri, ka yi ta mini alƙawaruka amma ba ka cika ba, na yi maka mgana? Ka nuna mini bambamci a kan matanka na taɓa yi maka mgana? Ka goyi bayan yan uwanka a kaina na yi maka mgana? Gimbiya ta yi mini abubuwa ta ci kasuwa a kaina kala kala amma duk ban ɗaga kaina ba, saboda kai Yusuf. Saboda karan da na ke yi maka, shi ya sa duk kake yi mini wasu abubuwa ba na ɗaga kaina, ba wai don bana jin zafi ba ne, sai domin ina kauda kai saboda kai, saboda ina daraja zaman mu da kai, ina daraja auran mu da soyayyarmu, ina kambama tarbiyan da iyayena suka ba ni, sabo da ina girmama bautar ubangijina, ka danne mini haƙƙi, ka yi mini wulaƙanci akan matanka, ka tozartani a kan su na taɓa yi maka mgana? Ka taɓa zama ka yi tunanin abubuwan da kake yi mini rashin kyautawa ka ware rana ɗaya ka ba ni haƙuri? Don ina matarka uwargidanka sai na zama bolarka, don ina haƙuri da kai sai na zama mazubin sharan da kai da matan kuke zuba duk dattin ku a kaina? Ɗauka ka ke yi alfarma ce ka ke yi mini da na ke zaune da kai? Wallahi tallahi na rantse da wanda raina ke hannun shi Darajan aure ne, bautar ubangiji ne ya sa na ke raga maka, amma ba domin haka ba wallahi tallahi ba ka isa na zauna kana cin kasuwa a kaina ba. Ba ka isa ba Yusuf ba ka isa ba wallahi, daga kai har waɗanan matan da ka ajiye a cikin gidan ba ku isa ba."
Na karishe fada ina nuna shi da yatsa manuniya, bayan shi suma na nuna su ɗaya bayan ɗaya cikin baƙin ciki, domin gabaɗaya na rasa control a kan ɓacin raina ji na ke yi auran na Yusuf kwata kwata ya fita kaina da gidan shi da matan na shi duk na yi nisa da su ko zan samu salama da kwanciyar hankali.
Na sake buɗe baki in yi mgana na kasa Kuka ne ya taso mini da ya sa na kasa ƙarisawa, su ko gabaɗaya sun yi shuru sun kasa mgana dukkansu sun nemi waje sun zauna saboda mamakin maganganuna.
Ina da tabbacin ko shi da muka kwashi shekaru tare, bai taɓa ganina na yi masa hauka ba, sai yau balle su da suke baƙin ganin ɓacin raina.
Ina kuka na cigaba da faÉ—in.