← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 103

Sashe 76

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bakin Suwaiba na ke jin wasu mangaganun, sun ce ni ce ke zuga shi saboda na ga ba ni za a yi ma kishiya ba ni in suna faɗar haka har mamakinsu nake yi mijina ne fa zai ƙara aure? Ni ba mace ba ce ba zan yi kishi ba? Ba dangin Yallaɓai kaɗai na ke shan zagi ba hadda na su Giimbiya a can Rano. Sameena ta kira ni a waya tana faɗa mini mganganun da ta ji a kaina marasa daɗi.
Wai na ki yadda mu haɗa kai da Gimbiya na koma gefe ina munafutarta wai tun kafin Amaryan ta shigo na ke ta tusa kaina a wajen yar cikina. Mangaganu dai marasa daɗi, ni ko na yi mata rantsuwan duk abin da ta ji ƙarya ne na yi mata cikaken bayanin abin da ya faru  da wanda ke faruwa.

"Sameena na isa na hana Yallaɓai aure? Ni ban isa ba shi ya sa na koma gefe na zama yar kalllo. Itama shawaran da na bata kenan ba ta ɗauka ba, ta biye ma su Anty Bahijja suna faɗa mata cewa ni ina jin daɗin auren da Yallaɓai zai yi sabo da ita. Sun manta nima ɗin mijina ne kuma mace ce ni, ina da kishi sai da na saka haƙuri kuma na roƙi Allah ya cire mini zafin kishi. Kuma ya cire mini shi ya sa na ke zaume lafiya su kuma shi ne ba su so, sun so ne yadda take hauka nima na biye mata duk mu zama mahaukata."

Sameena ta ce "wannan gaskiya ne. To kuma ba a kishiya ke kika bari aka auro ta,? Duk ta manta baya? Wallahi tana ta rigima domin jiya ma mun yi waya da Hajiyar mu take faÉ—a mini case É—in gida ma ake yi "

"Gida?

Na furta cikin mamaki domin ni ban ma san da maganar ba
Sai da ta yi mini bayani ashe Gimbiya ta yi tsalle ta ce Amarya ba ta isa ta fara tarewa a gidan ba kafin ita ba.

"Ikon Allah."

Na faÉ—a ina jinjina kaina.

"Wallahi an ce magana har Baba Tafida ya shiga ciki. "

"To ya ake ciki yanzu?

"Ban sani ba. Amma dai an ce Ya Tafida ya ce in har ta ga ta tarewa a gidan nan to kema kin tare ne amma tun da ta saka tsiya sai ya gani É—in."

Ni ma kasa magana har muka yi sallama da Sameena. Kenan da gaske Gimbiya take yi? Illau ko kwana biyu da maganar mu da Sameena Yallaɓai ya shigo mini gida da rana kamar kabubuwa ranar a gidan Gimbiya ya kwana ban san kuma me ya faru ba kawai ya ce nima na shirya za mu tare a sabon gida a ƙarshen wata bai ma ba ni damar magana ba ya fita ya shiga mota ya ta fi. Hankalina ya tashi saboda ban shirya komai ba ina ni ina tariya ni da Yallaɓai ya yi ma manyan falo uku da bedroom huɗu na su Gimbiya ne falo Biyu bedroom biyu. Ina na ga kayan da zan yi wannan tariya ai ba tariyan sauri ba ne sai na natsa.

Na rasa yadda zan yi, a yadda Yallaɓai ya zuciya ban isa na kawo wata magana ba. Domin a daran ma da ya dawo ina fara magana ya dakatar da ni.

"In dai maganar tariyan gida ne bana son jin komai. Ki shirya ki tare a ƙarshen wata nan."

Tun da na ji haka na san akwai matsala na rasa wa zan tun kara, na yi niyyar na yi sabbin labulaya. Da Zannuwan gado da É—an abin da baa rasa ba sauran abubuwan daga baya in Allah ya hore mini sai na yi. Ni kwata kwata ban shirya ba, har ya faÉ—a ma yara suna ta Murna su Jidda har sun fara parking É—in kayan su har Yumna tsalle take yi za su koma sabon gida.
Ganin ya ƙi saurarena ya sa na kira Mimisco na sauke murya ina faɗa mata uzirina.

"Ke ma kin yi magana Sadiya. Amma kin sani ki yi shuru kar ki yi masa mgana a yanzu yana cikin tsini ne, ki bari nan da sati É—aya in ya huce sai na yi masa mgana."

Sai na ce mata to, ban tambayeta ba da kanta ta fara faɗa mini matsalan da aka samu. Gimbiya ta matsa sai ta fara tarewa magana har magabanta ta sun shiga. Hajiyar Tafida ta goyo bayan yarta har tana cewa Tafida bai yi adalci ba ta ya ya wata can za ta fara tarewa ba mu ba, in ni ba zan tare ba amma ya zama dole ita Gimbiya ta fara tarewa. Shi kuma ya ce ba za ta taren ba, ya ɗauka ta gama fahimtarsa ashe ba haka ba ya cije ya yi taurin kai sai da magana ta kai wajen Nene ita ta tursaashi ya amince amma da sharaɗin sai dai mu tare ni da Gimbiya amma ba ita kaɗai ba. Ni dai Gimbiya ce ta kusa ja mini bala'i ina zaman zamana amma tun da Mimiaco ta ce za ta saka baki na san za ta yi mini iya ƙoƙarinta illai kuma ta yi domin sai ga Yallaɓai da kan shi ya zo mini da maganar.

"Me kika ce ma Mimisco?

Sai na gyara zama ina faɗin" Na fada mata ta roƙar mini kai. Ka yi mini alfarman tariyana sai bayan bikin ka sai na tare a tsanake."

Kallona ya yi amma bai yi magana ba ganin haka yasa na gyara zama ina sake faɗa masa hujojina, bai wai ya gamsu ba ne kawai dai ya dakatar dani da cewa" Shike nan tun da kowa abin da ya ga dama ya ke yi. Ni dai Allah na gani ina iya bakin ƙoƙarin sauke nayin da ke kaina. Wacce acikin ku take ganin ina cutar da ita Allah ai yana sama yana kallo."

Sai na ji wani iri a cikin zuciayata da maganaganunsa.

"Ka yi haƙuri. Bari kawai sai na tare tun da haka kafi so."

"Kar ki damu, ki yi na ki tsarin itama can ta tare a lokacin da ta so ba shike nan ba."

Sai na kasa magana saboda a daƙune ya yi maganar kuma tun daga lokacin bai sake ɗaga maganar ba sai na fahimci Gimbiyar ta gama ɓata ma Yallaɓai rai kan mganar gidan nan ba ma ya son maganar kwata-kwata amma ni tun da na samu ya amince shike nan na kama kaina ban shiga abin da ba ruwana ba. Ya faɗa mini ya fara ba ma Rabi'a wasu kuɗi na lefe tun da farkon wata mai kama za ta koma can maiduguri sai an ɗaura aure kamar wasa na ce ya ba ni kwangilan hijabai da iners na Amarya ban ɗauka zai amince mun yi maganar yau washegari ya zo mini da maganar na yi list ɗin komai amma mu yi magana da Rabi'atun na ji size ɗin ta. Jin zan samu nawa a sama ya sa da gudu na amince, na neme ta a wayar Jidda muka yi magana ta tura mini size ɗin bra ɗin ta pant, sai na hijabi adadim yadin da take sawa duk ta tura mini da kalolin da take so.

  Nan take na tura bangaren Hijabai, inears ɗin kuma na shirya da kaina Jidda ta rakani muka shiga kasuwa a rana ɗaya muka siyo komai. Na ci riba domin Yallaɓai bai yi mini ƙauron kuɗi ba isassu ya ba ni. Kuma da ya dawo ya ga kayan shi kan shi ya yaba. Sai da aka kawo hijaban sannan ya kwasa ya kai mata ta haɗa da sauran kayan, abin da aka yi daga ni sai Yallaɓai sai Rabi'atu sai ga magana na yawo a dangin Yallaɓai wai saboda neman gindin zama ni ce na haɗa ma Amarya lefe. Hauwa ta kyanƙyaa mini maganar ta ce a bakin Halima ta ji, sai ga shi na je barka gidan Jamila da ta haihu muka haɗu  da Anty Bahijja ta shaguɓa mini magana da cewa na dai na murna na sani duk abin ka yi shi za a yi maka.

Ni ko na amsa da cewa haƙƙun kuma in ka shuka alheri ka ga alheri in sharri ne ma shi za ka gani. Na kuma ƙara mata da cewa a wannan zamanin ma abin ba ka yi ba shi ake yi maka ballanta ka yi.
Abin da ke ba ni mamaki a ina maganar ta fita? Sannan ma ba za a faɗi gaskiya ba sai an ƙara da sharri. Ni su Hauwa kawai na faɗa ma gaskiyan magana sauran ban damu ba su cigaba da yaɗa duk abin da suka ga dama. Sai da na yi ma Yallaɓai magana na ce ko shi ya yi maganar da wani a can Gwammaja? Sai ya ce ya faɗa ma Nene ina jin haka na ce wata ƙila ita ce ta yi zencen da ya'yanta su kuma da man suna adawa suka ƙara ma labarin gishiri da maggi tun da ba sa son zaman lafiya. Tuni na fita batun su na kama harkan gabana fafutaka na samu yan kudaɗen da zan rage siyayyan tariyan sabon gida. Na samu na labule sauran cafet da zannuwan gado cikin riban siyayyan Amarya Yallaɓai sauran kuɗin da ke hannuna duka zan haɗe su waje ɗaya mu ga abin da Allah zai yi. Shi ya sa duk na faɗa ma su Ya Hamza za mu tare a sabon gida kuma akwai falo ɗaya da bedroom biyu ban san me zan saka ba.
Chapter 76 · 0% Book details