← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 103

Sashe 60

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hauwa ta faɗa tana dungurar kan Ƙanwarta Ashe.
Tura baki ta yi kafin ta ce" Ni fa ban yi nadama ba. Ni Anty Munnira ma shigan sauri ta yi mini. Ni ce na so na yi ma Maryama bugun tsiya wallahi"

"Kuma bakin ki bai mutu ba ko?

Hauwa ta sake faɗa sai ta yi shuru ni kuma na ma kasa mgana hankalina ya tashi. Ba wai domin za a kira Yallaɓai ba sai domin ni ban je sunan nan da wata zuciya ba. Amma gashi abubuwa marasa daɗi sun faru Allah kaɗai ya san a yanayin da labarin nan zai fita.
Fuskata ba walwala na sauke su Hauwa a gida tana faɗa mini wai na kwantar da hankalina ko Yallaɓai ya zo zai fahimceni in na yi masa bayani kallonta kawai na yi. In har an so ya fahimcenin ba.

Mun koma gida muka iske Baby a ƙofar gida tana jiran mu ita da Salisun. Shi ya bude mini get na shiga da motata ciki.

"Umma me ya sa muka dawo! Ni ba zan je sunan Anty Gimbiyar ba ne?

Baby ta fara tare ni da mgana bayan na fito daga mota.

"Ni matsa ki ban waje kafin na gwabje ki."

Na faɗa a fusace saboda ta ba ni haushi. Marwa ce ta ja ta gefe tana yi mata mgana ni kuma na wuce cikin gida. A falon Yallaɓai na samu matsugunni ina mai da numfashi, gabaɗaya sai na tsargu kaina, wallahi ban ji daɗi ba ba kuma a son raina abin da ya faru ya faru ba. Ina zaune su Marwa suka shigo ko kallon su ban yi ba na tashi jaka da mayafi a hannu na shige ciki ina ji Yunma na kuka tana Uma na yi banza da ita.

Kwanciya na yi a kan gado kawai na rasa mafita. Tunanin maganar da zan harhaɗa na kare kaima a wajen Yallaɓai na ke yi amma da kamar wuya. Tun da a san tare nake da Munnira Allah ne kaɗai zai iya fitar da ni, na kasa haƙuri sai na ɗauki waya na kira wayar Yallaɓai bai ɗauka ba har sau uku a raina na ce shike nan wayar na hannuna sai ga kiran Suwaiba da sauri na ɗaga kiran

"Suwaiba sun kira Yallaɓan ne?

"E ya ce gashi nan a hanya zai zo. Ni dai na gaji da ba ma Gimbiya hakuri na baro gidan gani ni da Mubeena za mu samu adaidaita."

Ta amsa mini, sai na furzar da iskar bakina kafin na ce" Wallahi Suwaiba na kasa sukuni Allah ne kaÉ—ai zai fidda ni a wannan sabgar."

"Gaskiya. Domin Gimbiya sai kuka take yi shima jaririn na kuka. Ina jin hannun nan da ta bugu ta yi gocewa ko targaÉ—e. Allah kaÉ—ai ya san mganganun da za su faÉ—a masa in ya zo. Halima can na barta tana ta faÉ—in duk abin da ya faru da gayya ne ke ce kika shirya komai."

"Uhm"

Kawai na iya faÉ—a na kashe wayar. Daman ai ba ta kaunata tun marin da na yi mata na kore ta a gidana ni na san tana neman ranar É—aukan fansa a wajena sai yau ta samu dama ai sai ta yi amfani da damarta da kyau da kyau.

Ina nan zaune Yallaɓai bai kirani ba har aka fara kiran sallar mangariba. Daga Marwa har Baby ba su neme ni ba nima ban nemi kowa ba. Tiolet na faɗa na yo alwala na so na ta yar da salla. Ina cikin yin salla na ji shigowar motar Yallaɓai da ƙaran buɗe get sai da gabana ya faɗi. Ya shigo falon farko ina tahiyar ƙarshe ina jin sa yana kirana suna da karfi daga ji ran shi a ɓace ya ke.

"Sadiya"

"Sadiya"

Ban zan iya sanin ko na ƙarishe salatin Annabi ba, na sallame salla, da hijabin jikina na fito daga bedroom na buɗe kofa na fito korido shima ya buɗe ta falo ya fito sai muka haɗe.

"Na'am. Ina salla ne lokacin da ka shigo."

"Me Daughter ta yi miki da za ki kwashi mutane ku je ku dake ta ita da ƙanwarta?

Baki na buÉ—e ina kallon Yallabai yadda ya yi mini tambayar a kausaahe alamun tabbaci ma gare shi ba hasashe ba. Sai na ma kasa mgana har na buÉ—e bakina sai kuma na yi shuru kawai.

"Ba da ke nake magana ba kin yi mini shuru kamar wani É—an iska?

Ya faɗa yana mai yi mini ihu a saman kaina. Kawai sai na ɗaga ido ina mai ƙara kallonsa kafin na ce" Ni ban kwashi mutane su je su dake ta ba. Wa ya ce maka an dake ta? Ni dai na san Munnira sun yi faɗa da kanwarta ta shigo rabo ba ta sani ba ta ture ta shike nan abin da na sani. Kuma ni har ga Allah ba da yawuna Munnira ta yi abin da ta yi ba. Ni da hankalina zan kwashi mutane aje a yi tashin hankali? Me matarka ta yi mini da zafi da zan yi mata haka?

"Wa ya sanin miki. Duk abin da ya faru kina sane saboda ai su Munniran da Hauwa tare da ke suke. In kika tsawarta musu ai za su bari amma da ya ke kema akwai mugun nufi a ranki. Shi ya sa kika yi shuru sai da abu ya faru za ki zo kina faÉ—amini wai mai matata ta yi miki da zafi? Kika san abin da ta yi miki domin ni ba makaho ba ne tun haihuwan nan na ga take-taken ki, ko barka sai da na yi ta miki magana kika je, asibiti ma ba ki je kin duba ta ba sai da ta koma gida da na yi magana sai ki ce ba ki da lafiya. To duk na gama gano ki. Kin kuma kyauta da abin da kika yi. Saboda ke an targaÉ—a mini mata a banza a wofi na gode Sadiya kin ji ko? Na ce Na gode."

Ya faÉ—a cikin hargagi har yana yarfa hannu. Marwa da Baby suka fito da sauri daga dakin su Jidda suka gan mu cirko cirko ni da Yallabai.

"Ni ce mai mugun nufi a raina?. Ni Yusuf?

Na faÉ—a ina nuna kaina cikin tarim mamakinsa.

"E ke ce fa, kuma kin aiwatar da nufin ki, kin kyauta. Amma ki sani ba ita kika yi ma wannan tozarcin ba illa ni. In ma kin ji hauahi tana ta haihuwan Maza ni ba ki yi mini adalci ba. Domin na shafa faɗa miki da mazan da matan duk ɗaya ne a wajena me ya sa ba za ki yi mini kara Sadiya ki boye kishin ki ba? Abin da kika yi dai dai ne? Abin da kika yi sunan shi ne zubar da ƙima. Watarana in Saudatu ta gan ki   ba ta darajaki ba. Juzt bleme your self domin ke kika zubar da girmanki, ta bi kuma ta tattaka shi."

Wai Yallaɓai har yana nuna mini hannu yana gaggaya mini magana ina kallon shi kwarmin idanuwana suna cika da kwallah.

"Na É—auka in ina da wani mugun nufi tun a shekaran baya zaka sani ba yanzu ba."

"Da ba ki da shi. Yanzu kika ɓullo da sabbin hallaya marasa kyau. Kin bari sheɗan na zugaki. Tare da su waɗanda kika rike a naki. Na daɗe da sanin saboda ke su Hauwa ba sa zumumci da Daughter amma ban taɓa magana ba. Kuma a adalci ai dake da ita duk ɗaya ne yadda za su yi miki haka za su yi mata. Duk na share wannan ban taba magana ba sai abu ya zo har da duka har gidan ta? To ba ki isa ba yadda kema ban kyaleki ba suma ba zan ƙyale su ba na kira Nasir da Mutaƙƙa kowannen su zai ja ma matarsa kunne. In dai ba za su dauke ki ɗaya da Matata ba to sai dai a raba wannan alaqar taku gabaɗaya tun da ba ta alheri ba ce sai ta sharri."

Ai ban san na kwashe da dariya ba, sai da na ga na yi ta cikin takaici da bakin ciki hawayen da suka zubo mini na share ina kallon Yallaɓai ido cikin ido kafin na ce"Wannan kuma wallahi ta yi kaɗan. Lokacin da tazo tare ta ganmu kuma wallahi tare za ta bar mu. Zama daram in ji mai naguda."

Na faɗa ina mai riƙe kuguna. Domin na lura an gama shiryaa mai mganganu ni zai zo ya tara mini gajiya to wallahi bai isa ba.

"Ni kike faÉ—a ma haka Sadiya?

"An faÉ—a maka sai me? Kai waye? Mijina!
Na yi wata bazawar dariya kafin na nuna shi ina faɗin" Mijina ne kai da muka yi zaman aure na shekari sama da ashirin ashe kai ba za ka iya sanin abin da zan iyawa aikatawa da wanda ba zan iya aikatawa ba? Wato duk abin da matarka da danginta suka faɗa akaina shi ne gaskiya a wajenka ko? To bari ka ji na faɗa maka ko na ce na ƙara tunasar dakai ko garke Gimbiya za ta haifa maka na Maza wallahi ko a gefen gyalena da yau ban haihu ba da bakin ciki ya kashe ni. Maganar zuwa barka ban yi niyya zuwa ba ne, duk ita a nata haihuwan ka fahimci ni ban je ba amma a lokacin da na haifi Yunma ba ka fahimci sai da ta ga dama ta zo ba? Ita ka same ta ka yi mata mgana kamar yadda ka yi mini? Wato sai ni ce marainiyar ka dole ka zo ka same ni ka sauke mini magana. To bari ka ji na rantse da wanda raina ke hanun shi ina dai dai dakai daga kai har munafukar matar taka."

"Sadiya."

"Yusuf"

Yadda ya kira sunana cikin tsawa nima haka na buÉ—e murya na kira sunan shi yana huci ina huci.
Sai kukan Yumna muka ji, can sai na Baby ko ni juyawa ban yi ba shine ya juya yana kallon su yara sun ga abin da ba su taba gani ba.

"Marwa ki ja yaran nan ku koma ciiki."

Ya faÉ—a yana sassauta muryan shi,
Chapter 60 · 0% Book details