← Book details Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 103

Sashe 81

Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ita ta ce ba za ta yi ba Sadiya ba zan kuma taɓa matsa mata ba. Ke ce na ke da yaƙinin kina yi ma zaman auren mu kara na kuma san wannan karan ma ba za ki ƙi yi mini karan da kika saba ba."

"Uhm"

Na faɗa a ƙasan makoshi.

"Ba zan takura ba, in kina ganin ba zai yuyu ba sai mu bar shi na cigaba da oder. Amma kamar bai kyautu ina da matan aure har biyu na riƙa siyan abinci a waje ba, sannan ita kanta ya za ta fassara lamarin?

Sai na ga kuma gaskiya ya faɗa duk da wata zuciyar na ce mini na ce ya cigaba da siya amma na kasa. Sai da na tuna da kalaman Alhajinmu da ya ce  na yi ma abokan zamama alheri da ƙarfina da jikina da aljihuna. Ruwan su ne su ma yar da alheri da alheri ko su ma yar da alheri da sharri. Ni dai in dai na yi don Allah ladana na wajem Ubangiji kuma ya gani na sauke haƙƙi da nauyin zaman tare. Sai kawai na ce masa to shike nan da yaushe da yaushe za a riƙa zuwa karɓan abincin?

Cikin murna ya ce" Ko sai É—aya a rana is ok."

"Shike nan Allah ya ba ni iko."

"Na gode Abar ƙaunata. Allah ya kare mini ke."
Na amsa da Amin a ƙasan maƙoshi, ban wani ja mgana ba muka yi sallama bayan ya ce mini za a kawo cefane a raina na ce tunda hidimar amarya ya tashi ba. A washegari aka kawo cefane har da su Nama da kaji, Sadi ne ya kawo sabon Direba Salisu Yallaɓai ya ɗauke shi ya koma direban kamfani. Sai Salisun ya kawo Sadin a matsayin madadin shi anan gida tun kafin ma bikin ga shi shima har an saba ya fara zama ɗan gida ya kai yara makaranta ya dawo da su sannan ya yi aike aike da kawo cefane.

Ban faɗa ma kowa ba, ni na ke yi abincin Sadi na kai ma Yallaɓai da Amarya. Kuma a satin na je gidajen su Hauwa na kai musu sakon su amma ban amince na yi musu ma zencen ba, dalilina shi ne ba komai ne na aure ya ke buƙatar fallasa ba na bar ma cikina. Kuɗi Yallaɓai ya tura ma Jidda ita da direba suka tafi kasuwa ta yi siyayya. Kayan abinci da man daga gida take ɗiba kayan kwalama ne su bickit sai mayuka da su pad da kayan tea ta je ta siyo. Anan gida ta yi miyanta ta yi cincin  da Donut za ta tafi da shi, tun ina sa ran zuwan Yallaɓai har na cire ma raina, ganin ma daga wajen Amarya sai ya fara dawowa wajena kafin ya koma wajen Gimbiya shi ya saa na kira Surayya Dee ta aiko mini da haɗin kazar sababi na uwargida. +234 803 277 3332
Sai kuma a gida ina ta cin ganye da kayan marmari, ba domin wai na gyara ma Yallaɓai ba aa sai domin nima macece ina bukatar na gyara kaina. Ko da na ba ma arba'in baya ban tsufa ba akwai  ruwa a jikina har yanzu kuma ko gobe ai ruwa na mganin dauɗa nima asabuwar Yallabai ya aure ni muka gurji juna har ta kawo mu ga yau, saboda haka in ma ya manta mafari zai dawo mafarin na shi dolen shi dai.

Ba Yallaɓai ya zo gidana ba sai ranar lahadi da safe ranar da ya cika sati ɗaya a ɗakin Amarya. Kun gan shi da wata bakar jallabiya ya yi kiɓa ya yi haske ga tumbi ya ƙara tasawa. Shima dalilin zuwan saboda tafiyar Jidda ne. Adnan ne zai ma yar da ita. Ita ta kira shi ta ce za ta tafi ba su yi sallama sai ga shi da jallabiya iriin ma fitowar na dole ne.
Baby da Jidda suna ta murna ganinsa suka dafe shi suna ihun ga Abba ni ko kallon su ban yi ba. Yallaɓai ya ba ni mamaki muna gari ɗaya? A wayar ma sai ya ga dama yake kira ko kuma in ta shi buƙatar ya taso shi zai kira yana rage murya yana daidaiciyar mgana.

Jidda na tafiya kunya ce ta hana shi shima ya wuce sai ya É—an shigo ciki. Ni ko abun kari ban yi masa ta yi ba sai ya ce wai na ware shi kamar ba É—an gida ba.

"Na É—auka ka ci kai da Amarya."

"Ba mu tashi ba wayar Jidda ce ta tashe ni, na baro ta can tana barci.'

Ko kunya Yallaɓai ke faɗa mini haka na tusa buredi a bakina na yi masa wani kallon renin wayau bai ma gani ba yana can yana mgana da Baby, Yumna kuma ta ishe mu da kiran sunan shi Abba sai ya amsa sai ta yi shuru sai kuma ta sake kiran shi. Tare da mu ya zauna ya karya yana hira da ya'yan shi, ni ina gamawa na shig ciki sai da zai wuce ya biyo ni yana yi mini sallama nan ne na ke nuna masa sauran kayan da dangin Rabi'atu suka kawo mini sannan na faɗa masa na yi kyauta da wasu.

"Kar ki damu kayan ki ne fa. Ke suka kawo mawa kina da damar yin abin da kika ga dama da shi, yau ko da ma nawa ne tuni na yarje miki ki aiwatar da gabaci in dai ba na nan."

Ban bari daɗin bakin shi ya yi tasiri a kaina ba na yi masa sallama. Har yana cewa ko rakiya babu? Na shige tiolet ina faɗin fitsari ya matse ni ya fita yana dariya shi kam shi ya san na zille ne kawai sai da na ji tashin motarsa sannan na fito ina ƙunƙuni ni kaɗai.
A ranar na kira Alhajinmu na gaishe shi shi ne yake faɗa mini jiya Yallabai ya kawo masa Amarya ta gaishe shi Amarya ta kawo masa kyautar turare. Sai na saki baki ina jin Alhajinmu kawai ina mamakin Yallaɓai bayan daɗin baki yanzu har makirci duk ya iya.
Kafin mu yi sallama Alhajinmu Jadadda mini yake yi na zauna lafiya da abokan zamana don Allah , na ce to ni kam ai ban isa na ƙara komawa gida na ce Yallaɓai ya yi mini wani abu ba sai Alhajinmu ya ce sharri na yi masa.

Can da yamma sai ga kiran Yallaɓai da cewa anjuma zai kawo su Gimbiya gidana zai yi zama da mu.
"Har sai ka tarkato su gidana ? Ka yi musu duk maganar da za ka yi acan ni in ka zo sai ka faÉ—a mini ba ni da matsala."
Na faÉ—a masa haka har a cikin zuciyata
Kawai sai ya fara mini faÉ—a wai ni zan faÉ—a masa ga yadda zai yi?

"A'a yi hakuri daga shawara."

"Riƙe shawaranki sai na ce ina ɓukata. Malama za mu zo anjuma nan sai ki hana ɗin."

Daga haka ya katse wayarsa sai na bi wayar da kallo ina riƙe da baki da man tun lokacin da ya kira wayar na ji muryansa a sama ina kyautata zaton shi da Gimbiyarsa ne aka tafka wata tsyar shi ne zai sauka akaina ƙaramin tsaki na ja ina tura baki kamar yana ganina

Ni da Baby mu ka share gida muka goge. Tare kuma muka yi girki cous-cous da kayan lambu mai hanta sai na yi mana kunin Aya da zoɓo muna gamawa na bar mata gyaran kitchen na ce kuma ta jera komaI a saman dining ni kuma na shiga wanka. Gayuna na ci da man ni duk wanda ya sanni ya sani da ban yarda da zama haka ban gyara kaina da jikina ba. Wata doguwar rigar amfata na saka sabuwa ban ma taɓa sata ba, ɗinkin A shafe ne ta yi min ɗas a jiki na kashe ɗaurina na maryam babangida. Da man na yi kitso Maman Nana ranar asabar ta zo ta yi mana ni da yara har da Jidda tun da ana gobe za ta koma ne.

Na idar da sallar isha'i Saude ta kirani a waya na tsaya muna gaisawa. Har suka iso ma ban sani ba sai da Yallaɓai ya shigo ciki da kansa. Ji kawai na yi an ruƙumƙumeni ta baya tunda na ji  kansa a saman wuyana na san shi ne in Yumna ce kafafuwana take rumguma
Sama sama na yi sallama da Saude ina ture Yallaɓai.

"Ke ba ki iya zuwa tarban miji ba ko?

Hararan shi na yi kafin na ce" Mijin wa?

"Mijin Sadiya mana."

Ina dariya na ce" Ai ni na bar ma su  Rabi'atu kai."
"Wallahi ba ki isa ba"
Ya faÉ—a kai tsaye har yana wani shan mur sai ya ba ni dariya.
"Ahto ban yarda ban kuma lumta ba. In ke za ki iya haƙuri da ni, ni ba zan iya haƙuri da ke ba My Sady"
Ya faɗa yana ƙara rumgumomi wannan karan ban kwabe niyarsa ba nima sai na rumgumeshi ƙamƙameni ya yi yana shinshinan ƙamshina.

"I miss you"

"Na yi kewar dumin jikin ki.'

Ya sake faɗa yana shafa bayana zuwa ƙuguna.

"Na yi kewar ban ruwa a nan."

Hannun shi na ture ina faÉ—in" Wani kewa? Kai da ka samu sabon lambu ba irin nawa tsohon da ya ji tsatsa ba."
Kallona ya yi cikin ido kafin ya ce" Haka nan na ke son shi, ai tun yana sabon shi ni na riƙa gurzan shi har ya yi tsatsan kin ga ko dole na so shi a haka"
Na buÉ—e baki zan yi magana ya matse ni ya haÉ—e bakin mu sai da ya tsotse jan bakina tas sannan ya sake ni ni da shi gabaÉ—ayanmu muna sauke numfashi.

"I miss everthing about you Sadiya ta. Har da wannan jan bakin."

Ya faɗa yana shafa bakin sa, baki na tura masa ina ƙunkƙuni

"In kika sake tura mini baki wallahi zan turmushe ki sai na yi ɓarnan ruwa."
Chapter 81 · 0% Book details