Sashe 13
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da haka a ka bar maganar amma na ji sanyi a raina tun da ya fahimci in da magana ya dosa. Ni dai ban san ya abin ya ke ba amma ranar da Khalipa ya zo gidana zai kwana da ya yi barcin uban ya kai shi É—akin su Jidda ya kuma ce ko zai yi kukan jini su bar shi in ya gaji zai kwanta. Sai ga shi ranar barcin mu ka sha, sai da safe Jidda ke faÉ—in ya tashi yana rigima ya na kiran sunan Abba da ya ga an yi banza da shi ne ya koma ya kwanta. Tun daga lokacin na samu lafiyan Khalipa a raina na ce daman iskanci ne da na yi shuru da yanzu an daÉ—e ana cuta ta.
Ganin mun samu jituwa da Yallaɓai a wani dare da yana gida na bayan mun gama samun natsuwa sai na ce masa ina so zan koma makaranta.
"Makaranta? Wata makarantar? Islamiya?
Yallaɓai ya tambaya cikin mamaki.
"A'a boko dai. Masters nake so na koma na yi."
Kawai ba sai Yallaɓai ya fara mini dariya ba sai ka ce ya ga mahaukaciya sabon kamu nan da nan na harzuƙa.
"Mene abin dariya a mgana ta?
Sai ya dakata yana faɗin" Ki yi haƙuri amma mganar ce ta ba ni dariya ke yanzu gotai gotai da ke da budurwan ƴ'a ki ce za ki koma makaranta?
"To ana girma da karatu ne?
"A'a kawai dai."
Sai kawai ya cigaba da dariyan shi. Na cika na yi fam ina shirin fashewa.
"Kin ga yi haƙuri."
"Izinin ka na ke nema shekaran da za mu shiga nake so na koma."
"To ai ni ba zan hana ki ba amma da zan ba ki wata shawara."
Sai na kalle shi ta wutsiyar ido duk da akwai duhu a É—akin amma muna kallon juna ta hasken dake shigowa ta jikin labulan window É—in bedroom É—in.
 "Kina so?
"Ina jin ka"
Na faɗa a daƙune.
"Ki haƙura da karatun nan Sadiya. Digree gare ki fa yanzu mata ne nawa ne ke neman kwalin karatun ki ba su samu ba? Komawa makaranta abu ne mai kyau amma wahala kawai za ki ƙara ma kan ki a yanzu. Saboda ƙwaƙwalwar ba za ki haɗa ta da lokacin baya da na yanzu ba?
"Wannan ne shawaran?
Na faÉ—a ina kallon shi domin so na yi ma na juya masa baya.
"Shawaran ita ce ki bari kawai na ƙara miki jari ki cigaba da kasuwancin sai da hijaban ki kawai "
Ya gama faɗa har yana wata dariya. Raina ya ɓaci na ƙufula.
"Ka ba ni izinin na cigaba da karatun?
"Why not in kina sha'awa? Sai na ce Allah ya ba da sa'a."
"Amin"
Na fada azafafe sannan na juya masa baya sai ya biyo ni ya na faÉ—in" To jarin fa?
"Ba na buƙata"
"To shike ko kuÉ—ina sun huta"
Ya faÉ—a yana mini dariya kara shige min ya yi yana tsokanata da Sadiya ta masu mastars ke dole sai kin kamo kwalin karatuna ina jin sa na yi masa banza domin haushi ya ba ni ya ina mganar cigaba na kuma yana mini dariya.
Tun daga lokacin ya samu sara da na yi magan sai ya ce su Sadiyallle masu degree da Masters ni ko na ce da ikon Allah, na gane in ina fushi ma ya fi jin daÉ—in tsokana ta sai na daina nuna na ji haushin shi,
Maganar jari kuma tun da na ce ba na so bai ƙara mini mgana ba, ni kuma da gasken ba na so shi ya sa ma har su Ya Hamza na faɗa ma zan koma makaranta da na ce Yallabai ya amince fatan alheri kawai suka yi mini. Na gama shirina tsab saboda muna tunkaran sabuwar shekara da cewa ko Yallaɓai bai taimaka mini da sisin shi ba zan kwashe jarin hijabai na koma makaranta da shi.
****
*2020*
Da gaske na ke yi na nemi gurbin Masters a BUK Kano, kuma har na samu, har na yi cuku cuku, kuma ilai dai bangarena na farko na sake É—auka na kula da tattalin arziki wato Economics
Sannan Jidda na son ta biya Jamb tun da sai bayan sun rubuta Jam ɗin za su fara jarabawar su ta WAEC. Ko lokacin da Jidda za ta cike Jamb tare da Musbahu suka je ni ban san ina ta cike ba sai da ta dawo take faɗa minI a first chioce ABU Zariya ta cike.
"Ni dai ba ruwana kin san dai Abban ku ya ce a garin nan za ki yi karatu ba ya son nesa."
"To ni Umma ina son ABU ne kuma ai ba ga Kawu Hamza a zaria ba"
Kallonta na yi kafin na ce" Ya san da shi É—in ya ce ba za ki je ba"
Za ta fara mini magiya na katse ta faÉ—in"
Ba ruwana na ma faÉ—a miki."
Ai ko da ya dawo ta faÉ—a masa ta sha faÉ—a ya kuma ce mata ta ma cire rai ba anan za ta yi ba BUK za ta yi domin ba ya so ta yi nesa.
 Jidda na ji ta na gani dole ta cire rai tun da Ya ce ba za ta je ba to mgana ta ƙare.
A she ya je sun yi mgana da Gimbiya itama ta roƙe shi, amma ya ce ya gama mganar sa. Ni daman ban saka baki ba sabo da tun da ya kafe da wahala ya sauya ra'ayi infact nima shirin nawa karatun nake yi Yallaɓai tun ya na ɗauka wasa ne har dai ya ga na miƙe ga kaina. Wasu abubuwan duk ta online Datti ya yi mini su sauran kuma na shiga cikin makaranta na ƙarisa. Da dai Yallaɓai ya ga tabbas na samu addmission har ya na zuga ni wai na yi part-time.
Ni ko na ce full-time zan yi. Ɗa gare ni ko jika da zan yi part-time sai ya yi shuru. Ina shirin yin rigistration ne Yallaɓai ma ya ba ni kuɗi ya ce na hidimar makaranta ban tambaye shi ba kuma da bai ba ni ba, ba zan tambaya ba.
Kwatsam kawai aka fara cutar corona a Negeria, daman tun december 2019 cutar ta fara ɓulla a na mganar ta a kafafen sada zumunta.
Kafin a motsa ta fara yaɗuwa a Nigeria kafin ka ce me an shiga lockdown wannan hutun na corona shi ya ruguza burina na komawa makaranta Yallaɓai sai ya koma yana mini dariya har wani suna ya saka mini wai mai kwalin masters zaman gida dole.
Sai ga shi da ga ni har yara mun koma mun dafe a gida. Jidda ke ba ni tausayi su da ke da shirin zana jarabawar fita an yi musu tsiya.
*Janafty**TKG0B30D4*
*Littafin TURKEN GIDA 1K ne on Telegram. 09069067488.*
Kina buƙatar kayan kitchens domin ƙawata Kitchen ɗin ki? Ya ke Uwargida kina buƙatar chanza ma megidan sabbin kwanukan cin abinci? Ko kina buƙatar sauya masa kofin shan ruwa? Ko kina so ki burgeshi da farantai masu kyau da yarari? Ko Amarya ce yar ƙwalisa da ke son ƙawata gidanta da kayan alfarma? To ku matso kusaa domin JANAFTY EXLUSIVE AVAILABLE Muna kawo muku ko wani nau'in kayan Kitchen da na kwalliya gida domin farincikin ku, kuma akan farashi mai rahusa, muna aikawa da kayanmu ko'ina daga in da muke, ku tuntuɓemu ta wannan lambar domin ƙarin bayani.
09069067488
+234 706 234 9732
Ban ji daɗin ɓullowar cutar corona ba, sannan ban ji daɗin lockdown ɗin da a ka san ya mana ba gabaɗaya ƙasa ta tsaya waje ɗaya cak. Ba makarantu ba zuwa aiki komai ya tsaya, in fita ta kama ka dole sai ka saka takumkumi kamar wani ɓarawo kana tsaka tsan tsan. Shikenan Burina na son komawa makaranta ya tsaya cak shima amma duk da haka ban karaya ba faɗa ma kaina nake yi na san na ɗan lokaci ne kasa za ta daidai ta na cika burina na komawa makaranta.
Kowa na cikin takura da wannan lockdown ɗin amma sai na ga kamar Yallaɓai shi murna ma yake yi, ko don ba aikin gwammati yake yi ba ne wataƙila domin ya ga na shi ayukan ba su tsaya ba ne shi ya sa. Sai daga baya na fahimci har da zama na a gida ban samu tafiya makaranta ba kamar yadda na ci buri saboda ba shi da aiki sai tsokana ta har wani suna ya saka mini yanzu Hajiya Saadiya mai kwalin mastes. In kuma ya tashi tsokana ta da cewa masu masters dai an koma zaman gida tun ina nuna jin haushina shi kuma ya yi ta dariya har wani jin daɗin tsokana ta yake yi ranar dai na gaji na ƙufulu na ƙudirta a raina in ya sake tsokana ta sai na mayar masa da martani kamar ya ko san ina jiran shi sai ga shi ranar ya kwana a gidan Gimbiya sai ya biyo nan gidan da safe mu gaisa sai ya iske ni na ci gayu na cikin riga da wando ina zaune a saman kujeran falon ina danna waya ta lokaci ɗaya kuma ina ɗan kallon talabijin ɗin da Baby ta kunna cartoon a ke yi a MBC3.
Da Surraya Dee mai kyan ɗa'a muke chart na tura mata ciko kuɗin ta domin satin da ya wuce na siya mganin sanyi da haɗin kaza. Tana ta mini tsiya saboda sai da ta ƙara kirana ta ce ta ji shuru ba ta ji ni ba, ni kuma na ce mata lokacin muna ɗan hatsaniya ne da megidan da ya ke ta san yanayin tun da itama matar aure ce. Ta ce Mazan ne sai a hankali su yi tutsu in sun so a yi daɗi ana yi in suka so tsiya ma sun san ta kan shi. Shi ne fa muke ta hira da ita a kan matsalolin rayuwa na yau da gobe.