← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 103

Sashe 27

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya Aina Alhaji ba ya sona yanzu. Magana kaɗan sai ya rufe ni da faɗa. Hajiya Zainab ce ke juya shi ta na gaba gaba wajen zuga shi ya yi auren kuma yarinya ƙarama fa zai auro."

Ta faɗa ta na ƙara rushewa da kuka. Da gaskiyanta haka a ke ji fa in za a yi ma mutum kishiya. Balle ita da ta haɗu da kai din kishiya ita ai daman za ta so a yi mana amma kuma ba ta kyauta bai kamata in ba ya kamata in ba za ta iya hana shi ba to kar ta ingiza shi.

"Duk da haka Ma'u da kin kwantar da hankalin ki. Kin ta rama ki kashe kan ki a banza shi fa ba fasawa zai yi ba"

"Wallahi kuwa. Ki yi hakuri ki kauda kan ki. Ki yi koyi da Sadiya mana. Lokacin auran Baban su Jidda jarumtar da ta nuna wallahi sai da ta burge kowa."
  In ji Ya Balki.

"Gaskiya. Haƙuri a ke yi tun da su Maza in suka yunƙuri da maganar aure ba mai iya hana su. In ka matsa ma sai su ce ka yi gaba."
Cewar Rahila.

"Wallahi nima haka na yi ta faɗa mata ta yi haƙuri da kwantar da hankali ta ki jin mgana ta."

Ya Murja ta faÉ—a, duk suka haÉ—u suna ta mata faÉ—a ta kwantar da hankalinta ta yi hakuri da na so na yi shuru tun da ai kamar alhakina ne yakama ta, lokacin da za a yi mini kishiya ta biye ma su Anty Bahijja ana mini dariya ta manta ita mace ce zai iya faÉ—owa kanta. Ita ai kishiya yanzu ta zama ruwan dare in ba a yi miki ita a kusa ba. A gaba kaÉ—an za a iya miki ita.

"Ma'u kalle ni nan in ba ki wata shawara in har zaki iya É—auka."

Na faÉ—a ina kallonta itama sai ta bar goge hawayen tana kallona.

"Kukan ki da wani fushin ki da ramar da kike yi duk a banza ne a wajen namiji. In dai suka tashi ƙara aure in ke ta gida ba ki haƙuri ba wallahi sunan ki sorry. A gari a kalle ki a wacce za a yi ma kishiya ta ki kwantar da hankali. Shi kuma yana miki kallon mai son kanta. Dangin sa suna yi miki kallon ba a aure a ka aure ki? Mafita ɗaya ce a gare ki, ki kwantar da hankali ki dogara ga Allah. Ki kaima Allah kukan ki shi Ubangijin kowa ne mai share ma kowa kukan shi. Ki roƙe sa ya cire miki damuwa ya ba ki dangana. Ya ba ki juriya da haƙurin ɗauka. Sannan ki sani dole sai kin toshe kunnuwan ki, abin da kika ji ki nuna baki ji ba, wanda kika gani to ki nuna ba ki ji ba. Ki tsaya a matsayin ki magana in ba ta shafe ki ba ki zare kan ki ciki. Magana in dai ba ta tsallake hurumin da kika ga za a tozarki ba kar ki sake ki tanka. Yanzu gazawar ki a ke nema domin a samu damar ya ƙar ki, in ki ka yi sakaci kaɗan in ya auro ta za ki zama a bar takawarta amma in kika rumgumi haƙuri wallahi za ki ci riba. Ki zauna da ita saboda Allah sai ki ga ubangiji ya yi miki nasibin da har shi mijin na ki zai dawo yana daraja ki. Ki yi duba da ni ba irin abin da ban gani ba. Amma na yi hakuri na jure, Gimbiya kishi ta ke da ni muraran amma ban nuna mata na san tana yi ba. Kwanaki har sa'in mun yi da ita amma ban faɗa ma kowa ba. Saboda Yallaɓai ya yi mini kara ya kuma darajani ya nuna mata in ta ce za ta mini rashin ɗa'a to kamar shi ta yi mawa! Me ya jawo mini wannan darajan? Haƙurina da nuna komai ba komai ba. Na san kishi da zafi na san kishi na da raɗaɗi amma don Allah ki daure ki yi addu'a  in sha Allahu za ki samu sauƙi samun sauƙin ki kuma shi zai ba ki damar da za ki zauna ki yi ma kan ki tunanin mafita. Mafitan kuma shi ne haƙuri da kauda kai. Wata rana sai labari Ma'u. Haka  duk wata macen da aka yi ma abokiyar zama ta ke ji da farko amma in ta yi haƙuri wata rana sai dai ta tuna."

"Wannan gaskiya ne."

In Ya Aina. Ya Balki ma ta ce shawara mai kyau. Har Ya Murja sai da ta ce na gama ba ta dukkan shawaran da za su ba ta. Ma'u sai sharan ƙwalla tana mini godiya na ce yiwa kai ne amma na jadadda mata faɗa da miji ba na ta ba ne. Itama uwargidan nata na yi ne saboda ta ga ta ɗaga hankalin ta in ta ga ta kwantar da hankalinta da kanta za ta daina. Daman ai kulawa yabawa ta ga ana yabawan ne shi ya sa.

Har na koma gida auren mijin Ma'u ya tsaya mini a rai. Na tausaya mata matuka. Ba ita kaɗai duk macen da za a yi ma abokiyar zama tausayi take ba ni. Mace ba ta sanin gwagwarmayan zamantakewa har sai an yi mata abokiyar zama. In shekaru dubu za ki kwashe da mijin ki in dai bai ƙara aure ba, to ba ki san zamantakewa mai cike da fafutuka ba. Mu da a ka yi mawa muke zaune da su mu kadai ne za mu iya faɗin irin fafutukan da muke yi a zamantakewar mu na yau da kullum.

Na daɗe ban cire abin a raina ba. Kuma kusan ɗan'uwa rabin jiki duk yadda na ke jin haushin Ma'u tausayinta ya danne haushin nata bayan kwana biyu na kira ta a waya na ƙara tausarta ta, da ba ta shawarwarin da za ta riƙe su amfane ta. Tana kuka tana faɗa  mini.

"Na gode Sadiya. Na gode Allah ya saka da alheri."

"Bakomai yiwa kai ne Ma'u"

"Duk da haka dai zan yi miki godiya. Duk da tarin abubuwan ƙin da na yi miki ba ki riƙe ni ba. Matsala ta tunkaro ni kin nuna mini ke ɗin ɗin yar'uwata ce. Ba ki yi mini dariya kamar yadda na ke yi miki ba in kin shiga matsala. Sai ki ka zabi ki jawo ni a jiki ki saboda mu gudu tare mu yi tsiran tare. Na gode Sadiya kin ƙara haska mini rayuwa. Na gode ina fatan ki yafe mini duka laifukan da na yi miki."

Sai ta ba ni tausayi har sai da ruwa ya cika kwarmin idanuwana

"Na yafe miki Ma'u. Allah ya yafe mana gabaÉ—aya."

Muka yi sallama kamar ta yi min sujjada. Rayuwa kenan ban taɓa tunanin Ma'u za ta yi laushi haka ba sai ga shi a cikin lokaci ƙalilan Namiji ya birkita mata tunani. Hmm namiji. Namiji buhun ƙaya ne. Mai sauya launi gabansa fari bayan sa baƙi.

*Janafty**TKGB30G07*

Lokaci bayan lokaci ina kiran Ma'u na ji yadda a ke ciki. Zamantakewarta da Alhajin nata dai sai a hankali, tun da ya yi niyyar auren nan sai ya yi ita kuma Ma'u rashin haƙurin ta ya sa duk ta zube a wajen shi. Shi fa daman Namiji haka yake. In suka tashi ƙara aure to ba sa ji ba sa gani ne in ba ka yi haƙuri ba to za ka yi nadama ko kuma ka ga a na yi. Kuma a yadda na lura ita Uwargidan Ma'u ta na yin komai da gayya ne saboda tura ma Ma'u haushi. Ko ramuwa ta ke yi wa ya sanin mata. Domin Ma'u ta yi lokacin ta yanzu ne alƙadarinta ya ƙarye take girban a bin da ta shuƙa.

Ni dai haƙuri nake ba ta domin babu kamar haƙuri. Ba a yanzu za ta ga riban hakurin ba sai nan gaba. In dai za mu yi waya da Ma'u sai na ji ta cikin kuka Allah sarki wallahi tausayinta nake ji. Saboda ni na san zafin ƙishi, ga kuma ita abu ya haɗe mata biyu ga kishi ga ba zaman lafiya da miji. dole ta yi kuka, abin da ya ba ni mamaki cikin lokaci ƙankani wannan rashin jituwar dake tsakanina da Ma'u ya gushe. Har mantawa na ke yi da ba ma jituwa, ko ban kira ta abu kaɗan za ta kirani ta na faɗa mini ni kuma na yi ta ba ta hakuri domin shi ne kaɗai abin da zan iya faɗa mata. Sannan shawaran haƙuri na da zafi sai dai tana da riba a nan gaba.

Tana kawo mini ƙorafin cewa ranar da ya ke gidanta kusan raba dare ya ke yi waya ko chart in ta yi magana sai ya ce ba ta isa ta hana shi yin waya ba. Na yi ta ce mata ta yi haƙuri ta ƙyale shi ta riƙa shigewa cikin ɗakin ta, ba ta ji ba ballanta hankalinta ya tashi tun da ta faɗa mini ba a ɗakinta ya ke wayar ba ko falo ko cikin Bedroom ɗin shi. Sannan ta ce ba ya mgana da ita ko gaishe shi ta yi da ƙyar ya ke amsawa. Ya kuma je can Kura ya karɓo yaran ya kai su gidan Uwargidan, da ita kawai ya ke shawara yanzu ita ce ke kitsa masa komai a kanta duk na ce ta kauda kanta daman yana yi ne saboda ta yi mgana to ta yi kamar ba ta ji ba kuma ba ta gani ba. Ni ko Yallaɓai ban taɓa masa mganar ba sai ranar ya na gida na ya ji muna waya duk da tashi na yi daga falon saboda sirrina bai kamata na yi wayar yana wajen ba.

Sai da na dawo falon ne jin bai tambaye ni ba, na san halin shi Yallaɓai bai cika bin diddigi ba. Ni ce ma na faɗa masa Alhaji Mustapha zai ƙara aure. Kawai sai ya fashe da dariya ya na faɗin."Ma sha Allah. Ta uku fa zai yi ko?
Ya faÉ—a ya na kallona sai kawai na gyaÉ—a masa kai ban samu zarafin mgana ba.

"Kai ya yi ƙoƙari da kyau. Gwara in kana da shi ka cike sunnar gabaɗaya."
Chapter 27 · 0% Book details