Sashe 82
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ai ina jin haka da gudu na fice ina jin sa yana ƙayƙyatan dariya.
Sai da na daidaita kaina har É—aurina ya kwance sai da na sake yin wani sannan na fita can falo, na iske Rabi'atu da su Baby, ta saka dogon hijabin ta har kasa sannan ba ta yi kwalliya ba amma da ka ganta fuskar nan ta yi fresh alamun dai ana shan amarci.
Gimbiya ko na gefe ta kame a kan kujera mai zaman mutum É—aya an ci gayu da mayafi a saman kafaÉ—a, Ammar na hannunta Amwar na gefenta Khalipa ne kawai tare da su Baby.
Rabi'atu na ganina ta fara gaisheni cikin girmamawa na amsa ina tambayanta baƙunta ta sunkunyar da kai. Gimbiya ko ni da gidana ni ce na fara gaisheta ta amsa kamar ba ta so. Ban damu ba Yallaɓai na fitowa na ce na haɗa mana dinner mu fara da cin abinci.
A gaban su ya É—an rumgumo gefen kafaÉ—ata ya sumbaceni kafin ya ce" Allah ya yi ma matata Sadiya albarlka"
Na amsa da Amin Rabi'atu ta yi gaba ita da su Yumna Gimbiya ce a wajen amma ba ta amsa ba ina ganin ma tana hararan mu ko shi ne ya ja mini ban sani ba.
Dukkanmu har da yaran muka zauma a dining muka ci abincin. Gimbiya kunin aya kawai ta sha ta tashi ta koma saman kujeran falon ta ce ita dai ta ƙoshi. Ni da Yallaɓai ne a wajen ke ta hira sai ni in na sako Rabi'a ciki ta ɗan yi mirmishi kuma ta ci abincin sosai ta sha kunin aya. Da ma ina cewa ta ci mana ta daina baƙunta nan ma ai gida ne.
"Za ta ci fa, a can gida in kika aiko mana da abinci ta riƙa santin cewa gaskiya Umma ta iya girki "
Ya faÉ—a yana kwaikwayonta ni da shi muna ta dariya ita ko ta sunne kai, ina son ta tana da kunya sosai. Anan ne na ke masa taÉ—in ashe ya kai ta wajen Alhaji.
"To ni da babana kuma? Ko sai na tambayi izini."
Ina dariya na ce ba ruwana, mun tattauna mganar makaranta ya ce ai itama Rabi'atu cikin satin za ta shiga cikin makaranra ta yi risgtration suma sun koma sai ina zolayansa na ce shi zai kai ta?
"A'a sati É—aya ban je aiki ba gobe zan koma office. Amma ina tunanin na haÉ—a ta da Musbabu ko Adnan"
Ni ko na ce sai dai Adnan din Musbahu ma ayyuka sun yi masa yawa ita ko tana gefe ta ce ai za ta iya fa ita kaÉ—ai, sai ya ce bari dai ya gani in ba buJata sai ya haÉ—ata da direba. Baby ta yi zencen nata makarantan ya ce gobe zai shiga makaranta ta zama cikin shiri za ta fara SS1.
Ni ko na ce ga Yumna a saka mini ita a Ajin yara.
"Mugunta ko? Wannan jarriyar ne zan kai makaranta to ni ba da ni za a yi haka ba "
Ina dariya wai Yumna ce jaririya ina roƙon Yallabai ya kai ta bakinta ya buɗe da karatu ya ce sai ta kai shekara huɗu zai saka ta a makaranta wai Baby ta riƙa koya mata a gida tun da na ga ya dage na yi shuru na san ba zai amince ba.
Muna gama cin abincin na saka Baby ta gyara wajen sannan Yallaɓai ya ce duty ɗin ta ta tattara yara su koma can falon su a zauna lafiya ban da hayaniya har Ammar sai ta karɓe shi hannun Gimbiya ta tafi da shi can falon su, saboda ya ce kar a yi hayaniya shi ya sa suka yi shuru kamar ba su a gidan.
Farko Yallaɓai ya buɗe taro da addu'a sannan ya yi nasihohin shi, da tunasarwan cewa dukkanmu ya aure mu ne domin yana son mu ne, Gimbiya da ya aurota ni ban gaza ba haka itama Rabi'atun ya faɗa mata Gimbiya ba ta gaza ba. Duka matsayin mu ɗaya mu yi haƙuri mu zauna lafiya mu rike juna da Amana. Ya ce ni ce Babba ya san ina ƙokari to don Allah na ƙara Rabi'atu ƙarama ce a cikin mu, mu zauna da ita bisa gaskiya da Amana.
Ya ba mu damar magana ni dai na ce in sha Allahu ba matsala daga bangarena Gimbiyar ma ta ce haka itama Rabi'antun ta ce haka sannan ya yi mata gargaɗin ko ba aure ba a shekaru mun girme mata ta yi mana biyayya in ya ji saɓanin haka zai saɓa mata ta ce hakan ba zai faru ba.
"To na ji daɗin haka. Maganar rabon kwana mu bar shi 2dys ɗin ne ko ya ya?
 Sai na ce a bar shi a haka ɗin ai ya yi.
Amma sai Gimbiya ta ce ba ta yarda ba sai dai a ma yar da shi kwana É—aya.
"Miye wani kwana É—aya,? Da ba biyun kuke yi ke da Sadiya ba?
"Da ka ce yanzu ko mun ƙaru gwara ɗayan saboda kar a cuci kowa."
Gimbiya ta faÉ—a cikin gatsali, zai fara faÉ—a na dakatar da shi da cewa" Ba komai a yi kwana É—ayan ai duk É—aya ne."
Bai haƙura ba yana so ya dai yi magana na ce"Ka yi haƙuri a bar shi a haka don Allah"
Jin haka yasa sai ya yi shuru. Zaman dai haka ya shi ba wani kwarjini, shi da ya kawo su shi ya ɗauke su ya ma yar da su yafi awa da tafiya sannan ya dawo ni kuma ban tuhume shi a in da ya tsaya ba da kan shi yake faɗa mini Rabi'atu ke kuka wai tsoro ba za ta iya kwana ita kaɗai ba, shine ya tsaya yana lallashinta da nuna mata ga Gimbiya a gidan kar ta ji tsoro.
"Allah sarki. E kafin ta saba ko a gida ta É—auko yarinyar da za ta É—an rika taya ta kwana in baka gidan."
"E mun yi wannan mganar to can gidan baffan nata ba yara fa, ni da man Baby na ce ta riƙa zuwa tana taya ta kwana kafin ta saba."
Na ma kasa mgana ni shike nan ya'yana Yallaɓai yana raba su tsakanin matansa ba tare da izinina ba kala ban ce masa ba.
Mu ka yi shirin kwanciya amma bai bar mu mun kwanta ba sai da ya yi ɓarnan ruwa har yana yi mini sambatun ya yi kewar gidan ruwan shi a raina na ce ka ji da shi dai da asuba ma ya koma ruwa. Da safe kuma tun safe ya yi shiri ya tafi office da yamma da ya dawo ya biyo ta nan gidan ya ɗauki wasu kaya sannan ya wuce can gidan yana ƙara jadadda mini na fara shirin tariya, a nan ne ma ya ke faɗa mini gidan da Gimbiya ta tashi Kawu ya bashi shawaran ya saka yan haya, ni dai na ce kar ya saka yan haya a gidana don Allah.
"To a bar miki za ki rika zuwa partime kenan?
Na ce masa e, saboda ina son gidan ya fita yana dariya wai duk abuna sai na tashi na koma sabon gida na samu cigaba ni ina noƙewa bai san yadda na ke son gidan nan ba ne ne har raina ni kaɗai ce fa anan can ko da gayyar kishiyoyi. Ganin ya matsa ya sa dole na fara shiri Baby dai ta koma makaranta an zama manya yanzu, ni dai labulayan na samu na siya sai cafet na falo biyu sauran kuma na tattara aka kai wanki na ce na yi amfani da su. Yallaɓai na yi ma maganar falo guda ɗaya ba kujeru ban saka rai ba ya ce na yi magana nawa za a yi saffa saffa gado da kujeru da gudu na je na tambayo, can ɗan kusa da gidanmu na Dorayi ne kafinta ya ce 800k na zo na faɗa masa ya ce a yi mini ganin na samu sauƙi na ce a yi mini ƙaramin gado da wardrope na ɗayan bedroom ɗin sauran kuma kaya na kuma da su zan koma, na so tariyan ya zama bayan biki ko da wata ɗaya ne amma bai samu ba sai da ya kai wajen bayan biki da wajen wata biyu sannan saboda an ƙarisa aiki a shashena. Allah ya taimake ni bangarena na haɗe da bangaeen Yallabai ne. Na Rabi'atu ne da Gimbiya suke a haɗe.
Ranar wata asabar ce na tare a sabon gida. Da man tun satin mota ta zo ta kwashe kayana zuwa can gidan y'an uwana suka taya ni muka gyara komai. Ban yi gayya ba daga ni sai su Munnira sai y'an gidanmu sai Marwa da ta zo, sai dangin Yallaɓai, mun dai yi girki saboda ma su zuwa. Bangarena babban bangarene kamar gidana sai dai nan na samu ƙaruwan falo da ɗakuna amma duk samfur ɗaya ne. Dining na so na yi sabo rashin kuɗi ya sa na dawo da tsoho. Amma zencen gaskiya gidan ya yi kyau Yallaɓai ya kashe kuɗi sosai masha Allah. Gimbiya tun da ta leko sau ɗaya ban ƙara ganin ta ba Rabi'atu kuma tana zuwa makaranta amma in dai ta dawo ta nan tare da mu da ita duk muka gyara ɗakuna na.