Sashe 3
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Lafiyanta ƙalau na zo ganinta ne kawai."
"Ki ce zumumcin ganin Amina ya motsa. To yara fa? Ko suna Gwamnaja?
"Ban sani ba. Gida na bar su tare da babansu."
"Wata ƙila suna gidan Gimbiya."
Da haka muka bar mganar hira muka É—an yi sama sama kafin mu yi sallama sai da ta ce yaushe zan dawo?
"Ban saka rana ba."
"Eyye. Kin ji ki tsaya ki É—an huta"
Ina mata dariya daga nan muka yi sallama. Ita ta faɗa ma Hauwa ina kaduna sai gashi ta kirani, su har sun damu da ni amma wanda ya ijiye ni na koma ni da banza duk ɗaya a wajensa. Ban taɓa tunanin zan kai tsawon kwanakin ba tare da Yallaɓai ya neme ba amma ganin har na kwarari sati biyu bai kirani ba sai na daina mamakinsa na kuma ɗauka da gasken na gama yi ma Yusuf amfani a rayuwarsa. Duk na yi waya da su Ya Aina amma ban nuna musu ba na gida ba har Ya Balki mun yi magana wasu maƙotan ta na son Hijabai na ce na hannuna sun ƙare sai an sake kawowa.
Ban faɗa ma Amina komai ba, itama ba ta dame ni da mgana ba. Amma tabbas a raina na san cewa ta yi shuru ita kanta ta san lafiya lafiya ba zan zo gidan ta na shantake ba. Ashe ma duk ta na lura da motsi na ban sani ba sai ranar da na ke da sati biyu muna zaune a falo ni da su Yunma in na kallon su tuna wa na ke yi da nawa yaran da suka yi min nisa ina cikin kewarsu sai na yi kamar in kira Yallaɓai ba sabo da shi ba sai saboda yarana amma sai na ji na kasa domin wani irin haushin shi na ke ji haushin da ban taɓa ji ba shi ya sa na ke danne komai amma Allah kaɗai ya san damuwar da na ke ciki. Duk dare sai na yi kukan ɓarin cikina kuma sai na ji na ƙara jin haushin Yallabai daga ƙasan zuciyata.
 "Ya Sadiya"
Amina ta kirani sai na bar kallon yaran da ke wasa a tsakar falon na koma ina kallonta. Tsaye ta ke a gefen kujeran da na ke zaune daman muna tare ne muna hira sai ta tashi ta shiga ciki.
"Mu je É—aki na mu yi mgana."
Ban kawo cewa mganar Yusuf ba ne da ba zan yi saurin tashi na bi ta ciki ba
Gefen gadonta muka zauna gabaÉ—aya.
"Me ya faru?
Na faɗa ina kallonta ganin ta yi shuru ta ƙi mgana.
"Ya Sadiya kun samu matsala da Baban su Jidda ne ko?
Sai na kalleta kafin na ce" Me kika gani?
"Abubuwa da yawa. Ba ya kiran ki ke ma haka. Infact ma ni ban taɓa ganin ya kiran ki ba tun dawowar mu daga asibiti."
Sai na yi shuru na kasa mgana saboda ba ni da amsarta a lokacin
"Ko bai san kin taho nan ba ne?
"Ya sani"
Na amsa mata da sauri ina ƙokarin mai da kwallar da suka cika min ƙwarmin idanuwana.
"Ya sani fa kika ce?
"Ya sani Amina."
Wannan karon na faɗa cikin kwarin gwiwa. Sai kuma hawaye suka ke ce min wasu na korar wasu sai ta ruɗe ta riƙo hannayena ta na faɗin.
"Na shiga uku ba dai sakin ki ya yi ba ko?
"Bai sake ni ba."
Na amsa mata ina kallonta ina ganinta ta sauke wata ajiyar zuciya kafin ta ce" Alhamdulillah da sauƙi."
Sai kuma ta koma ta na kallona kafin ta ce" Me ya faru?
Na kasa mgana kawai sai kuka ya kece min, na riƙe hannayena Amina a saman fuskata ina kuka har da shessheƙa.
"Amina wai ni Yallaɓai ya kalli idanuwana ya ce ina yi ma baƙin ciki da Matarsa da ƴaƴansa saboda ban ƙara haihuwa ba."
Amina ta ƙwalalo idanuwana ta na kallona. Hannayenta na jinƙe cikin nawa ina jin kamar za ta iya cire min ƙuncin da ke zuciyata in na faɗa mata halin da na ke ciki.
"Amina bai tsaya anan ba sai da ya yi min gorin haihuwa. Ya ce ina baƙin ciki da yayansa kuma sai dai na mutu. Sannan ya ce gida gidan shi ba gidan ubana ba ne."
"Shi Yallaɓan ya ce miki haka?
Amina ta katse ni cikin mamaki da alja'abi na gyaɗa mata ina kuka ina ba ta labarin duk abin da ya faru daga farko har ƙarshe na ƙarishe da faɗin" Amina na taho gidan ki cikin damuwa da kuka. Tsawon kwanaki nan Yallaɓai bai nemi ba? Me ya ke nufi? Hakan da ya yi ba ya nuni da abin da ya faɗa har zuciyarsa ba ne? Amina yau Yallaɓai ya nuna min ba ni da sauran amfani a wajensa Gimbiya ce matar arziƙi uwar yaya maza ita ce mai amfani yanzu a wajen shi da ƴan'uwan shi."
Na faɗa ina kuka. Kukan baƙin ciki kukan kishi da kukan nadaman yadda na yarda da Yallaɓai daga ƙarshe ya tozartani na baro gidanshi na zo gidan ƙanwata ina zaune. Me ya fi wannan tozarci da cin zarafi?
Amina ma kamar ta yi kuka mamaki ma ya hana ta mgana.
"Shi Yallaɓai nan duk ya aika miki haka Ya Sadiya?
"Ya wuce wai Amina. Ni yanzu na rasa ya zan yi? In na kashe aurena ina za ni Amina? Shekara sha takwas da aurena jidda ta isa minzali amma ban wuce tozarcin Namiji ba."
Sai a yanzu na ke jin sauƙi sauƙi da na ke fada ma Amina damuwata. Amma a kasan raina danƙare ya ke da nadama. Nadamar yadda na yarda da duka kalaman Yusuf Inuwa tun a ranar farko na da fara ganin shi da ace ban bari ya ruɗe ni da kalamansa ba da wata ƙila wannan ranar ba ta zo ba.
"Gaskiya ya ba ni mamaki. Ƙiri ƙiri ya yi miki rashin adalci ki yi mgana kuma ya nemi tozarki? Tsskani ga Allah ya dace ya ce da yaro zaku riƙa kwana? Ba ya tunanin in kina buƙatar sa fa?
"Shi ba ya buƙatata domin ina tunanin rabo na da Yallaɓai na ƙarshe ranar da na samu cikin da ya zube ne Amina. Sai ya zo gida na har ya koma can wani abu ba ya shiga tsakanina da shi."
Na faɗa ina ƙokarin danne abin da ke taso min.
"Bai kyauta ba. Kuma wallahi zai gane kuren shi."
Kai kawai na girgiza na kasa mgana saboda in na zauna ina faÉ—in wani abun ma sai a ce na yi masa sharri ne.
"Amina ki yi fatan ki mutu tare da mijinki da ƴaƴan ku. In kuma ƙarin aure na cikin kaddaran shi ki yi ta fatan Allah ya ba ki haƙuri da juriya sannan ya ba ki wuyan ɗauka. Domin kishi na da zafi sannan masifa ne kuma bala'i ne"
Amina sai ta yi shuru ta kasa mgana. Ni kuma ina share hawayena na cigaba da faɗin" Domin duk zaman lafiyan da ke tsakanin ki da mijin ki in ya auro ta sai ta shiga tsakanin wannan zaman lafiya. Sannan duk amincin da ke tsakanin ki da shi sai ta zo ta raba shi haka ma duk yardan da ke tsakanin ku wata rana sai ya ce ke ba abin amincewa ba ce. Duk faɗan da za ku yi da mijin ki ke kaɗai ba zai kai girman faɗan da za ku yi in ya karo aure ba ki sani duk haƙurin ki da kawaicin ki wara rana sai an ƙure ki. Ki sani kishiya ƙalubale mai zaman kanta a gidan aure wanda ba a yi mawa ba ko za a bashi labari ba zai taɓa ganewa ba sai wanda ya tsinci kan shi a yanayin kaɗai zai iya sanin raɗaɗi tare da ƙalubalen."
"To in haka ne Allah ya raba mu da kishiya."
"In ta alherin ce fa ?
"Ko ta alherin ce Allah ya yi mana tsari da ita."
Sai Amina ta ba ni dariya sai da na murmusa. Ita manaki ta ke yi a tunanin Yallaɓai ba zai taɓa juya min baya ba na manta namiji mai manta alheri wasu mazan da yawa batulai ne, an yi musu alheri su manta su nemi saka ma mutumin da ya yi musu alheri da sharri. Amina ta ce ita ma ta na goyon baya kar na sake na neme shi har mahadi ko ya bayyana tun da bai san mutumci ba.
Maganar da muka yi da Amina sai ya fama min da mikin da ke cikin zuciyata. Ranar sukuku na yini sannan na daɗe ban yi barci ba ina tunanin mafitar da zan nema ma kaina ba zan zauna takaicin wani namiji ya kashe ni ba, in ma bai kashe ni ba ya saka min zuciyan da zan rayuwa sunan mattaciya. Ya zama dole na koyi jajircewa na kuma koyi tsayuwa da ƙafafuwana. Na yi tunanin ba zan cigaba da fakewa a gidan Amina ba in mijin ta ya dawo lamarin zai zama wani iri. Ba kuma zan koma Kano ba saboda duk da in da na je ba za a fars duba masalahata ba. Ni kuma a yanzu na shirya ma Yallaɓai da duk abin da ya ke takama da shi. In koma gida Alhajinmu ba zai zauna ina zauna a gida kuma ya yi shuru ba. Gwara kawai daga nan na wuce Yashe wajen Baaba Aminu na fashe masa da kuka ya na tausayi na tabbata zai fara duba masalahata kafin wani abu ya biyo baya.