Sashe 5
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Nufina yanzu duk in da za ki je Ya Sadiya wani ƙarin tonon asiri ne. Abin da ba ki taɓa yi ba kar ma ki fara. Har gwara ma ki koma gida wajen Gwaggo da ki je Yashe can fa ƙauye ne in wani ya yi shuru wallahi wani ba zai yi shuru ba. Gwara ki koma gidan ki amma shi ma Yallaɓai ki gasa mai aya a hannu yadda zai fahimci shayi ruwa ne madara ake saka masa ya yi kauri."
Ta gama faɗa ta na kallona ganin na ƙi mgana kuma na ƙi sakin fuska sai ta marairaice ta na sake faɗin" Ko ba haka ba? Ki duba magana ta da idon basira Ya Sadiya."
Yadda ta ce idon basira ne ya sa sai da na yi dariya, itama sai ta hau dariyan Kafin na jinjina kai ina fadin" Haka ne kin yi gaskiya."
"Yauwa Ya Sadiya ki koma ko saboda su Jidda."
Sai na jinjina kai a karo na biyu kafin na ce" To shi ke nan zan koma Amina."
Sai ta murmusa kafin ta rumgumoni tana faÉ—in" Ko ke fa My Ya Sadiya."
Mirmishi kawai na yi ba tare da na yi mgana ba. Duk in da ɗan uwa ya ke daɗi gare shi ni kaina sai na ji kamar kar na tafi, sai dai kuma gaskiya ta faɗa minj duk in da zan je yanzu kamar na soka wuƙa a cinyata ne na yi kururuwa na yi kirari gwara na koma amma ni da Yallabai zaman yan marina za mu yi tsakanin ni da shi.
Falo na kuma wajen yara Amina na kitchen ta na girkin Yamma. Yasir ne da Sumayya a gidan Afra ta tafi islamiya daga baya barin su na yi a falon na shiga kitchen wajen Amina ina ta ya ta aiki jefi jefi muna hira har muka gangaro kan mganar Ma'u.
"Wai Ma'u shuru kamar ba ta nan"
"Ta na nan, ai tun da aka yi wannan turken ni da ita sai ta shafa mini lafiya."
Amina ta ƙyalƙyace da dariya ta na faɗin" Ni kaina sai mu daɗe ba mu yi waya ba, ko a group na gida ta daina mgana kamar baya."
"Ni kaina na ga ta yi sanyi kamar ba ita ba."
Na faÉ—a ina yanka albasa.
"Rabon da mu yi waya tun lokacin da ta kirani ta na faɗa mini auren shema'u na ce mata ba zan samu zuwa ba."
"Ni dai bayan nan mun É—an hadu a É—orayi "
Na ba ma Amina amsa, an yi bikin Shema'u ko wata biyar ba a yi ba ta yi aure a gombe. Wani tsohon chairman ta aura matansa huÉ—u É—aya ce ta rasu ya cike da ita dukkan mu mun je bikin amma ba mu je can Gombe ba Ma'un ce ta je su Shema an gama yawon duniya an gaji dai an yi aure can kwanaki da na je gida Gwaggo ke faÉ—a mini ta zo ganin gida har ta shigo gaishe su har ta ba ma Alhaji dubu biyar a raina na ce su shema an samu duniya kenan.
Mun cigaba da hiran Ma'u ni da Amina har muka gangaro kan Anty Bahijja nan na ke ba ta labarin irin sunayen da suke kiran Gimbiya da cewa ita ce mai ƙashin arziƙi.
"Allah na tuba Amina ai ni da arziƙina Yusuf ya aure ni. In ma tsiyar ne sai dai in shi ne ya goga mini"
Me Amina za ta yi in ba dariya ba har ta na rike ciki na kusa buga mata ƙasan wuƙan hannuna ina faɗin" Ban son iskanci fa Amina"
"To ke ce Ya Sadiya da wata magana."
"Allah kuwa. To har ni za a yi ma gorin ƙashin arziƙi."
Ni da ita muna ta dariya cikin annushuwa da hira muka gama girkin nan ana ta kiran sallar mangariba ni da ita muka je muka yi salla, Afra ta dawo ta isko ni daki tana mini hira akwai surutu kamar Baby ce daman kuma tsaran juna ne.
Bayan sallar isha'i muna falo muna cin abinci Yallaɓai na ta kiran wayata bai haƙura ba.
"Ya Sadiya ki É—auka ki faÉ—a masa gobe za ki dawo"
"Wallahi ba zan É—auka ba."
Na faɗa ina hararanta sai ta sunne kai tana yar dariya. Kira uku ya yi mini bayan na ɗazu da na shiga sallar asuba na ga huɗu, ni kuma na ce wallahi ba zan taɓa daga kiran shi ba sai yau? Sai yau ne ya tuna da ni matarsa ce? Sai yau? Ai ya makara wataƙila da ya kira kafin yau ɗin da wata ƙila na saurare shi.
Mun gama cin abinci mun dawo falo Amina ta kunna mana kallo ni ba na ma kallon hankalina na wajen Afra ina koya mata aikin makarantan da a ka ba su a english Yasir da sumyyah na ta wasannin su a tsakiyar falon
Na ji ana kiran wayar Amina amma ban dai bi ta kai ba sai da na ji tana faÉ—in" Ya Hamza ke kirana."
Ban kawo komai a raina ba na ce" To ki É—aga mana."
Na ji ta É—auka da sallama suna gaisawa daga nan sai na ji tana faÉ—in" Ya Sadiya wai? E ga ta nan ina ga wayar tana É—aki ne shi ya sa ba ta ga kiran ba."
Sai na dawo da hankalina kanta har ina miƙewa. A ina Ya Hamza ya san ina gidan Amina.?
"Ga Ya Sadiyar"
Na ji Amina ta faɗa lokaci ɗaya ta na ta isowa in da nake ta miƙa mini wayar na karɓa ina mata inkiya da ido a ina ya san inan nan? Sai ta rika min nuni na yi mgana Ya Hamza na jin mu.
"Salamu Alaikum Ya Hamza."
"Sadiya kina lafiya?
Ya faÉ—a daga bangarensa.
"Lafiya lau. Ya su Anty Khaleesat da yara?
"Duk suna nan lafiya."
Shuru na wani lokaci na kasa mgana amma gaba na ya faɗi ina tunanin a ina ya san ba na gida ina kaduna ko dai Yallaɓai ne ya kai masa ƙarana?
Dam! Na ji ƙirjina ya amsa ban samu sararin mgana ba na ji Ya Hamza na faɗin
"Ashe kina kaduna?
Ina shirin na amsa masa sai kawai ya cigaba da faÉ—in.
"Ke haka ake yi ehe da ga zuwa ziyara sai ki shantake a gidan ƙanwarki sama da kwana goma ba ki da ranar ƙomawa gidan mijin ki?
Mamaki ma ya hana ni mgana. Mamakin Yallaɓai da zai tashi wasa da ni.
"Dama daman gobe nake shirin komawa."
"To ya dai kamata. Shi ya kirani yanzu yana faÉ—a mini ba ki a gida sama da sati ya na ta kuma kiran wayarki ba ki É—auka ba."
"Wayar ta na silent ne ban ji kiran na shi ba."
Na samu kaina da furtawa.
"To sai ki kira shi yanzu ku yi magana. Sannan gobe ki koma gidan ki Sadiya. Shi kan shi Dr sai ya ga rashin hankalin mu gandan gandan dake, ke ba suna kika zo ba sannan ba biki ba daga kun ɗan samu matsala da miji sai ki kama hanya ki tafi gidan ƙanwarki? In ma yajin za ki yi kuma tun da ba ki je ɗorayi ba me ya hana ba ki taho gidana ko gidan Auwal ba?
"Ka yi haƙuri Ya Hamza."
"Ba maganar haƙuri ba ne. Ba a haka kin ji ko? Amina ƙanwarki ce bai kamata ki je gidan ta in wani abu ya faru ba. Mu ya kamata ki fara nema."
"To Ya Hamza."
Na furta ina ƙokarin mai da ƙwalla da suka cika mini ƙwarmin idanuwana.
"Ki yi haƙuri ki koma giden ki ki rumgumi mijin ki da ƴaƴanki. Ya faɗa mini da kan shi ranshi ne ya ɓaci ya ɗan faɗa miki wasu mganganu ma su zafi sai kika ji haushi kika ce za ki taho kaduna. Ya ce ya bar ki taho ne saboda ke da shi ku samu zukatan ku su huta sai kuma ya ga kin shantake kin ƙi dawowa yana ta kiran wayarki kuma ba ki ɗauka ba."
Shuru na yi domin kalaman bakina sun gama ƙarewa. Yallaɓai ya shirya wasan ƙwaikwayon shi ya nemi yan wasa kuma har an yi wasa an tashi karshe dai shi ke da nasara akaina bayan tarin tozarcin da ya yi mini
"Ki yi haƙuri kin ji ko? Haba Sadiya da girman ki ai yaji bai kamace ki ba, ki yi hakuri ki koma gidan ki, ke yanzu uwa ce sai dai ma ki yi ma wasu faɗa."
"To Ya Hamza in sha Allahu gobe da safe zan koma."
"Yauwa. To mu kwana lafiya amma ki kira shi yanzu."
Da haka muka yi sallama da shi muna gama wayar Amina ta zauna gefena tana faÉ—in" Wai me Babansu Jidda ya kira Ya Hamza ya faÉ—a ma sa? Na ji ya na miki faÉ—a ne?
Sai na kalleta, lokaci ɗaya hawayen da na ke ta riƙewa suka kece mini amma sai na yi saurin saka hannu na goge hawayen ina faɗin.
"Ya kira shi ya faɗa mai mun ɗan samu sabani ranshi ya ɓaci ya ɗan faɗa mini mganganu ni kuma sai na ji haushi na ce zan taho Kaduna a cewarsa ya bar ni na taho saboda ni da shi mu samu zuciyarmu ta yi sanyi amma sai ya ga na daɗe ban dawo ba kuma yana ta kirana a waya ban ɗauka ba"
"Lalle ne ma. "
Amina ta faɗa ta na riƙe haba kafin ta cigaba da faɗin" Yallaɓan nan na ki ya Saduiya sai ke"
Ta faÉ—a tana dariya na kalleta amma ban yi mgana ba.