Sashe 73
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwana uku tsakani ranar wata laraba Munnira ta kira ni a waya tace ko ina gida na ce mata ina gida. Sai ta ce mini gata nan zuwa, da maganar mu ba a daɗe ba sai ga ta tun da na ganta na san da magana. Na kuma san bai wuce labarin auran Yallaɓai da suka samu labari. A daran jiya yake faɗa mini Baban Rabi'a ya neme sa yau zai je su sake ganawa. Ina kuma da tabbacin ya gama binciken shi ne zai ce ya turo magabantan sa. Tun da Yallaɓai ba shi da abin ƙin daga asalin shi har rayuwarsa duk da ɗan adam tara yake bai gama cika goma ba.
"Kwana biyu ke da Hauwa kun ɓoye?
Na faÉ—a lokacin da na shigo falon, da man ina cikin bedroom É—inna Jidda ta sanar da ni zuwanta.
"Wallahi ya gida?
Ta faÉ—a tana É—aukan ruwan da Jidda ta kawo mata na gora ta zuba a kofi ta fara sha sai ni kuma na zauna gefenta ina faÉ—in" Ya yara?
Kwana biyu ba mu haÉ—u ba."
Sai da ta gama shan ruwa ta dire kofin a saman centetr table ɗin dake falon sannan ta ce" Uhm ke ce ai kin ɓuya. Yanzu ma dalili ne ya sa na neme ki."
"Wai auran Yallaɓai?
Na faÉ—a ina dariya.
"Au ashe ma kin san abin da ya kawo ni."
Ina mata murmishi na ce" Na san dai yanzu shi ke trending."
"Uhm wai ashe Yallaɓai aure zai ƙara ba ki sanar da mu ba Sadiya?
"Wallahi na kasa iya faÉ—a ma kowa. Amma na bari in an saka ranar sai na kira ku mu yi maganar."
"Da gasken gasken dai auren zai ƙara?
Ta faÉ—a cikin tantama.
"Ya wuce wai fa. Yau ma yace mini zai sake komawa Baban Rabi'atun ya sake neman shi."
Na faÉ—a ina kallonta.
"Sunanta kenan? Rabi'atu?
"E. Yar maiduguri ce amma an riƙeta anan Kano. Yarinya ce ƙarama ajinta ɗaya ma jami'a."
"Duk a ina kika san wannan labarin?
"A ina kuwa? A bakin uban gayyae mana."
Na faÉ—a ina dariya sai Munnira ta gyara zama tana faÉ—in" Ba Shakka."
Sai kuma ta yi shuru.
"Ke a ina kika ji? Na tabbata dai maganar ba ta fita ba sosai."
"A bakin Jamila na fara ji, sannan jiya da daddare labari ya kawo labari Nasir ke faÉ—a mini. Ashe wai har sun samu matsala da mutuniyarki?
"Wac ce?
"Gumbiya mana."
Sai na ware ido kafin na ce" Subhanallah da shi Yallaɓan?
Munnira ta yi dariyan mugunta kafin ta ce" Wai ita ana dole ba zai yi mata kishiya ba. Ta manta ke ma da ita aka yi miki kishiyar? Wanzami ba ya son jarfa"
"Me ya faru ne! Ni wallahi ban sani ba. Na ga dai ya kwaso mini yara ya kawo mini da na yi magama sai ya ce bata nan ta je Rano."
"Af yaji ta yi "
"Yaji?
Na faÉ—a ina zaro ido.
"Wallahi faɗa suka yi a yadda Nasir ya ce shi Ya Tafidan ya faɗa massa. Tun da ya faɗa mata zai ƙara aure ba su samu fahintar juna da zaman lafiya ba ranar kawai ta saci wayarsa ta dauki lambar yarinyar ta kirata ta yi mata zagin kare dangi. Ashe yarinya yar gari ce ta yi recording yana zuwa ta kunna masa shi kuma da ya dawo sai ya hau ta faɗa shi ne ta miƙe yana faɗa tana faɗa daga ƙarshe zai bar mata ɗakin ya ce ta ja masa riga har tana yaga masa, ta kuma ci kwalan shi ta ce in dai ya rantse sai ya yi auren nan da wannan yarinya ita kuma sai ya sake ta. A cewar sa ya yi ta ƙi sakin shi sai ya fizge kan shi ya ture ta gefe ta faɗi shine ta hau kuka wai ya daketa akan wata banza gari na wayewa ta tafi Rano har yau ba ta dawo ba shi kuma ya ce ba zai je ya yi bikonta ba tun da abin da ta yi rashin tunani ne."
Tagumi kawai na yi na ma kasa magana. Sai da na ce mata ta bi a hankali. Amma sai take ganin kamar ni ina goyon bayan Yallaɓai ne.
"Na je Gwammaja jiya har Nene ba ta saka baki a maganar ba ta ce Gimbiyar ce ba ta kyauta ba.. aure ya ce zai ƙara ba wani zunibi ba"
"Ina su Anty Bahijja?
"Ohom musu. A bakin Suwaiba na ke jin Mimiaco ce kawai da Nene ke bayan Tafida. Anty Maimuma da Anty Bahijja duk yan bayan Gimbiya ne kar a yi mata kishiya."
Ban san ina dariya ba sai da na ga ina ƙyaƙyatawa.
"Wato kar a yi mata kishiya tuj da ta su ce? Ni da bare ce ai suna gaba gaba wajen ba shi goyon bayan ni ya yi mini ko?
"To da man. Ai ni farinciki na yi da zencen ƙarin auren na. Lokaci ya yi da Gimbiya za ta ɗanɗana abin da kika ɗanɗana ta ji in da daɗi."
"Wallahi. Welcome to the Game."
Na faÉ—a ina dariya har muna tafaww. Ba wai ina murna ba ne amma dai na ji daÉ—i a kallah dai za su san cewa yau gare ka ne gobe ga wanin ka jibi ma a kanka ne zai faru.
Muna tare da Munnira har bayan la'asar sanman ta tafi, Yallaɓai da wuri ya dawo ya yi wanka aka saka manya kaya ana ƙamshi ya tafi. Tun kafin ya dawo ya kirani a waya da albishir ɗin Baban Rabi'atu ya ba shi da man ya tura magabantan shi. Murna kamar Yallaɓai zai yi hauka da ya dawo haka ya rumgumeni cak kuma ya ɗagani yana juyi da ni a tsakiyar falo gaban yara. Ni dai na daki kafadan shi ina faɗin ya sauke ni. Ai na ga abin mamaki haka ya bi su Jidda ɗaya bayan ɗaya yana rumgumansu cikin farinciki.
"Abba me ya faru ne?
Ko ka samu wasu kudaÉ—e ne?
Jidda ta faÉ—a tana dariya.
"Abin da na samu ya fi kuɗi daraja My Jidda. Ƙaramar Anty zan sake kawo muku."
Daga ita har Baby shuru suka yi kamar ba su gane ba.
"Jidda Baby, aure zan ƙara. Baban Antynku ne ya ce na turo da magabatana."
"Allah ya sanya alheri Abba"
Jidda ta faÉ—a cikin natsuwa its ko mara kai Baby sai ta fara tsalle tana faÉ—in" Abba yaushe bikin?
"Ba zai É—au lokaci ba?
Ya faÉ—a yana shafa kanta falona ya kaure da ihun su har da su Khalipa da ba su san me ake ciki ba. Yumna ya É—aga sama yana mata wasa kafin ya kalleni yana faÉ—in" Rabi'atu ta ce ita fa Yumna za ki ba ta."
"Ba dai uwata ba kam!
Na faÉ—a da iya gaskiyata sai ya fara dariya.
"Jidda zaki ba ta ko Baby?
"Jidda ai É—iyar Gimbiya ne. sai dai ko Baby ko Khalipa."
"Ta fi son mace ta ce mini. Kin san tana ganin hotin su a wayata. Ita dai Yumna take so."
Ni tsabar mf zumuÉ—in Yallabai ya sa ban samu amsa masa ba.
Abinci ma bai ci ya ce ya ci a can wai an kawo Baba ya ce sai ya ci shi kuma ya kasa yi masa gardama su Baba manya. Ina so na yi maganar Gimbiya ina jin tsoro kar ya ce na yi shisshigi, ganin yana cikin farinciki yasa na yi kumdunbala na yi masa maganar amma sai ya shashantar da maganar da cewa na ƙyaleta za ta dawo.
"To ko za ka je ka dawo da ita ne? Ka yi mata uzuri kishiya fa zaka yi mata?
Kawai ya taso mini kamar ni cw na yi masa laifin
"Ke ba kishiyan na yi miki da ita ba, kin tada mini hankali? Ke da sai bayan an ɗaura ma kika sani kin sama mini zaman lafiya sai ita da na faɗa mata cikin lalama amma ba yadda ba. Kin ji irin zagin da ta yi ma Rabi'atu ba domin ta yi hankali ba ta biye mata ba daya kike tunanin lamarin zai tsaya? Kuma na so ina nuna mata kuskurenta amma daga ƙarshe ni ta yi attaking ina matsayin mijinta. Ban ce ta tafi ba amma tun da tafi wallahi kafata ba zai taka zuwa Rabo saboda ita ba kar Allah ya sa ta dawo ta gani in za a fasa komai ne saboda tafiyarta."
Ni dai haƙuri kawai na ke bashi domin na ga ya ɗau zafi da yawa.
"Wallahi ko Nene na faɗa mata ta cire bakinta ba in da zan je kuma haka nan ta ƙyaleni . Kema abin sda zan ce miki kenan ki zura ido kawai ba ruwan ki a wannan maganar."
Tun da na ji har Nene ma an bata haƙuri ni a suwa sai na kama kaina..
Yadda ma yake ta shirin turawan nan tuni ya shafe babin Gimbiya.
Aure fa ya tabbata da gaske Ya Usman daga porthercout ya zo Kano saboda maganar. Shi da Tafidan Rano Baffan Gimbiya da Kawu Sa'adu da Kawu Abba da Tariq suka je neman ma Yallaɓai auran Rabi'atum
Sun je da kudin gaisuwar iyaye dubu ɗari huɗu, ga kayan saka rana mota guda. An yanke musu sadaki dubu ɗari biyar, sanaan an yi maganar tana karatu zai barta ta cigaba. An saka rana wata ɗaya cikin na biyu. Ƙarshen January, shi Yallaɓai ma ya so ƙarshen watan Desember ne amma iyayenta suka ce aa a ba su lokaci suma ai suna da na su shirin sannan a garin maiduguri a gidan mahaifinta za a ɗaura auren
. Duk da suka dawo a can gidan Nene suka yada zango. Ni kuma a bakin uban gayyar na ji labarin yadda ta kaya da ya dawo da daddare.
"Ma sha Allah. Lamari ya yi daÉ—i Allah ya sanya alheri ya nuna mana lokacin da rai da lafiya."
"Amin Amin Abar ƙaunata."
Har yana sumbatar leɓena cikin farinciki, ranar a gaba ma Yallaɓai ya yi waya da Rabi'atun har ya na ba ni ita muka gaisa.
Tana wani maƙale murya da na ce Allah ya sanya alheri ya nuna mana lokacin da rai da lafiya.
"Amin Anty na gode."