Sashe 41
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kawai ta ce ba ta ƙara magana ba, ni ko ina zaune kamar zan yi magana sai na kwaɓi kaina. Yara ma ba sa jin abin da muke tattaunawa suna ta wasannin su. Gwara ma Jidda amma ita hankalinta na kan Tab ɗin da ke hannunta. Na yi na yi da Yallaɓai ya siya mata waya ya ce sai ta shiga Jami'a. Tab ɗin daman shi saboda karatu ya siya mata. Ko rigister ɗin jam da sim ɗin Yallaɓai ta yi amfani wani lokacin yana da tsauri wani lokacin kuma yana da sauƙin kai.
Har muka isa ma'aikata ba ta ƙara magana ba sai ma amsa wayarta da ta riƙa yi lokaci bayan lokaci.
Ƙwarai waje ya yi kyau fiye da labari da gani a hoto. Kafin shiga ma'aikatan akwai babban get in da masu gadi ke tsaro har mutum biyu saboda sace sacen kayan aiki. Sannan daga gefe an makala wani allo da aka yi ma rubutu kamar na zaiba mai ɗauke da sunan ma'aikatan HM TAFIDA AND SON'S LIMITED"
Ma'aikatan na nan a kan titiN zaria road gaba kaɗan da in da office ɗin su yake na yanzu. Kuma wajen babba ne akwai fili a haraba da zai ci kimanin motoci sama da goma. Sannan an yi shuke-shuke daman Yallaɓai na son shuke-shuke. Ko'ina sai da Yallaɓai ya zagaya damu an gama komai fenti ne ma ake ƙarisawa a wani wajen. Office ɗin Yallaɓai babban yana benen sama ne amma tun da ba yanzu za su fara amfani da can ɗin ba sai ya samu wani a ƙasa da aka saka masa suna da zane kamar na zaiba wato Managin Director Md. Har office ɗin Musbahu na gani shima makeke na ce tabbas ya cancanta har sama mun haura shi dai ba a ƙarisa ba amma ma'aikata suna kan aiki. Akwai ɗakin hutawa da sauran su ba abin da dai ma'aikatan ba ta mallaka ba sai godiya.
Ina kallon Yallaɓai ina tuna a farkon auren mu in ya ce mini shi ba ya son aiki a ƙarƙashin wani ya fi son aiki na ƙashin kanshi. In ya ce mini ya na son gina kamfanin shi na zane zane da abin da ya shafi kwangilan gine-gine a shaci faɗi nake ɗaukan duka mganganunsa. Ban taɓa tunanin bayan shekaru ashirin Yallaɓai zai cimma burin sa ba. Sai ga shi ya cimma burin sa da nasara tabbas ya yi aiki taƙuri sannan ya jajirce wahala da rashin kuɗi bai sa ya nuna gazawarsa ba. A gaban yara a gaban Gimbiya na rumgume shi sannan na bashi sumbata a gefen kumatun shi, ina mai faɗin.
"Congratulation Yallaɓaina. Im so proud of you."
Na faɗa ina yi masa wani irin ƙayattacen mirmishi.
Sai ya sake riƙo ni gefen kafaɗansa na dama yana mai kallona ya ce.
" Amin. Nima ina alfari dake Sadiya ta. Duk matakin da wannan kamfanin zai kai ke ce a gaba. Kin ba ni dukkan gudummuwar da macen ƙwarai ke ba ma mijinta. Thank you so much haƙika da ban haɗu da ke a shekaru ashirin a baya ba da na tafka babban asara rasa mace kamar ki."
Sai na ji wani farin ciki ya lulluɓe ni har ina ƙara narkewa a jikin shi, Jidda na gefe sai ji muka yi ƙyars ta yi mana hoto. Baby da su Khalipa ba su san ma me ake yi ba suna can suna wasa.
"Jidda Allah ya sa hoton ya yi kyau."
Na faɗa ina dariya. Yallaɓai ko sai faɗin yake yi ta ƙara yi mana wani.
"Kun yi kyau sosai Umma da Abba."
"Mun gode yar albarka ta wajen Abban ta"
Yallaɓai ya faɗa har yana ɗaga mata babban yatsan shi alamun jinjina.
Jidda na ta ɗaukan mu hoto kwata kwata na sha'afa da Gimbiya sai da ta yi tsaki na ji sannan na juya muka haɗa ido, wallahi na gan ta harara ta, ta yi sannan ta yi motsi da bakinta ta ɓata rai, duk da na ga abin da ta yi mini ban riƙe shi a wani abu ba sai na juya ina kallon Yallaɓai kafin na ce
"Mun manta da Amarya. Kira ta a yi mana hoton tare mana."
Saboda ba lallai in ni na yi mata magana ta saurare ni ba. Wataƙila za ta iya ganin hakan a matsayin cin fuska.
"Haka ne. Daughter taho mu yo hoto in an gama sai mu yi da yaran gabaÉ—aya."
Amma sai ta yi kamar ba ta ji ba, sai ma ta juya yana kiran ta ta yi banza dashi ta fita daga office É—in na shi, da muke ciki Jidda na É—aukan mu hoto.
"Ka je ka yo lallashi Yallaɓai."
Na faɗa ina kallon sa. Ni kaina yaƙe nake yi amma a ƙasan zuciyata ina jin wani abu kamar kishi na motsa mini.
"Me a ka yi mata? Ƙyaleta."
Ya faɗa ne kawai amma sai na ga hankalinshi ya tafi a kallon ƙofa ko za ta dawo sai na ƙara roƙon sa da ya je ya ba ta hakuri ta zo a yi musu hoton.
"Ƙyale ta kawai."
Jin abin da ya sake faɗa ya sa sai na kama kaina ban ƙara yi masa magana ba. Ina lura dashi saboda fushin da ta yi ya sa sama sama muka yi hotuna da sauran yaran sai ya ce a bar shi haka ya na so mu je filin can mu gani ya mai da mu gida yana da wajen zuwa. Ko da muka fito tana cikin mota kila da ace da motarta ta zo sai dai su haɗu a gida. Ya yi sallama da masu gadin sannan muka tafi a cikin motan ma Khalipa sai da ya sha mari wai ya ta ka mata kafa.
"Kawai saboda ya taka ki sai ki yi masa irin wannan marin haka?
Yallabai ya faÉ—a cikin mamaki, ni kaina ban yi maagana ba ne amma marin da ta yi masa ya yi tsauri a bi sa dai laifin da ya yi.
Yaron sai ya fashe da kuka Baby ce ke lallashin sa.
"Sorry. Khalipa sorry."
Amma sai ƙara ɓare ma mutane baki yake yi, ni dai na sake tallafan Yumna dake hannuna da ta yi barci faɗan da ba ruwanka daɗin kallo ne dashi.
"Kar ki sake yi masa irin wannan marin."
"Ya yi laifi kar a hukunta shi?
Ta faÉ—a a zafafe ni a tunanina ko dai daman suna faÉ—a ne kafin su fito? Domin na ga a zafafe take kamar za ta kai duka.
"Ni dai na faÉ—a miki kar ki sake. Ba a hana ki yi masa hukunci ba amma ba mari irin haka ba."
"Na ji."
Ta ce a ƙasa ƙasa, shima sai na ga ya yi wani ƙyaci na ɓacin rai a raina na ce can ta matse muku. Tafe tafe sai ga mu a anguwar Alu veneu in da Yallaɓai ya siya wawaken fili. Mun sauka daga mota dukkan mu muka shiga filin babba ne Yallaɓai ke nuna mana yadda fasalin ginin zai kama. Ya tabbatar mana da kan shi zai yi zanen gidan shi, ya yi masa irin fasalin da ya ke so a cewarsa yanzu ginin ne a gaban shi bayan taron lunching na buɗe kamfanin shi za a fara yin katanga a saka get sai kuma a fara gini.
"Flat huÉ—u zan yi a cikin filin nan in sha Allahu."
"Kuma duk a gida É—aya nufina a haÉ—e?
Na faÉ—a ina kallon filin, babba ne amma flat huÉ—u na su waye?
"E mana. Naki ɗaya na Daughter ɗaya. Ɗaya nawa ɗayan kuma ko saboda baƙi."
Ina shirin sake magana Gimbiya ta yi zaraf ta ce.
" Me ye amfanin yin shashen baƙi tun da ga shashen ka? Infact ma mu kan mu na san akwai spare room a bangarorin mu."
Sai na zama ƴar kallo, domin kai tsaye Yallaɓai ya ce" Duk da haka flat huɗu zan yi."
"Babu amfanin yin haka."
Ta bashi amsa sai ya share ta bai yi magana ba.
Ni kuma da ƙarin bayani sai na ce" Yana da amfani ko saboda su Khalipa in sun tasa zai musu amfani.
"To kin ji ma."
Ya faɗa cike da ƙarfin gwiwa. Amma ita duk ba ta gamsu ba na san fargabanta kar Yallaɓai ya ce zai ƙara aure amma saboda na ƙara samun tabbacin sai na tsaƙalo maganar.
"Yallaɓai ko dai shashen ɗin Amarya ne."
Yadda ta yi saurin kallona da razana a yanayin ta shi bai yi haka ba sai ma dariya da ya yi kafin ya ce" Wannan kuma lamari ne na Ubangiji. In ya kaddaro mini zan gode masa."
"Yallaɓai dai zai yi ginin mata huɗu ne. Wata ƙila shashen naka ma in ka ji ra'ayin aure zai tashi a naka ya koma nata."
Ni na faÉ—a amma yana ta dariyan nishaÉ—i.
"Ke ko?
Ya faÉ—a ya na nuna ni da hannu. Nima dariyan nake yi ina faÉ—in" To ai gaskiya ne."
Gimbiya na tsaye amma ta kasa magana sai dai ina kallonta ta gefen ido ta ƙara kumbura. Har tana wani kifta idanuwana kamar na yi dariya sai na kanne. Yaran suna can gefe Khalipa da Baby suna ta wasan ƙasa Jidda na tsawarta musu har da Anwar da shima yana tafiyan shi ko'ina.
Ban É—auka za ta yi magana ba tun da har muka baro wajen muka shiga mota. Muna hanya zai fara sauke mu gida Gimbiya ta kira sunana daga bayan mota.
"Madam"
Da man haka take kira na ko ta ce Maman jidda.
"Na'am"
Na amsa mata ina ɗan waiwayawa bayan in da take zaune ita da yara.
"Kina ta wani dariya yana faɗa miki in aure na cikin kaddaransa zai ƙara."
Sai na saki dariyan nishaÉ—i kafin na ce" To kuka kike so na yi?
"Amma bai kamata ki yi masa dariya ba."
"Ikon Allah."
Ni da shi muka haÉ—a baki wajen faÉ—a.
"Ka gama aure Daddy. Ni da Madam mun ishe ka in sha Allahu."
"Gaskiya ne."
Na biye mata ina Æ´ar dariya.
"Ba ku isa ba. Ku ji minI ƙarfin hali ni na ce kun ishe ni ne?
"Ko ba ka ce ba mu mun ce ko Madam?
Ta faÉ—a tana sako ni a ciki.