Sashe 49
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Barcin da na yi duk sai ya sakar mini kasala shi ya sa ko girki ban yi ba. Gidan ma ko sharan shi ban yi ba, yini na yi kwanciya sai danna waya sai da Yumna ta tashi ne na haƙura ma da kwanciyar da suka dawo daga makaranta sauran dankali suka sha tare da Tea, Jidda kuma na ce ta ɗora mana girki har da ni da Babansu tun da yau ba zan iya yin wani girki ba. Shinkafa da miya ta yi sai na kira Musbabu na ce in ba damuwa ina son kayan lambu, sai ya ce mini ba sa nan sun fita shi da Yallaɓai sai na ce to ya bar shi kawai daga karshe Adnan na kira shi ya siyo mana su kabeji da cocumber sai da ya kawo na bashi kudin nan ma ya yi isha'i ya ci abincin yana ta santin har yana ba ma Jidda Tuƙwaicin dubu biyar na girkin da ta yi. Bai jira dawowar Yallaɓai ba ya ta fi saboda Yallabai sai after 10 ya dawo a gajiye ya ce mini na haɗa masa kayan tafiya kala uku Jigawa zai je gobe kuma akwai yuyuwar ya yi kwana uku a can.
Tafiyar Yallaɓai ya sa su Khalipa ba su koma gidan su ba, ni kuma ban ji na duba ta ba na dai kira ta a waya na yi mata sannu ta ce mini ai ta ma samu lafiya, har tana ce mini ya su Khalipa an kawo mini hayaniya na ce ai ba komai. Yallaɓai sai da ya yi kwana shidda sannan ya dawo. Washe gari kuma ko hutawa bai yi ba ya wuce Kaduna daga can ya je Abuja kwangiloli ne yake samu ga su nan akai akai shi ya sa yanzu ba ya samun zama dalilin haka ne ya sa su Khalipa suka share wajen sati uku a gidana ba su koma ba sai a satin da suke da uku ne Yallaɓai ya samu zama a weekend ranar kuma sai ya faɗo yana gidana ne.
Safiyar lahadi, ranar Yallabai zai koma gidan Gimbiya kuma ya ce a shirya kayan su Khalipa za su koma gida tun da Gimbiyar ta samu lafiya. Wankin kayan su daman mai wanki na haÉ—a mawa sai na kira shi na ce ya kawo sauran kananun kuma tare da Uniform na saka Jidda ta É—an wanke musu, ni da Baby kuma muka gyara gidan bayan mun gama na ce ta gyara Kitchen ta yi mini wanke-wanke sai Baby ta fara tura baki tana cewa ita kanta ke ciwo.
"Ai ko kan naki zai cire ne sai kin gyara mini Kitchen kin kuma yi mini wanke-wanke yarinya."
Na faɗa ina zare mata ido. Ta san halina tana yi mini wata magana za ta ji dundu shi ya sa bakin ta alaikun ta wuce, Jidda ke yi to yau tana wanki in ta gama ma za ta yi mu su Khalipa wanka. Yumna na goye a baya tun da na yi mata wanka take barci. Yallaɓai na ciki yana ta barci tun bayan da ya dawo sallar asuba ya koma bai tashi ba har muka karya sai ban tashe su ba sanin ya fi sati biyu bai samu lokaci ya huta ba bawan Allah ya na ta fadi tashi duk an kan mu, jiya ma Gwammaja muka yini ni da yara sai dare muka dawo da yake Nene ta ɗan yi zazzabi kwana biyu.
Baby na tura baki da komai ta gama aikin da na saka ta ban bari ta zauna ba na ce ta ɗora musu abinci Jidda tana gama ayyukata ta saka hijabi ƙawayenta sun biyo mata sun tafi tahfez suna ta mura'ju'a domin an kusa yin musu walimar saukar su, jarabawa kuma sauran ta paper ɗaya su gama shi ya sa nake ta tunanin tun da abin ya zo a tare zan ɗan jinkirta na haɗe graduation ɗin ta tare da Walimar saukar su gabaɗaya.
Yallaɓai sai biyu saura ya tashi, ya yi salla sannan ya sha tea ya hau kuma aiki a cikin laptop ɗin sa na wani lokaci ni kuma a lokacin na gaji sai kawai na kwanta Yunma ma a wajensa na bar ta, na daɗe ina barci sai bayan la'sar na tashi shima ɗin hayaniyan yaran ne ya tashe ni, na duba agogon wayata hudu da rabi har ta gota sai ban fita ba, na shiga Tiolet na ɗauro alwala na zo na yi salla sannan na fita falo. Abin da na gani ne ya sa ban san na riƙe kugu daga korido na ƙame ina kallon ikon Allah ba.
An yi mini kaca kaca da falo ba ma wannan ne abin mamakin ba. Illa Yallaɓai da na gani daga shi sai bakin wando sai singlet haka su Khalipa ba riguna sai kananun wanduna har da Baby itama ta ci zanzaro da kayan tekwando ɗin su na makaranta suna wasan doke ni in doke ka su da Yallaɓai gabaɗaya sun haɗa zufa. Jidda ce kaɗai ba ta shiga ba tana zauna ɗauke da Yumna da ke zillo kamar ta je a yi da ita.
Baki na saki da hanci ina kallon ikon Allah. Yallabai na ware hannu yana faɗin su zo su zo, suna zuwa suna kai masa duka yana tarewa suma yana kai musu suna tarewa, Baby ce ta ba ni mamaki yadda na ga ta ware ƙafa ta na kai ma Yallaɓai bugu yana ƙarewa itama yana kai mata tana karewa da sunan wasa. Na ma kasa magana saboda haushi da mamaki Jidda ce ta fara ganina tana dariya ta ce.
" Umma ko zaki shiga a yi chinese din da ke ne?
Hararan da na wurga mata ne ya sa ta rufe bakinta tana dariya ƙarisowa na yi falon ina fadin" Na shige su ni Halima. Yallaɓai me zan gani haka?
Sai a lokacin ya lura da ni ya na wani tsalle na ga kamar zai yo kaina na kwace ina faɗin" Yallaɓai.'"
Na ma kasa magana saboda mamaki Baby ta kalleni tana faÉ—in" Umma akwai dadi ki shigo mu yi da ke'
"E Umma ki shigo"
In ji Khalipa.
Hararansu na yi kafin na ce" Ni? Ai ba ni da irin ƙarfin ku Allah ya ba da sa'a."
Buɗe bakin Yallaɓai sai cewa ya yi wai na zo ko na rage kitse na ce na ji, amma ni ba zan shiga ba na tuna lokacin ina amarya Yallaɓai ya yi ta ja na da irin wannan wasan tuni na nuna masa bana so saboda shi ya iya kai duka ni kuma ban iya ba daga wasa sai a cuceka.
"Ke me ya sa ba ki shiga ba?
Na faɗa ina zama gefen Jidda. Yumna na ganina ta fara zillo tana miƙo mini hannu sai na karbeta.
"Ban iya ba Umma."
Ta faÉ—a a hankali ni da man na san ba za ta shiga ba. Ina son Jidda saboda kamewarta da Ajin ta.
"Kin taimaki kanki. Ita wancan da ba ta san ciwon kanta ba ai ga ta can ta na ware kafa kamar wata namiji."
Jidda ta fara dariya ni kuma haushi ya kume ni ganin yaran sun danne Yallaɓai suna kai masa naushin wasa gabaɗaya sun cika mana kunnuwana da iface ifacen su hauahi ya kama ni na yi ma Baby tsawa na ce ta baro wajen nan.
"Me ya sa? Ki ƙyale ta mana."
In ji Yallaɓai ganin ta yi mini wani nakwa nakwa da fuska kamar za ta yi kuka.
"Haba Yallaɓai ita fa mace ce. Ka dai yi can da su Khalipa su da suke maza amma ita bai da ce ba."
"A wajen ba shi ne bai dace ba,
amma ni a wajena Normal ne. Domin ta na mace shikenan ba za ta yi wasa da babanta ba? Ko su mata ba Æ´aÆ´a ba ne?
Sai na yi shuru saboda Yallabai tun da ya tare maganar ba zam iya ja da shi ba, ita ko jin ban yi magana ba sai ta koma cikin murna shi kuma sai ya zo ya ja hannun Jidda yana faÉ—in" Come on Daughter mana."
Sai ta maƙe kafaɗa tana faɗin" Abba karatu zan yi"
"Ba za ki yi wasa da Abba ba?
Sai ta noke kanta ba ta yi magana sai kawai ya ƙyaleta yana fadin" Kar ki zama raguwa irin mamanki mana Jidda."
Hararan shi na yi kafin na yi magana ya tare ni da fadin" Ƙarya na yi ai ragganta ke hana ki yi, wannan fa koya ma yarana nake yi faɗan kare kai domin wata rana."
Ni da Jidda muka kalli juna na tsintsire da dariya itama tana ta ya ni, ganin muna yi masa dariya ya sa ya ce" Au dariya ma kuke yi mini ko? Shi ke nan."
"Yallaɓai baka da aikin yi ne yau?
"Kin san dai ba zaman banza na ke yi ba ko?
"To na ga ne yau kana ji da karfi."
Yana É—aga power É—in hannun shi kafin ya ce" Sosai. Amma yau din rana ce ta musamman domin iyalaina da yarana."
Ina dariya na ce" Ka ce yau Happy Family day ce Yallaɓai"
Banza ya yi dani ya koma ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. Jidda ya ce ta ɗauko masa ruwa mai sanyi a fridge su Baby na kalla har suna kusa ɓaro mini da Tv ƙasa cikin ɗaga murya na ce" Duk barnan da aka yi mini baby ke ce za ki ɗauki asara domin bugun tsiya zan yi miki. Kuma ki sani ku gama ke za ki gyara mini falo na ma faɗa miki."
"Ubanta dai kike so ki ce ya gyara ba ita ba."
Ina dariya na kalli Yallaɓai kafin na ce" Ni dai ban ce ba"
"In ma kika ce ai kin san ba zai gagare ni ba malama."
"Na sani."
Na amsa ina masa dariya Jidda ta kawo masa ruwan gora da kofi bai ma zuba a kofin ba ya buÉ—e ya kafa kai kaÉ—an ya rage ina kallon shi na ce.
"Lalle Yallaɓai ka gajiyar da kanka."
"Ni ai ba malalacin namiji ba ne. Lebura ne ni mai aikin ƙarfi."
"Allah ya taimaki Md Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana."