← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 103

Sashe 58

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abinci ta ce a kawo mana sai na ce a kai mana falo can za mu koma, ba mu ma kai ga barin dakin ba sai ga Suwaiba ta iso tare da ita muka fita falo ana ta hira. An kawo mana abinci tuwon shinkafa mai naman rago. Sai dambun zogale sai alale, sai muka haɗu da ni da Suwaiba da Hauwa muna cin abincin ina tambayan Jamila ta ce itama yau ƙanwar mijinta ake suna ta haihu sai anjauma za ta leƙo. Muna cin abinci muna hira su Marwa suka dawo in da muke suka zauna a cikin hiran ne Hauwa ke maganar me ya sa ba ta ga Suwaiba da ankon sunan ba?

"Wa? Mu a suwa. Naja ta tura mini na ce ba ni da halin yi."

"Au da man ankon ma sai wanda ya isa ake nuna ma wa?

Hauwa ta faɗa tana riƙe baki. Suwaiba na dariya ta ce" Ku ba a nuna muku ba? Wataƙila saboda Sadiya ne domin na ga ana kishi da ita ko sunan ma in kun lura yanayin na Yumna aka kwaikwaya. Duk haihuwar su Khalipa ba ta yi anko ba sai wannan?

"Uhm'

Kawai na iya cewa kafin na yi magana Ashe ta karɓe da cewa" Wai ba a nuna muku ankon ba da gaske?
"Wallahi ba mu sani ba."
Na rantse mata sai ta yi kasake kafin ta ce" To har Rano wannan akon bari mu ku ji."
"Zai kai can mana. Kun manta gidan su na can ne."
In ji Suwaiba, Marwa ta ce itama Anty Bahijja ta tura ma Kawu Abba ya ce ba zai siya ba sunan ne sai an yi anko. Shi ne ta ce ai nima da na haihu na yi anko kuma ya siya mata a lokacin shi ko ya ce ba shi ya siya ba da kuÉ—inta ta siya a wancan lokacin. Yanzu ma shine ya nuna mata in tana da kuÉ—i ta siya Marwa ta ce ita kam ba ta da kuÉ—i ba ta siya ba.

"Ikon Allah.!

Suwaiba ta sake faÉ—a tana mai mamaki, Hauwa ta ce da man ko na Yumna ba su yi ba gwara ma da ba su nuna mana ba muma ba za mu yi ba.

"Da sun sanar damu za mu yi ko don mu tura musu Aniyar su."

Na faÉ—a ina mirmishi.

"Wallahi kuwa."

In ji Marwa.

Muna ta hiran mu, Naja ta zo ta ga ba a kawo mana ruwa ba da kunin Aya ba.

"Wa ya kawo muku abincin?

Ta tambaya tana kallon mu.

"Maryama ce ta kawo musu abinci ba ruwa ba lemu."

Ashe ta faɗa cikin gatse sai Naja ta yi dariya ta ce Ashe ta biyo ta karɓo mana. Ita ta bita sai ga shi ta dawo da ruwan gora da fanta sai kunin Aya da zobo cikin wani roba. Tana ta masifa wai an ce Maryama ta ba da zobo da kunin aya tana wani daga kai.

"Har tana ce mini ba kin sha ba ke Ashe? Na ce na sha in zan ƙara za ki hana ni ne?

Na kwashe da dariya ganin yadda Ashe ta yi da baki tana kwantata mana yadda suka kwashe da Autar su Gimbiya.

"Sai ta ce me?

In ji Suwaiba itama tana dariya.

"Me kuwa? Ta yi shuru ai ta san ni yadda ba ta taɓuwa nima haka. Naja ta ce na ku ne sai ta wuce ta buɗe dakin ta ba ni."

Hauwa na dariya ta ce"Da man Maryama ba ta da dama. Ga rashin kunya da ta yi auran nan ne ma ta yi sauƙi."
"Rashin kunya ai duk tare muka yi muna yan mata. Ni yanzu ai sai dai ta nuna mini zaman agolege ni kuma na gwada mata na Sulaja."
Ni dai dariya har ina kwarewa, Yunma na zaman jikina ina ba ta alale har tana sulmiyowa.

"Ke da man ba cikin garin Lagos É—in take aure ba?

"In ji wa! Ko dai ake raina ma wayau. Tana cikin garin Agege can mijinta yake kasuwanci. Shine da ta zo garin ta yi ta buÉ—a hanci wai ita a dole tana auran miji mai kuÉ—i suna zaune a garin lagos. Allah na tuba wallahi ko ni da mijina ke aikin gwammati a kallon farko mai hankali in ya yi mana ya san na fita jin daÉ—i "

Ni da Suwaiba muna tsintsira dariya ina faÉ—in Munnura ta yi missing na so tana wajen nan da an ji muryanta a sama. Abin da ya É—an tsagaita hiran ma Faridan Tariq ne ta kira ni a waya ta ce ita ba ta samu zuwa ba suna sai sallar azumi take tunanin za su shigo garin. Sai na ke faÉ—a mata ina gidan sunan gamu nan ana ta hira ana dariya ta ce na gaida kowa da kowa. Muna zaune a falon sai ga Mubeena ashe tana makaranta suna da test duk ta sha wuya Naja na yi ma magana na ce a kawo ma Mubeena abinci daga makaranta take. An kawo mata itama irin na mu, muna nan muna ta hira sallar la'asar ne ya tada mu bayan mun yi salla mun idar muka fito an kira mai hoto kamar dai lokacin sunan Yumna.

Mun fiffito, sai ga Munnira yar halas ita da Hadiza ƙanwarta tana ko ganin mai hoto sai da ta riƙe baki kafin ta ce" To pha sabon salo tusa a lasifika."
"To za ki fara ko?
Hauwa ta tare ta, tana dariya.
"To ai na ga ana ta so a kwaikwayo mu ne."
"Ai komai ma irin naku ne. Ba ki ga har da su anko ba.?
Suwaiba ta fada mata tana dariya Munnira ta waiga ta sake waigawa kafin ta saki shewa da ƙarfi tana faɗin" Ahayye nanaye. Yau ina ganin abin da yafi karfina ni haihuwar mutun biyu"

"Kishin ne har da na suna?

Hadiza ta faÉ—a tana dariya Ashe ta ce" To miye ma ba a yi ma kishi yanzu? Kishi ya zama É—an gata yanzu."
Ni dai ganin hankula sun fara dawowa kanmu na ce Munnira ta yi wa Allah ta yi shuru
"Zan yi shuru amma in na ga abun da zan magantu wallahi sai na mangantu."
"Nima ina bayan ki."
In ji Ashe har suna tafawa sai na lura hatta Hadiza irin su Munnira ne,  har tana cewa tun da dai a dake ba za mu dakun ma kowa ba ai da sauƙi.

"Ni dai ku rufa mana asiri mu bar gidan sunan nan lafiya kafin a yi mana rubuti."

"Ai wallahi ba wacce ta isa tab.!"

Munnira ta faɗa har tana ɗaga murya na balla mata harara. Munnira ba ta shiga ciki ba sai da aka gama hotuna yadda ba a gayyace mu, mu ma ba mu tura kan mu ba, ni ko a sunan Yumna na kirata mun yi amma ni ko kallona ba wanda ya yi. Su Naja ne da su Anty Bahijja sai ƙawayenta da dangin ta ba ma kamar Maryama ɗin nan na yadda ta cika kauɗin tsiya.

Bayan an gama hotunan muka dawo cikin gida muka zazzauna a falo muna hira. Munnira ina kwabarta sai da ta yi ma Naja magana wai an fidda anko an nuna ma waÉ—anda aka so.
"Haba. Ban tura muku ba? To wallahi na manta ne"
Ta faÉ—a daga ji ma karya ne, Suwaiba ko ta ce" Sadiya ai ba a waya ya kamata a nuna mata har gida ya kamata a kai mata ta gani."

"Anty Suwaiba abubuwan sun yi mini yawa. Jibi za mu bar kasar ni da Honey. Ankon ma Gimbiya ba ta so a fitar ba ni ce na matsa. Mantuwa ne duk wanda ban turamawa ba ya yi hakuri."

"Ai ba komai. Kun hutattashe mu da kuÉ—in mu "

In ji Munnira.

"Afuwan Anty Sadiya."

Naja ta faÉ—a, tana kallona ni ko sai na yi mirmishi na ce ba komai. Nan dai ta wuce tana juya mazaunai.

"Ƙarya take yi wallahi kunya ce, da man domin ta ji kunyar na yi magana "

"Allah ya shirye ki Munnira "

Hauwa ta faÉ—a tana dariya ni kuma sai na ce" Kuma da ba haka take ba. Da ni ce mai bakin amma yanzu Munnira ta taka ni."
Na faɗa ina dariya kai tsaye ta ce" Wallahi da bakina kawai dai na ɗan yi lamɓo ne. Sai da na gama ganin takun kowa sannan na bayyana kalata."

Muka kwashe da dariya gabaÉ—aya muna nan zaune aka mai do nepa falon ya yi haske Suwaiba ke tsokanan Anty Bahijja da ba chasu ne ta ce ita ina ruwanta da chasu yanzu ma gida za ta tafi, ba ta kuma daÉ—e da maganar ba muka ga tafiyarta ta fita ba daÉ—ewa Maryama ta zo ta kunna waya da wakar Amarya ki haÉ—a kayan ki na Nura. Inuwa tana wani takawa yan gidansu na yi mata ihu

Ba zato kawai Munnira ta ce" wannan ai tsohuwar waka ce. Kuma ƙauyanci ne mu taka rawa da ita."
Kallon Munnira kawai na ke yi kallon ina ruwan ki.
"Gaskiya ba. Kuma sautin waya ai ba sauti ba ne. A nemo speaker."
Hadiza kanwarta ta amsa mata, daman duk zamu ce ta iske mu je mu.

Suka yi kamar ba su ji ba, Maryam É—in ta cigaba da rawan ta suna yi mata tafi. Ita ke fadin a je ta fito mata da Gimbiya ta zo ta yi rawa. Sai kawai ta saka wakar uwar gida ran gida har Gimbiyan ta fito lokacin ta sauya kaya ma Maryam É—in ta kamo hannunta tana bin wakar.
"Uwar gida ran gida Tafida yana yi miki rawa."
In da aka ce shaba sai ta kira sunan Yallabai

Ni da su Munnira muka kalli juna kafin mu yi dariya cikin mu ba wacce ta yi tunanin Munnira za ta mike sai ganin ta kawai mu ka yi a cikin su tana juyi tana faÉ—in" A fagen na mu ne mu Uwagidaye ne bai kamata amayar ta shigo ba."
Sadiya, Hauwa wannan fagen namu ne."
Chapter 58 · 0% Book details