Sashe 55
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka cikin dauriya na rabata da jikina ina share mata hawaye ina mai faɗin" Ki daina kuka kin ji ko? Ki riƙe manganganun da na yi miki kin ji ko? Ki kula da kan ki ban da kula maza. Ban amince ba in dai ba mgana ce ta karatu ba? Ki riƙe azkar da karatun Qur'ani domin daga Allah sai kan ki kike da shi a can kuma mganar zuwa gidan Ya Hamza za ki je weekend bayan sati uku huɗu haka ki je ki gansu ki huta kin ji ko?
Sai ta sake rumgume ni tana kuka, nima na riƙe ta ina bubbuga bayanta alamun lallashi sai ga Yallaɓai ya fito daga mota yana faɗin" Ki sake ta don Allah, ba na so mu yi dare a hanya"
Ko kallon shi ban yi ba na sake ta na raka ta har mota ba ta shiga ba sai ta sumbaci kumatun Yumna da ta fara barci tana faÉ—in za ta yi kewar mu.
"Mu ma za mu yi kewarki Jidda. Allah ya ba ki sa'a."
Na tura mota na rufe ina ɗaga mata hannu, hawaye suka taho mini sai kawai na juya na shige cikin gida, ga baƙin cikin Wulakancin Yallaɓai ga kewar Jidda. Sun tafi amma Yallaɓai bai yi mini sallama ba haka na faɗa a raina da na ji fitan mota da rufe get sai kawai na kifa kaina a saman dining na fashe da kuka. Ban san shigowar sa ba sai ji kawai na yi an dafa ni a firgice na ɗago sai na ci karo da Yallaɓai yana kallona kawai sai na mai da kaina ƙasa ina cigaba da tsiyayan ƙwalla.
"Sorry ko za ki shirya mu tafi ne?
Ko kallon shi ma ban yi ba saboda takaici.
"Ga Jidda can tana ta kuka itana kema kina nan kina kuka. Shi ne Daughter ta ce ko kawai ki shirya mu tafi gabaÉ—aya "
Wani irin kallon da na yi ma Yallaɓai shi ya sa da sauri ya ce" Me kuma na yi?
Yi haƙuri."
Kawai sai na ture hannunsa daga kafaɗata kafin na miƙe ina faɗin" Ka gama magana ka ce wata ta rigani. Saboda haka ku je kawai Allah ya tsare."
"Ni fa wasa nake yi da wannan mganar"
Yallaɓai ya raina mini wayau. Wai wasa yake yi? Ya kirani ya ce na shirya ko da ya ga ban shirya ba. Bai damu ba ko mgana ma bai yi mini ba sai yanzu da matar shi ta yi magana. Ƙokarin riƙe ni yake yi na fizge jikina na bar masa falon ban san lokacin da ya ƙara gaba ba. Na yi ta tafasa ni kaɗai a gida saboda da zaran na tuna wulakancin Yallaɓai sai na ji ina tafasa ni kaɗai.
Haka na yini a gida daga ni sai Yunma sai can da azahar sai ga Mubeena da Musbahu shi yake faɗa mini daman Yallabai ya ce da Anty Gimbiya za su tafi ba da ni ba amma saboda munafunci ya zo yana ce mini wai wasa yake yi mini. Zuwan su ne ya sa na ɗan saki Mubeena ce ta yi mana girki, Yallaɓai ya kira ni da kan shi ya ce sun sauka suna ma cikin makarantar, sai na kira Khaleesat na faɗa mata da man ta ce za su leka su ga wajen ita da Ya Hamza.
Mun yi waya da Jiddan itama can da gabda la'asar da su Ya Hamza suka je, ita ke faɗa mini Yallabai da Antynsu sun tafi gidan kawar Anty ina jin haka na ce gidan wannan ne da Yallaɓai ya yi maganarta ranar. Wani abu ya taso mini daga kasan zuciyata amma dai na daure. Daga baya da muka yi waya da Khaleesat ta ke faɗa mini sai da suka jira su Yallaɓai suka dawo a bakin ta na ke jin sun yi dare nan za su kwana amma yara kawai za su bar musu Yallabai da Amaryansa Hotel za su kama.
Ni fa daman na faɗa, ni na san da wata a ƙasa. Namiji uhm ni Yallaɓai zai yi ma haka? To ai shike nan, shi gogan sai dare ya kira ni ina ga bayan ya sun gama natsawa a hotel ɗin da suka kama sannan ya kirani yana daidaiciyar mgana.
"Sadiya mun yi dare za mu tsaya mu kwana zuwa da safe.'
"Allah ya nuna mana goben lafiya."
Na faÉ—a a yatsine, na yi kums shuru jin ya yi shuru har ina jiyo maganar Gimbiya amma ban san abin da ta ke faÉ—a ba.
Ina shirin kashe wayar ne na ji yana faÉ—in" Yara suna gidan Ya Hamza"
"Anty Khaleesat ta faÉ—a mini."
Na faÉ—a da gayya domin ya san na sani.
Jin na ji labarin a in da suke yasa bai ja mganar ba ya yi mini sallama saboda bariki har yana rage murya yana faÉ—in" Na yi kewar Sadiya ta "
Ashar ne kawai a bakina shi ya sa na yi shuru domin in na yi magana zan zage shi ne shi ya sa na yi kamar ban ji ba.
"Ina Yumna ta? I miss her."
"Ta yi barci."
Na faÉ—a a gajiye ban bari ya sake magana ba na yi saurin cewa" Zan kwanta sai da safe."
Ban jira cewarsa ba, na kashe wayata ina jan uban tsaki wayar na hannuna ina jin wani abu na taso mini. Ina tuna me na yi ma Yallaɓai da zai shirya mini wulakanci haka.
Shigowar sako daga waya ta, ya sa na duba Yallaɓai ne.
"Ki yi haƙuri My Sady kin ji?
"I love you."
"Munafuki"
Na faɗa a fili kafin na dankwafar da wayar. Barcina ranar rabi da rabi ne, da na farka sai takaicin Yallaɓai ya taso mini da safe ina ganin kiran shi ba ƙi dagawa. Sai can da muka yi waya da Jidda ta ce sun ta so ba su haɗu ba saboda yau ta fara attending ɗin lactures na yi mata fatan alheri sannan muka yi sallama cike da kewa. Na san za su sauka a gidana shi ya sa ki girki ban yi ba suka dawo ga yunwa ba abinci sai fita Yallaɓai ya yi ya siyo abincin ai yadda ya ganni ina cika ina batsewa ya san in ya yi mini magana to zan fa fashe na fara masifa shi ya sa bakin sa alaikun ya fita ya je ya siyo kuma har ni ɗin ya siyo mawa na karba kuma na ci. Sai da yamma ya tara matarsa da yaran su ya mai da su gida da wuri ya dawo yana mini yar murya da labarin Jidda.
Kallo ni bai ishe ni ba, ya yi ya gama yaga ban tanka shi ba sai ya koma ban haƙuri.
"Kin ga ta ce mini za ta je bai kyautu na ce mataa a'a ba. Ni kuma ganin ba ki ce mini za ki je ba shi ya sa ban kawo da ke ba. Ki yi hakuri na san kina da kara kamar yadda kika ce ke da ita kun zama É—aya."
Ni kallon shi kawai na ke yi, domin ni ba zan ɓata ma bakina akan shi ba tun da na san duk yaudara ce ta maza. Da na ga zai dame ni sai na ce masa ni ba haushi na ji ba amma da zai ƙyale ni da maganar nan da ya samu zaman lafiya. Shi ya sa sai ya yi shuru da mganar, ranar dai ba mu yi kwanan daɗi ba sai washegari na ɗan saki muka shirya amma na daɗe ina kallon Yallaɓai da wulaƙancin da ya yi mini amma tun da ya karyata kansa sai na ƙyale shi ɓan kara ta yar da mganar ba..
Na ɗauki girman na yi hakuri na share, Jidda ana can an kwarari sati uku a makaranta ko da yaushe ina kiran ta na ji halin da take ciki. Yallabai ma ko da yaushe satin ma ya shiga Kaduna sai da ya biya ya ganta. Mu dai ta bar mana kewa koda yaushe Baby zencenta kenan Ya Jidda, ni kaina ina kewarta da sanyin halinta gida ya rage daga ni sai Baby sai Yumna.
*****
Cikin Gimbiya ya shiga watan haihuwan shi a bakin Yallaɓai na ji, hankalin shi duk ba a kwance yake ba, ni dai in yana magana ina yi masa fatan Allah ya sa ta sauka lafiya.
EDD dinta ma bai cika domin karshen watan march ya ce mini za ta haihu amma a ba ta kai ba ranar wata laraba yana gidana da safe ta kira shi ba ta da lafiya ya fita. Tun da ya fita bai dawo ba kuma bai kirani ba sai ni ce can na kira shi , a lokacin ya ke faÉ—amini suna asibiti haihuwa ce amma har lokacin ba ta haihu ba.
"Aikin za a sake yi mata?
"A'a sun ce a dakata a gani za ta iya haihuwa da kanta."
Fatan sauka lafiya na yi masa na kashe wayata. Da a baya ne tsab zan shirya mu je, ni kan ai Gimbiya ta gama yi mini hankali ban ko a raina zan iya zuwa ba. Har dare da Yallaɓai ya dawo ba ta haihu ba, haka muka kwana da shi bai yi barci ba ni dai barcina na sha to ina ruwana, ai ni na gama hana kaina zaman lafiya a kan Gimbiya. Washegari tun safe ya tafi asibitin har yana jirana ko zan je na duba ta na ce ya je zan yi ma Hauwa ko Munnira waya mu je tare nan ko ba zuwa zan yi ba kuma ban kira kowa ba. Ba ta haihu ba sai bayan la'asar kafin ya kirani a status ɗin Anty Bahijja namiji Gimbiya ta sake haifa.
Anty Bahijjan ma a ƙasan hoton ta rubutu mai farar haihuwa ta sake yo wata farar ƙal ma kuwa. Na yi taging na yi Allah ya raya domin ni ba na baƙin ciki.
Sai daga baya angon karnin ya kirani ya faɗa mini ta haihu da kanta. Amma za su riƙe ta zuwa gobe ta zubar da jini sosai."
"Ayya. Allah ya raya ya kuma ba ta lafiya"
Ya amsa da Amin Amin.
"Kin fito ne?