Sashe 7
Turken Gida Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abin da ya ce kenan a saƙon na shi ƙaramin tsaki na ja na danna delete saƙon ya goge daga wayata. Data na kunna ina ganin saƙonni nata shigo mini ma su tambaya hijabai ne daga yan makarantar mu ta BUK daman suna siya tun da duk na yi musu tallah. Na amsa na yi ta ba su da cewa cikin satin nan za a kawo tun da ina Kaduna ma mun yi mgana da mai ɗinkin Hijaban lissafi kawai za mu yi na tura masa kuɗin shi, sannan na fara tunanin yadda zan in ganta kasuwancina shi ya sa a I.G na yi ta following ɗin masu ƙananun kasuwanci domin na ga yadda suke marketing ɗin kayan su sai na fahimci ina bukatar suna da ledan da zan rika saka ma kowa hijabin shi in ya siya shima duk inganta kasuwanci ne, sannan ina bukatar ɗinka hijaban in diffirent styles ma'ana kowani yanayin ɗinki ya kasance ana samu bambamci sosai da ganin abu unique a hijaban da na ke siyarwa sannan akwai bukatar na ƙara da wani abu. Ni kaɗai na zauna ina ta tunanin da me zan kara? Na fi son abin da ni kaɗai na ke siyarwa ba ko ba ma ni kaɗai ba to ya kasance bai yi yawa ba. Lamarin ya kai har littafi da biro na ɗauko na fara rubutu har takalma na saka da atamfofi amma sai na ji hankalina bai kwanta da su ba sai kawai na saka under wears irin su pant, bra, sikat gajerun wanduna da dogaye tare da sleeping drees sai na ji na fi karkata anan sai na fara tunanin sunan da zan saka a jikin logon kasuwancina daga jarshe da na ga na matsa ma kaina da yawa sai na ijiye zuwa da safe amma waya na hannuna ina ta shige-shige ina ganin sunayen da mata ke sanya ma kasuwancin su very interesting.
Ina cikin shige- shige na sai ga kiran Surayya Dee Bojuwa herbel, da na ga kiran ta sai da na ji kunya na daɗe ban nema ta ba daman ina shirin neman ta ne muka samu matsala da Yallaɓai. Ta ce kwana biyu ba ta ji motsina ba shi ya sa ta kira ta ji ko lafiya
Ina dariya na ce" Lafiya ƙalau wallahi kwanaki can ne na kwanta asibiti da yake na samu ɓari."
"Subhanallahi Sannu. Allah ya kawo wani mai albarka."
Na amsa mata da Amin sai ta fara min mganar tun da na yi ɓari ai ya kamata na yi gyara sai na ce mata zan yi in sha Allahu amma ba ni da kuɗi a hannu in na samu zan yi mata mgana.
"Haba Matar injiniya. Ni dake ai ba haka tsakanin mu kawai ki yi lissafin abin da kike so mai delivery da safe sai ya kawo miki"
Sai na kasa ce mata komai tabbas mun saba ko ba ni da kuɗi a hannu ta na ba ni kaya in na samu sai na tura mata. In na ce zan yi mata wani bayani ba za ta taɓa ganewa ba sai kawai na ce zan tura mata whatsApp abubuwan da nake so da haka muka yi sallama.
Sai na yi zuru ina tunani to gyaran me zan yi? Na gyara ma wanda ya gaji da ni! Ko na ce na fara tsufa na rage daɗi shi ya sa yanzu Yallaɓai ya daina marmarina. Na so na sha kayan lambu ne su kankana da rake da za su ɗan ta da min ni'ima saboda amfanin kaina ba domin shi ba, amma ban yi niyyar siyan wani mgani na sha ba shi ya sa ma na share Surayya kawai ban tura mata ba, na dai kira Aisha lame na ce ta aiko min da lotion sai shower gel saboda na wajena saura kaɗan ya ƙare mun rabu da ita kan cewa da safe zan san ya mata kuɗin.
Hankalina ya yi kan wayata shi ya sa ko shigowar motar Yallaɓai ban ji ba sannan ban ji maganar yaran ba, ina kwance ruf da ciki a saman gado ya shigo ɗakin ba domin ban san shigowarsa gidan da ba da a ce na sani da ba zan taɓa ɗaga idanuwana na kalle shi ba amma tun da cikin rashin sani ne ina ɗagowa muka haɗa ido huɗu da shi, da sauri na mai da kaina kan wayata. Saboda sai da na gan shi sai na ji wani irin ƙunci na mamaye min zuciya. Na so na daure ma zuciyata ko sannu da zuwa na yi masa amma na kasa shi ya sa na yi kamar ban san da shigowarsa ɗakin ba shima ina ga ya na jiran ne na fara yi masa mgana shi ya sa har ya ijiye ƙaramar jakar hannunsa saman side drower ɗin gadon tare da agogon fatan da ya cire daga hannun shi ya fita bai ce min sannu ba nima ban ce masa ba ina kwance in da nake ya dawo ya tuɓe kayan jikinsa daga shi sai gajerun wando ya koma tiolet duk ina kallon shi ta wutsiyar ido sannan na raka shi da hararan da bai san ina yi ba har kuma ya yi wankan shi ya fto ban ta shi ba, ya shafa mai sannan ya saka saukaƙkun kayan zaman gida ya fita can wajen su Jidda. Ni kuma na daɗe kan wayata sai wajen goma da rabi na kashe data nima na miƙe na faɗa tiolet na kama ruwa, sannan na zo na saka kayan barci na shafa ma wuyana da hannuna humra sannan na kwanta har ina kashe wutar bedroom ɗin kuma cikin ikon Allah barci ya ɗauke ni ban ta shi ba sai huɗu da rabi na asuba, na je na kama ruwa na yo alwala na zo na shimfiɗa sallaya na ta da salla, ina kan darduman Yallaɓai ya tashi lokacin an fara kiran sallar farko ni kuma na gama nafilfiluna ina ta jan casbaha ko kallo bai isheni ba kamar yadda shima bai nuna ma ya san ina gidan ba.
Ina idar da sallar asuba na tafi ɗakin su Jidda muka yi azkar da karatu bayan mun gama muka shiga kitchen ni da Jidda muka yi abin karyawa. Kuni na ji ina son sha tun jiya daman na jika geron sai na wanke na niƙa shi a blander Jidda kuma wanke wake shima na niƙa shi a blander, ni na dama kunin da tsamiya Jidda kuma ta fara tuyan ƙosan daga baya na karɓa na ce ta je ta shirya kar ta makara. Ni da ƴaƴana muka karya lokaci na yi Salisu ya zo ɗaukan su suka wuce ni ko daman na ci na ƙoshi sai na kishigiɗa a kan kujeran falon su Jidda tibin a kunne sai na ɗauki remot na sauya tasha zuwa arewa24 suna maimacin shirin daɗin kowa. Ina nan zaune ina kallo sai na ji motsin fitowar Yallaɓai ta wutsiyar ido na kalle shi, ya fito daga shi sai dogon wando da farar singlet Yallaɓai har wani kiba ya narka to in ba idona ƙarya ya yi min ba har da timbi ya fara ijiyewa ya samu duniya. Yau ɗin ma na so na daure na gaishe shi amma sai na ka sa ma na ƙara sautin talabijin ɗin a zuwan ko ya yi mini magana ma ba zan ji sa ba.
Ina zaune nan ya zo ya wuce ni zuwa kitchen ai ban gama mamaki ba sai ga shi ya fito da Mug cike da kunu sai filet shaƙe da ƙosai, daman ni ban shirya masa na sa a saman dining ba, a kitchen na bar komai shi ne ya shiga ya gani ya nema ma kansa mafita. Baki na saki ina kallon shi ya zo ya zauna saman kujeran dake fuskanta ta, har ya na haɗe kafafunwabaa ya kuma jawo center table ɗin da ke tsakiyar falon zuwa gaban shi ya ijiye mug ɗin kunun da filet ɗin da ya shaƙo kosan a ciki.
Remot na gefe na ya ta so ya zo ya ɗauka, ya sauya ta sha zuwa MbcAction. Ina ga ya so na yi magana ne sai kuma ya ga na mike tsam na wuce ciki na bar sa anan. Ban san yadda ya ƙare ba ina shiga ciki na kwanta sai barci tashi kawai na yi na ga bashi a gidan ya fita a raina na ce ɗan renin wayau ranar da yamma Salisu ya kawo min cefane shi na ba ma kuɗi ya je ya siyo mini kayan marmari na yi fruit salat na sha sannan na faɗa masa da safe direba zai kira shi za a kawo min hijabai daga Zariya zai karɓo daman tun da Musbahu ya yi aure sai na koma Salisu ke karɓan kayan a tasha.
Haka muka yi ta zaman doya da manja tsakanina da Yallaɓai in ya na gidana. In kuma ya na gidan Gimbiya ya kan zo duba mu da daddare. Har kuma ya gama zaman shi ya tafi ko ma ya ganni ba ma mgana. Ya san halina sarai na iya gaba shi kuma ina ga jirana yake na je na bashi haƙuri tun da ni na yi masa ba dai-dai ba ni kuma a raina na ce wallahi ya yi kaɗan ina yin abinci na ijiye masa na shi saman dining kuma ba kunya yake zama ya narka ma cikin sa. Na san har Jidda ta fahimci tsakanina da Abban na su ba zaman lafiya domin tun tasowarta ba haka ta ga muna gudanar da rayuwar mu ba, shi ya sa ta tsiri in ya shigo gidan ta biyo ni ɗaki ta na faɗa mini ga Abba ni kuma sai na ce ta je ga ni nan zuwa kuma haka zan yi ƙeme ƙeme na ƙi fita sai dai su in yana son wani abu ya ce su yi masa tun yarinyar bata fahimta ba har na fara fahimtar ba jituwa a tsakaninmu yanzu. Ranar da yana gidan Gimbiya ya zo mana sallama da daddare ina ɗaki ina rubuta waɗanda suka karɓi hijabai ba su ba ni kuɗi ta shigo tana faɗa mini ga Abba ya zo ya na falo.